*RAYUWATACE*💚
*WATTPAD@PRETTYSALMA17*
*darling_princess*
*55-56*
Jitayi duk tadamu,ahaka har akakammala nata gyaran yau sai kuma nagobe wanda shine last sukatafi gida.
Kobayan sunkoma agida tagwada kiransa yafi adirga nanma shiru wayar kashe har dare wanda tana tsammanin yanzu yaje gida,tun abin nadamunta haryakaiga itama tafara shaka takashe wayarta baki daya.
Washe gari ake ball,can wurin ango zasuyi ball banda amarya,angama ball kowa yawatse,shima ango tun yinin ranar yake gwada layinta amma shiru hardare bayan yasamu kansa yakira billy,lokacin billy nafalo anata fira da yan'uwa anashewa taga wayarta tayi kara,ganin sunan mai kiranne yasa tadan bata face dakamar bazata dagaba kuma tadaga"hlo uncle ina yini"
"Lafiyalo sister,lafiya wayar babyna kashe tunsafe nake kira amma sai acemin kashe take"
Saida tayamutsa face kamar tanaganinsa sana tace"nima bansaniba,amma itadekam tana lafiya""Pls bata waya muyi magana"
Mikewa tayi domin taje dakin tabata,azaune tatarar da ita fitowarta wanka kenan billy tamikamata waya"gashi mijinki keson magana dake yace yanata kiranki tun safe wayarki akashe"
Kallon banza deena tawatsamata"bazan karbaba,kibacemin daga gani wallahi"
Duk abinda deena kefadi yanajinta don baikasheba.
"Hlo uncle tace bazata amsaba"
"Ohk kyaleta dani billy,but kicemata wallahi idan bata bude wayartaba zanyi abinda nacemata jiya danazo"kitt yakashe wayar.
"Yace idan baki kunna wayarkiba zaiyi abinda yafadamaki jiya"tanafadan haka tasa kai tafita.
"Tsww yadade baikoro kowa gidaba,kuma wayace bazan kunnaba,nizaigwadama zuciya"tacigaba da shafa manta,koda tagama tabi jikinta da turaruka masu kamshin gaske sana taja blanket tarufa jikinta takwanta.
Anata harkar hidimar biki,gida yadauki harama hargashi gobe daurin aure,amma haryanzu deena taki bude wayar tata,yaune za'ayi bridal shower,amarya tahadu iya haduwa,doguwar riga red tasaka sai akasamata crown fari mai adon stones jajaye sai sheki sukeyi,beejay tayimata makeup,sukuma kawayen amarya sukasaka dogayen riguna bakake da head red bakaramin kyau sukayiba,sunwanku iya wankuwa,acikin gidan akayishi,photographer biyu sukadakko,sunsha hoto daga bisani karfe 7:00pm akatashi.Misalin karfe takwas nadare deena taji mararta namurdawa,batakawo komi arantaba,saida taji ciwon nadan damunta kuma taji kamar kasanta nadanshi,dan ita azatonta ruwan ni'imane kawai take ambaliyarwa,mikewa tayi tashiga toilet domin tayi checking up,tanacire panta dinta taga yabaci da jini,wani uban takaicine yarufeta,rasama mizatayi tayi,gashi babu pad acikin toilet din,lekowa tayi tayima billy signal alamar tazo,tasowa billy tayi tatsaya bakin kofar tace"minene kuma?"
"Pls kisamamin pad,wallahi period dinane yazo"
Wata dariya billy takece da ita sana tace"kashhhh gaskiya wannan jinin baima uncle adalciba dayazo yau,inalaifin yabari sai ankaiki yaciki sana yazo,anyway,nidama inataya my love kishi garama dayazo wallahi,bari nasamomaki adakin mama"tatafi cikin hanzari.
Harara deena tabita da ita,tananan tsaye saiga billy tadauko pad ko sakayawa babu tamikomata tasa hannu takarba tameda kofar bayin tarufe.
Wanka tayi sana tasaka pad din tafito jiki asukwane tahaye gado takwanta,kallonta anty maryam tayi tace"naga kamar pad billy tabaki,kadakicemin period kike"
"Uhum"kawai deena tace.
"Lalle angonki nacikin gararin rayuwa,saukinma bakekadece matarsaba ai da anshiga ukku wallahi,kinsan suma maza yanzu idan zasuyi aure sundinga banke², allah yakyauta kam".
Itade deena tanajinta amma tayi banza da ita ta kyale,don itakanta abin yafara damunta,dahaka tayi bacci.
Washe gari ranar daurin aure,karfe shadaya anguna suka iso,daurin auran na karfe biyune,da andaura za'a wuce da amarya,itade amarya nacan kwance ba'ita tatashiba sai karfe shabiyu,shima dan anmatsamata,billy ko itada wasu kawayen nasu sunbi yankai kayan amarya sunyi gaba.
Tashi tayi saida tafarasahn tea sana tashiga toilet tayi wanka,tadauki lokaci cikin kewayen kafin daga bisani tafito,mai makeup hartazo itakawai akejira,nan akafara tsantsaramata makeup nagani nafada,dukda bawani uban makeup bane light makeup ne,atamfa akabata tasaka akadauramata dankwali,aiko nan amarya takarasa fitowa matsayin amarya,sai wani sheki takeyi.
Karfe biyu dede akadaura auran madeena da abubakar sadiq bisa sadaki naira dubu hamsin,bayan daurin aure yan daukar amarya sukazo,nan akadauki anmarya akakaita dakin abbanta yadingamata nasiha mai karya jiki,hakama mamanta sukasata agaba sunatamata nasiha,babu abinda deena keyi sai kuka,sukansu iyayen nata saida suka zubar da hawaye,kafin akafito da marya domin sadata da gidanta.
Mutanan dasukabi kai amarya balaifi akwai yawa,don wasu basuyi niyar zuwaba,amma dinner din da'akace za'ayi itatasa sukabi.Karfe ukku sukadauki hanya basu suka isaba sai shidda da rabi,shima dan sunsa r.
Masha'Allahu gidan amarya kowa nayabonsa,don suntashi daga gidan dayake yakoma gidan dayagina mai part ukku,daya na zuby daya nata daya nashi,duk wanda yaga gidannan yasan bakaramar naira kazubaba wurin gininsa,to shima mahaifin deena yayi rawar gani,don naira takoka apart din deena,gado kirar dubai kala biyu sai dan lajeriya guda sune skayi making ukku,kujerunta set biyu duk nawaje falonta biyu.Su billy anriga da an'iso tuntuni,can bangaran amarya tabaro kawayen nasu itakuma tashiga bangaren uwar gida zuby,zuby nazaune cikin yan'uwanta da kawayenta anata hira taga billy tashigo,tashi tayi tatareta da murmushi tace"baby yadahaka"?
"Wat"?
"Zuwa babu sanarwa""Hahaha,suprise"
"Lallekam surprise,dama inata Allah Allah kizo dawuri"
"To gani nazo miza'ayi"
"Mushiga daga cikide muyi magana"
Hannunta takama sukashiga daya daga cikin bedroom dinta tazaunar da ita bakin gado itama tazauna.
"Ni wallahi sweetheart bakisan haushi kikebaniba,ace wai mijinka zai kara aure amma kwata² kiki nuna damuwarki,haba dan Allah"
Kamo hannunta zuby tayi tace"haba daughter,sanin kankine inada masifar kishi,amma mi,dake da deena daya nadaukeku,jinake tamkar kece sadiq zai aura,to kinga kuwa baikamata nanuna komiba,wallahi babu komi ni awurina,kema haka banason kisaka komi aranki my baby"
"Uhum hqkade kikace amma nikam inakishi idanke bakyayi,miye kikace zakifadamin""My baby rigima,anyway,ga kayanan na'amso daga wurin tailer,dan wulakanci sai jiya yakarasa dinkasu shima saida nayime bala'i sana yacemin zai kawomin,laces ne kala daya nidake,don banason ko amarya tafimu kyau awurin dinner"
Dauko kayan zuby tayi tabazasu gaban billy,dagawa billy tayi tanagani sai kiran"woow,woow" takeyi alamar dinkin ya jugunu,ga kalar lace din cream,dinkin bakaramin kyau yayiba,haka zalika shikansa lace din bakaramin lace bane,nan billy tadingama zuby godiya.
"Shiiiii,banason godiya,nide kawai kishirya,nakiramana mai makeup anjima bayan magrib nace tazo don haka kizama ready"
"Ohk bakida case my love,nide kibarni nan nakwanta don nagaji"
"Kisha bacci lafiya"zuby tafada tatatshi tabar dakin.