21

1.3K 26 0
                                    

*RAYUWATACE*💚




*darling_princess*




*41-42*




_*AM SO SORRY MY FANZ,WALLAHI ALLAH BANYI DAN WULAKANCIBA,INA BUSY SHIYASA KUKAJINI SHIRU,MASUYIMIN MAGANA BANDUBABA KUMA KUYI HAKURI,DAN ADAM AJIZINE,BANADA WULAKANCI KUMA BANASO AYIMIN DAN ALLAH KUYIMIN UZURI NAGODEMAKU DA KAUNAR DAKUKE NUNAMIN WALLAH HAKAN NASANI SHIDADI,ONLE LOVE*😍



Kuka mai tsanani deena keyi harda majina,dakyar abubakar yalallasheta takoma ciki shikuma yaja motqrsa yanaji aransa yanason madeena sosai tare da tausayamata.

Koda deena tashiga gida lokacin dr yafito daga wanka haryagama shirinsa yazauna afalo yanashan juice yaga tashigo idanuwanta akumbure gawasu hawayen duk sunwankemata fuska.
Ajiye kofin juice din yayi yatashi zai tarbeta yahadasa da jikinsa deena tayi saurin dagamai hannu"kada katabani"
Tsayawa yayi yanakallonta cike da mamaki yace"bangane kada natabakiba deena,kinsan kuwa abinda kike fada"

"Tabbas nasani dr,hakika nayaudari kaina,naccici kaina,duniya tarubaceni,inazansaka kaina,dr dagani har kai munsan abinda mike aikatawa haramune,amma zuciya tarudemu mukaki ganin laifin abinda muke aikatawa,dr natuba nayi nadama,kuma kaima inason kadena wannan rayuwar kakomama mahallincinka,duniya duka nawa take dazata rudemu,mugane cewa annabi yayi kaura"cikin kuka tafada tadyrkuse kasa tanata gunjin kuka kamar idanunta zasu fita.
Bakidaya shima dr jikinsa yayi sanyi,hakika yasan abinda deena tafada gaskiyane,tisue yazara tareda dukawa kusa da ita yamikamata"kigoge hawayenki muyi magana"
Dago idanuwanta dasukayi jawur tayi takallesa ko magana batayimeba tatashi kawai tashiga cikin bedroom tadauki abinda tasan mallakintane tafito tanufi kofar fita,saurin tashi dr yayi yasha gabanta"dan Allah kitsaya muyi magana deena,kifahimceni mana"

"Dan Allah kibari muyi magana,kitsaya kiji mizancemaki"

Fita tayi tabarsa anan tsaye,shikansa wani irin mugun tausayi tabasa,ga zuciyarsa dakemai wani iri dukda baisan takamaime mikefaruwaba.
Tanafita saida tayi tafiya sosai sana tasamu abin hawa,nan takwatantame inda zai kaita,har kofar gida Yakaita tafiddo 1k tabasa,kallonta mai napep yayi"hajiya banda caji"

Ko kallonsa batayiba tace"dauka kawai"tawuce.

Tadda billy tayi itada wata suna cin abinci atare,banza tayi dasu tasamu katifa tafada tayi kwanciyar rigingine hawayenata zuba a idanunta.
Kallonta billy tayi tatabe baki"to kekuma mi'akami zakishigoma mutane without taken excuse"
Jitayi shiru babu amsa kara tabe baki tayi"kinsande ni banason ina magana kiyi banza kikyalenifa"
Nanma shiru,itamadin shiru tayi tacigaba dacin abincinta bayan sungama wannan kawar billy tatashi tace zatatafi,rakata billy tayi tasamu abin hawa sana tadawo.
Tunkafin tashiga dakin take jiyo sautin kukan deena,cikin hanzari tashiga dakin,tsaye tayi tadafe baki tace"wai deena mike faruwane,yau kwananki biyar baki gidannan yanxu kuma kindawo kinata kuka,kowani abu dr sambo yamaki,kokuwa likitane yatabbatarmaki da kinada ciki"

Dagowa deena tayi idanuwanta sunkara kumbura tasaka bayan hannu tana goge fuskarta,billy ganin yadda idanuwan deena suka koma yasa taji gabanta yafadi,tayi saurin fadawa kan katifar tadafa deena"subhanallahi,deena kinga yadda idanuwanki suka koma,dan Allah waye yatabaki acikin garinnan"?

Dafata itama deenar tayi tace"billy hakika yau nayi danasanin irin rayuwar danatsinci kaina aciki,wallahi bantaba danasanin zuwana duniyarnanba sai yau,miyasa rayuwa zatazomana ahaka,kiduba kigani nidake uwarmu daya ubanmu daya,amma acikinmu babu nakirki,babu maifada mawani gaskiya acikin yaji,wannan wace irin rayuwace haka"

"Tooo kekuma da wannan salon kikadawo,wainama tambayeki,waye yamaki wa'azi haka haryashigeki"

Kallon billy deena tayi tasake fashewa dawani kukan"billy kifahimceni,babu wanda yamin wa'azi,Hakika Allah nasona darahamarsa shiyasa haryabarni nagano gaskiya,billy kema inamai baki shawara daki zauna kiyi tunani kiganecewa rayuwar damuka daukarma kanmu barayuwabace,dan allah billy kema narokeki dakidena wannan rayuwar kidawo hanya madedeciya,mucigaba da abinda yakawomu"

"Hummm,gaskiyane,to agaskiya nide deena bazan boyemakiba,bazan iyayin abinda kikesoba,kekikaji zaki iya,to Allah yatemakeki,nima kada kidamu,nakusa shiryuwa amma ba yanzuba "Haba billy,nifa yar uwar.....dakata malama,rayuwarki daban tawa daban,haka kabarinki daban nawa daban,so inamaki congrat dakika shiryu,dan haka bari kiji nafadamaki wani abu guda,inaso duk abinda zanyi acikin gidannan bance kidakatar daniba kokuma kiyi yunkurin yimun wa'azi,idan kuma kika kuskura kikamin haka,duk irin rashin mutuncin danamaki ke kikaja.

Wani sabon kukan deena takara fashewa dashi,bata iyacewa komiba har billy tatashi tashirya tadauki bag dinta da wayarta takara gaba,sai binta da ido kawai deena keyi,kwanciya tayi tacigaba da rusar kukanta har magriba tasameta tatshi tayi alwala tazo adaddafe tayi sallahr sakamakon wani irin mugun ciwon kai dake damunta,harbata ganin abinda ke gabanta.
Tananan zaune taji wayarta tayi kara,rarrafawa tayi tadauki wayar,ganin sunan mai kira yasa taki dagawa,saida aka addabeta dakira sana tadaga.
"Baby inakikashige haka inata kiranki shiru bakidagaba.
Muryarta duk tadishe tace"ina sallahne"

"Subhanallahi,yanaji muryarki kamar wadda batada lafiya,mike damunki"

"Aah babu abinda kedamuna kawaide ciwon kai kedamuna"

"Ayya sorry babyna,kice zuwa katsina yakara kamani gobe"

"Aah kibarsa basai kinzoba,yanzunma danasha magani nasan zai dena"

"Kintabbata zakisha magani"

"Allah dagaske nake"

"To kisha magani,zankiraki anjima naji idan ciwon kan yadena"

"To nagode"takashe wayar,wani irin takaici da kuka suka kamata,tanaganin duk irim rayuwar datasamu kanta anty nafeesace silar komi,itace silar tarwatsewar rayuwarta,tananan tanata kuka har akayi sallahr isha'i tatashi itama tayita adaddafe ko abinci bata iyaciba taja kafa takwanta saman katifa.
Cikin bacci taji wayarta nakara,dubawa tayi taga sadiq ne kekiranta,dagawa tayi"assalamu-alaikum"

"Amin wa'alaikissalam my feature wife"

"Uhm tun yanzu"

"Ehman,mi'akejira,nifa banki ace gobe naturoba"

"Uhum kai sadiq,anyade"

"Madeena wake daya"?

"Allah"

"To wallahi tallahi billahi,kinji rantsuwar musulmi ko,idan kinga ban aurekiba to bana numfashi adoran kasa,kokuma ke kice bazaki aureniba,to shine kawai zaisa kiga ban aurekiba,kirubuta ki ajiye"

"Nayarda dakai sadiq shiyasa ban boyema komiba dangane dani,hakika babu wata yamace dabazataso kakasance uban yayantaba,zuwanka acikin rayuwata alkhairine,koda baka aureniba bazan taba mantawa dakaiba arayuwata insha'Allahu"

"Ballantana kuna bazanki aurenkiba,nide abinda nakeso dake,kamar yadda kika nuna kinyi nadama to kikara tsarkake kanki dakuma zuciyarki,kada kibari wani abu yakaracin galaba akanki,kizama mai yawaita istigfari,domin Allah shi mai yafiyane ga kowa,dan haka kikara kysanci ga Allah kinji babyna"

"Insha'Allahu sadiq namaka alkawarin bazan sake maimaita kalar rayuwar danayi abayaba,waddama nayi abyan kaddaratace,fatana kaina katayani da Addu'a Allah yayafemin zunibbaina"

RAYUWATCEWhere stories live. Discover now