*RAYUWATACE*💚
*_ALLAH SARKI DUNIYA,WANI YAKIKA WANI YASOKA,HAKIKA MASOYANA NAGODE WALLAHI SOSAI ANA MUGUN TARE ME N UHHH OLL,WATAKAM WANNAN BOOK DIN DANA KUDINE BAKARAMIN KUDI ZANSAMU DASHIBA,AMMA NAYIMAKUSHI KYAUTA SAKAMAKON NUNAMIN KAUNA DAKUKEYI WANNAN SHINE TUKUCINKU,LOVE UHH OLL,GAMSU NEMAN NUMBER TA ZAKU IYA DUBA SONE PAGES DANAYI AKWAI NUMBERTA AKAI_*
*WATTPAD@PRETTYSALMA17*
*darling_princess*
*47-48*
"Shikenan billy insha'Allahu zangwada kamar yadda kikace nagode sosai da kulawarki agareni kinji"
"Bakomi dr anatare"takashe wayar.
Tashi tayi takoma gidan ko inda deena take bata kallaba tacigaba da harkar gabanta.
Washe gari sunada lecture,haka suka shirya idi yazo yadaujesu yayi droping nasu askul,basu suka fito lecture ba sai karfe ukku,duk sunata shirye²n fara text sabida last semester suke kuma daga ita sun gama.
Takowa deena tayi harzuwa bakin gate zatafito taji wayarta tayi kara,dubawa tayi tada mai kiran nata kawai tashare har wayar takaraci ringinta bata dagaba,tasan cewa kafin idi yazo sai yabatamasu lokaci haka tashiga skul bus akayi droping nata a national daganan tatari napep yakawota har kofar gida tacakemasa kudinsa cass tasa key tabude gida tashiga.
Wanka tashiga tayi tazo tanajiran ayi sallahr la'asr tayi sana tasamu abinda zatasakama cikinta.
Yar karamar wayar datake rikewa bata fita da itace tasoma kara,koda ba'afadamataba tasan mai kiran,sabida babanta kawai keda layin,da hanzari tadauki kiran"hlo abba inayini""Lafiyalo madeena yakuke ya makaranta"
"Abba lafiyalo,munata shire²n fara text daga mungama kuma mufara exam,abba atayamu da addua"
"Insha'Allahu munamaku addu'a sede mukara,ina bilkisu?"
Gabanta taji yabada damm tadan daburce tace"abba tana bacci,bamudade dadawowaba daga skul kanta ke ciwo"
"To idan tatashi kice inagaidata da jiki insha'Allahu ranar Wednesday zanshigo katsina ai"
"Allah yakaimu lafiya abba,agaida mama"
"To zataji insha'Allahu"nan sukangama gaisawa sana yakashe wayar dede ana kiran la'asr tatashi takabbara,tana idarwa tashiga kitchen tadaura jelof din taliya da busashen kifi,tana saukewa tazoba iya wadda zataci a plate sauran tajuye akula tafito tazauna adaki tafaracin abincinta cikin kwanciyar hankali,tanatsaka dacin abincin taji sallamar idi yashigo.
Kallonsa tayi tace"hala kaje skul din?"Saida yasamu wuri yazauna sana yabata amsa dacewa"naje,dan wulakanci aida saiku kirani kuce basai nazoba shine zakusa nay tattaki naje natarar babuke babu gantalalliya"
"Uhum idi kakiyayi cema billy gantalalliya,Allah duk sadda tajika bazaku kwashe da kayubafa"
"Tsww share kawai,aike kanki kinsan basharri namataba,wallahi idan batabini ahankaliba zataganefa"
"Nide naji bawannanba idi dama akwai magabar danakeso muyi kasan tsakanina dakai babu wani boye²"
"Hakane,shiyasa nina jinina yazo daya danaki fadamin miyene matsalarki insha'Allahu zanmaki maganinta inde inada ikonyin hakan"
Kwashe komi tayi tafadama idi,hatta maganar sadiq bataboyemasaba dayadda sukayi da billy duka duk bataboyemasaba hartakai aya.
Ajiyar zuciya idi yasaki sana yace"Alhamdulillahi,hakika madeena natayaki murna dakika gane gaskia harkika bita,sana maganar billy kuma kifita harkarta,duk danasan cewa ni ban'isa narabaki da itaba,amma kisani yau da dan uwanka za'ahada baki acuceka,dan haka kiyi taka tsantsan da ita,don kamar yadda tafadamaku zata'iyayin komi,dole kidage da Addu',sana maganar shi wanda kikace zai aureki,kibasa dama yaje yaga alhaji,ninatabbata bazai hanaki aure yanzuba,tunda gashi kina kan gangara akan karatunki,wannan damace Allah yabaki,don haka kiyi amfani da ita tunkafin tasubucemaki,iyakar abinda zancemaki kenan madeena"