*RAYUWATACE*💚
*WATTPAD@PRETTYSALMA17*
*darling_princess*
*45-46*
*gaisuwa mai tarin yawa agareki my one n only..ROUKAYYA SUFYAN*😍😍
Sako nafarko dr sambo ne ga abinda yace kamar haka.
*_slm my baby inafatan kina cikin koshin lafiya,inata kiran wayarki amma kashe,hope all is well_*
Tsoki taja kawai tayi delete,sauranma duk taduba taga namatane duk tayi delete.
Haka tahau online tashiga nanma taga msgs dayawa duk tabi tagoge,baki daya tayi delete din account dinta na whatsapp zata canza number amma sai tasiya sabon sim,duk wannan abinda takeyi billy nakallonta itade tanata chat dinta.
Da yamma tashirya tsaff taci kwalliya tasaka dogon hijab har kasa tana zaman jiran sadiq,aiko karfe biyar dede ya iso kofar gidan,waya yamata tabashi izinin yashigo ciki,dama tariga datagyara gidan tasaka turaran kamshi,duk billy najinta.
Sallama akayi deena ta 'amsa tanasakin dariya tace"shigo yallabai"
Tsayawa yayi daga bakim kofa yace"anya nashigo kuwa,kinsanfa babu kyau mace da namiji sukebe idan bamuharraman junaba"
"Uhm nasani,ai banikade bace agidan,sister na nanan"
"Ohoo,to bari nashigo"shigowa yayi har cikin dakin yana sallama,dago kan da billy zatayi karafff sai cikin idon sadiq,nan take tatashi azabure tamike tare dacewa"uncle sadiq"
Shima kallonta sadiq din yayi yanafadin"ah billy ashe madeena itace yayarki"
Ai tsabar mamaki bata iya bada amsaba saide kawai gyada kai tayi takoma tazauna,duk abinda suke kan idanuwan billy,hatta firarsu duk akunnanta,jir kawai takeyi yatafi ayita takare.
"Madam yakamatafa kibani izini naje kano domin neman izinin auranki"
"Uhm sadiq kenan,tun yanzu,kabari mukara sabawa mana"
"Rufam asiri,aida zafi zafi akan daki karfe,intsaya kawai wani yamun tsakiyar da babu ruwa,garade inje asan dani,dan banason aja dogon lokaci,sonake dazywana dasa biki duka kada yawuce wata ukkufa"
Dan rufe fuskarta deena tayi alamar kunya tace"yadda kace haka za'ayi ranka shidade"
"Yawwa my baby,yanzu sai kibani number baba ko,ko itama num rowa zakimin?"
"Hahaha,waceni,kawo wayar nasama"
Mikatama wayar yayi tasakame number mahaifinta tabasa abinsa,atare sukaci abinda yasiyomata kamar yadda yamata alkawari sunaci suna fira har sukaji cikinsu yacika,karfe shidda dede sadiq yamike"tohh bari natafi magrib tafara sanyo kai"
Mikewa iatama deena tayi"tom yanzu sai yaushe kenan?"
" aini ko anjima kikace nazo banda damuwa"
"Hahah,balle kuma bazanceba"
"Ai nasani,kada kidamu dududu kwana nawa tarage nasakaki aciki nata kallonki kuma baki isa kice nadenaba ba"
"Uhmm kaiba,nide muje narakaka"har bakin mota tarakasa yafiddo kudi yabata amma taki amsa,saida yayi juyin duniyarnan amma taki amsa,haka yasa kai yatafi itakuma tadawo ciki.
Aiko cire hijab dinta batayiba taga billy tsaye kanta tana rike da kugu tanawani girgize2 tana cika tana batsewa,kallonta deena tqyi tace"ah lafiyade billy naganki akaina kamar zaki dakeni"
"Aini deena bansan cewa ke mayaudariya bace sai yau,ashe dama inajin labarin yanmata na amshema matan aure mazajensu bankara yaddaba sai yau"
Kallonta deena tayi duba irin nabangane inakika dosaba"kinga billy,kifitomin amutum kifahimtar dani miyene kike nufi wai"
"Ehh aidama dole kice bakigane miyenake nufiba,to bari kiji,kinga wannan sadiq din dakike ikirarin zaki aura,garama tun wuri kifidda hakan aranki,dan abine dabazaitaba yiwuwaba"
"Kozaki fadamin dalilin dayasa kikace bazai taba yiwuwaba"?
"Sabida mijin anty zubyne"
"Hahahahaahah"wata irin dariya deea tasheke da ita"to saimi? Dan yana mijin anty zuby,aini bantunanin abinda zaki fadaba kenan,to bari kiji billy,wallahi allah idan kinga ban auri sadiq ba to nufine na Allah amma bade mutum ba"
"Haka zakice,to narantse da Allah kibar ganin kina yar uwata,zan ajiye sanayya gefe guda,zan nunama bansankiba,don akan zuby zan iyayin komi dan ganin farin cikinta,ke baki isa kiyi kishi da abinda nakesoba wallahi karyarki tasha karya"
"Billy,nikike fadama wannan maganar"?
"Nafada kiyi abinda zaki iya"
"Hmmm babu abinda zanmaki amma aure yananan daram dam,babu mahalukin daya isa yahanasa"
"Aiko na isa nahanasa,shima sadiq din dan baisan kiwacece keba aida bai kawi kanshi garekiba,amma idan mafadame koke wacece kinaganin zai aureki"?billy tafada agadarance tana murmushi"
"Hummm billy kenan,ai bansan rashin wayon naki yakainan ba sai yau,to bari kiji,sadiq yasan koni wacece sadiq shine silar shiryuwata dan haka bismillah,kindade baki fadamaya komiba,tun kafin kikaiga fadamasa narihaki fadamasa koni wacece kuma yace yaji yagani yanaso ahaka don haka saiki sake wata shawarar"
"Tswwww banza maciya amana,aini nayi danasanin hada jini dake wallahi kuma kijira kiga abinda zai biyo baya"kawai tafigi hijab da wayarta tafito
Koda tafita rasa inazata tayi dan tasan idan tace zata gidan zuby yanzu mijinta nanan don gida yayi wuri tasamu tazauna takira zuby,saida takatse batadaukaba anabiyu tadaga.
"Hlo sweetheart babu lafiyaba"
"Subhanallah,miyafaru babyna"
"Kinji labarin mijinki zaikaramaki kishiya"
Zuby azaune take amma saida tamike tsabar hirgicewa"bangane miye kikefadaminba,ke a ina kikaji sadiq zaiyi aure"?
"Hmm anty zuby kinatsu dakyau,yakamata kituntubi mijinki da wannan zancen,sana banason kitada hankalinki kokadan,domin kuwa kinada dani,bazan taba bari hakan tafaru dakeba"
"Haba baby taya zakice nakwantar da hankalina,bayan kinsan babu abinda natsana sama da kishiya,kinsan inada bala'in kishi koban fadaba kinsani"
"Nasani amma kada kidamu ninasan yadda zamuyi"
"Shikenan zankiraki anjima kinji"takashe wayar.
Lambar anty billy tayi dialling,aiko anty naganin billy tasaki murmushi tadaga"hlo my ykk"
"Lafiyalo anty,dama kira nayi nafadamaki,dan nariga dana daukarmaki alkawarin cewa inde naga deena tayi badedeba to zan sanarmaki,deena de aure zatayi,shiyasa nace bari nasanarmaki dan kisan tayadda zakifara"
Ajiyar zuciya anty tayi tace"billy nasani,kuma nafadamata cewa tafidda maganar aure aranta,don abine dazan taba bari tayisaba,inata kiranta wayarta akashe,amma tunda takiji bataki ganiba,inanan zuwa katsina cikin week dinan,sana inaso kisamin ido akanta"
"Shikenan anty,zanyi yadda kikace"sukayi bankwana.
Still dr sambo takira,dama tanada number sa,dr nadagawa suka gaisa.
"Sede bangane dawa nake maganaba"
"Sunana billy kanwar deena"
"Ah malama billy kece agari,injide lafiya ko"?
"Dan Allah dr akwai temakon danakeso kamun,domin duk duniyarnan kai kadene zaka iyamun wanan temakon"
Gyara zama dr yayi yace"inajinki,Allah yasa zan iya"
"Kanada labarin deena zatayi aure"?
"Nima haka takecemin"
"Yawwa,dr nasan koba kafadaba kanason deena ko?"
"Gaskiyane inasom deena amma nasan deena bazata taba amincewa daniba,don tasha fadamin dan iska baya auran dan iska sabida kar tasan karce,amma ayanzu wallahi nagane gaskiya nabita,kuma duk wani abu danakeyi nadenasa,ashirye nake dana auri deena"
"Yawwa,to kada kadamu,zantemakamaka,domin mutunin datakeso ta aura banasonsa baiyiminba,don haka zanyi iya kokarina naganin natemakama kashawo kan deena,kaima kasan yadda zakalallabata,daso samunema kazo yau dadaddare kafurtamata abinda ke ranka,koda taki yarda kada gwiwarka tayi sanyi,kasan irin kalaman dazakmata harta amince,inde zata janye batun auran wanan mutumin to tabbas zanfi kowa murna"
