page 3

361 32 0
                                    

*Rayuwar Bahijja.*

*03*
Gwagwgo Bintu bata kulataba taja su Bahijja suka shige d'aki wanda duk jikinsu yayi sanyi. Zuwa can Hindu tashigo dakin gwagwgo Bintu ta duk'a agefen k'ofa ta sunkuyar da kai tasoma magana cikin muryan kuka "Dan Allah gwagwgo kitai makeni Malam ya yafemin kada ya koreni a gidansu domin bansan inda zani ba, nasan inkinsa baki zai huce."

A hankali Gwg. Bintu tasoma magana "Hindu baki kyautama rayuwarki ba, wallahi kin b'ata wayon ki kuma kinzubarwa da gidanku k'ima a idon al'umma musanman mahaifinki da ta ke limamin gari."

"Gwagwgo wallahi nasan ban yiwa rayuwata adalci ba amma ina rok'onki da ki taimakeni ki mance rashin kunya dana rik'a yimiki abaya wallahi duk gwagwgo ke sani amma yanzu natuba na daina."

"To madallah Allah yashige mana gaba, kuma insha Allahu Malam zai d'au abin asannu bazai koreki ba."

"To nagode gwagwgo Allah ya k'ara girma."

"Amin, bakomi tafi kije ki kwanta amma ki tabbatar kinyi sallah kin rok'i gafarar ubangiji."

"To." Ta amsa tare da mik'ewa ta fice jiri na d'ibanta. Arba tayi da Malam da k'anninsa aguje ta dawo d'akin gwagwgo Bintu, arazane ta tareta tana tambayarta "Ke da waye kuma?."

Bata samu damar bata amsa ba Malam ya shigo ya fizgota yayi waje da ita gwagwgo Bintu ta biyoshi tana ce wa "Haba Malam kabita asannu mana, inrai yab'aci hankali ke nemosa, don Allah kada ka doketa domin aikin gama ya gama sai nemo mafita ya rage."

Bai kulataba ya isa inda k'anninsa suke tsaye yatura musu ita ya ce "Ku casamin ita har sai tafad'a muku gaskiyar wanda yayi mata ciki."

"Ciki! fa ka ce Malam?" Suka tambayeshi atare,  bai amsa musuba ya shige d'akinsa a fusace.

Baba Faruqu sarkin zuciya tuni yasa k'afa ya yi ball da ita ya zare belt yasoma zuba mata ta ko ina yana cewa "Yau saidai uwarki ta haifi wata mara tarbiyan amma kedai yau sunarki marigayiya."

Ihu takeyi tana fad'in "Natuba baba zan fad'a wallahi Dogari Ilya ne kuma gwagwgo ta sani dan ita ta ce in nemo mata kud'i ko ta halin k'ak'a zata sayi saniya ta turke da sallar layya ta siyar in aurena ya tashi tayimin kayan d'aki wanda yafi na kowa a garin nan." Ta k'arashe magana cikin nufar-fashin wuya.

A fusace gwagwgo Lanti tafito tayo kan Hindu tana cewa "Sharri akiyimin komi?" Dai-dai lokacin da Baba Faruqu ya daga belt zai zubawa Hindu yana ganin isowar Gwg. Lanti aikam ya dage ya lafta mata a mazaunai ta sa ki k'ara tayi baya tana sosawa, ya kuma zabgawa hannayen ai sai ta kwasa da gudu ta koma d'akinta tana antayo masa zagi.

Dakyat Gwg. Bintu tayi nasaran tsaida Baba Faruqu ya bar dukan Hindu ganin zai yi kisan kai. Ita ta taimaka mata ta kaita d'aki ta rok'i Gwg. Lanti da kada ta k'ara bugunta sabida bashi ne mafita ba. Cikin ruwa bala'i ta amsa "To kanwa uwar gami, 'yar bak'in ciki, munafuka burinki yacika sai ki maza ki tafi ki k'arawa bokanki kud'i tunda aiki yayi kyau 'yata tabi maza hankalinki ya kwanta."

Ita dai Gwg. Bintu shiru ta yi tana kallon ta zuwacan ta juya zatafice taji Gwg. Lanti ta kuma cewa "Kuma ban yafemiki ba, Allah ya sakamin akan 'yarki Nana, insha Allahu ita har k'anjamau zata d'auko domin kuwa burina tazama magajiyar karuwai."

Cikin sanyinta Gwg. Bintu tadawo daf da Gwg. Lanti cikin matsanancin bacin rai tasoma magana "Ba Amin ba Lanti, bak'in baki yayi ta komawa kanki da yardan Allah kamar yadda yanzu ya koma miki gashinan 'yarki d'auke da abin kunya duk don sakamakon mugun alkaba'iran da kike jifar marainiyar Allah Bahijja, kin takurawa rayuwarta kin hanata sak'at da mugun baki, kullum burinki mugun abu yasameta, alhalin tana cikin gatanta kika rabota dashi, to ta Allah ba nakiba Lanti, bak'in bakinki yasami bishiyar tsamiya kuma aniyarki tayi tabinki har yauma tanadi. Azzaluma kawai mai mugun nufi wacce bata san komi ba sai mugunta." Ta fice tabar Gwg. Lanti da baki bud'e cike da mamaki wai yau Gwg. Bintu ce ke fad'a mata magana haka bako jin shakka. 'Uhm lallai gobe sammakon zuwa gidan 'yar mod'o ya kamani in zana mata abinda ke faruwa domin samo mafita.' (Zuciyar asara kenan mai cike da tsa-tsa sam babu Allah cikinsa sai shagalar rayuwa. Allah ya kiyashemu da irin ta. Amin)

Washe gari malam na dawowa masallaci yatara kowa na gidan a dakinsa. Bayan an gama taruwa yayi sallama tare dayin gyaran murya sannan yasoma da cewa "Duk kanmu munsami labarin iftik'in da ya sami rayuwarmu na samuwar cikin a jikin Hindatu ta gurbatacciyan hanya, to abisa da haka ni Malam Yusufa na soke talla agidana akan kowani yaro ba mace ba hatta da maza kuma in nasami wani ya yi watsi da umurnina to za agamu da bacin raina wanda ba'a tab'a ganinsa ba, da fatan anjini."

"Eh Malam." Matan su amsa cikin had'a baki.

Jinjina kai ya yi tare da cigaba "Hindatu kuma zata haife cikin jikinta in Allah yaso sannan bazamu tuhumi Dogari Ilya akan maganar ba sabida ba fyad'e yayi mataba da kanta taje don haka inta haihu sai abashi d'ansa ko 'yarsa inyana so in kuma yak'i amsa zamu raine ta dan tamemana k'addararmu."

Kowa ya yi shiru yana jimani sai sautin kukan Hindu kad'ai ke fita mai tsuma zuciya.

Ta rarrafa gaban malam ta ce "Kayimin rai Malam, ka yafemin natuba kuma ka taimakeni acire cikin dan Allah wallhi bana sonsa bazan haifi shege ba, nikam ban yafema gwagwgo ba ita da Ilya."

A fusace Gwg. Lanti ta fallmata mari bata maida nunfashiba Malam ya sauke yatsunsa biyar afusknta bai tsaya ba sai da ya yi mata maruka hud'u masu kyau sannan ya ce "Lanti ina daf da tsige igiyata akanki in har baki shiga hankalinki ba, ko jaka ce ita da kike ta duka alhalin ke ba wanda ya dukeki dik kuwa da tsiyar da kike kan shukawa."

Cikin zubar hawaye tafi ce d'akin tallabe da kumatu, dan bata shirya asarar igiyoyin aurenta ba.

Malam ya dubi Hindu "Ba za'azub da shi ba sai kin haifeshi, shi ne hukuncin dazan miki kuma hakan ya dace da ke dama masu hali irin na ki."

Ta fashe da kuka tana fadin "Na bani na lalace, sunana yagama zaga gari, za'a sanyoni cikin gad'an dandali."

Tsawa Malam da da ka mata tafice da gudu, daga haka taron ya watse kowa da abinda ke fad'a musanman dokan hana talla da Malam ya kafa.

*
K'auyen kwara-kwara, k'auye ne mai tarihi sosai. A nan garin Malam Yusufa ke zaune da iyalansa kuma shine limamim garin kamar yarda ya gada wurin mahaifinsa.

Yana da mata biyu Lanti da Bintu. Baya da 'ya'ya da yawa su hud'une duka-duka Lanti uwar gida keda uku Bantu nada daya itace Nana. Ado, Hindu da musa su ne yaran Lanti.

Bahijja kuwa 'd'iyar yayan Lanti ce na miji. Tunda babanta yarasu ta taho da ita tana 'yar shekara bakwai yanzu takai shekaru biyar ahannunta kuma tak'i kaita ganin mamanta ko sau daya sannna sukuma tayi musu surkulle sunkasa zuwa ganinta sam. Dama su biyu iyayensu suka haifa, daga ita sai mahaifin Bahijja, shi yasa ta sami damar yin ikon da ta so.

Lanti jaraba lak'abinta  kenan a k'auyen. Kowa yasanta da masifa amma sosai take shakkan mijinta Malam domin tasan bai d'aukan iskancinta amam dik da haka wata rana yab'a masa magana ta ke yi dan masifa yariga da yazamo jinin jikinta.

*mrs j moon*

RAYUWAR BAHIJJA.Opowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz