*RAYUWATACE*💚
*WATTPAD@PRETTYSALMA17*
*darling_pricess*
*49-50*
Fadawa tayi kan katifa tacigaba da rusar kukanta kamar ba gobe,tanaji wayarta na ringing amma taki dagawa dukda batasan kowayeba.
Zuby ganin tayi ruwan bala'i da masifa amma duk basu kaitaba yasa takira billy,bugu daya billy tadaga tace"darling"
"Baby kina ina"?
"Naje kasuwa amma yanzu haka ina kan hanyata tadawowa lafiya"
"Inace kinsan yarinyar da sadiq zai aura ko?"
"Saida billy taji gabanta yafadi amma tadake tace"eh nasanta"
"Ohk kibiyo tagidana yanzu muje kirakani"
"Ohk badamuwa bari nazo"takashe wayar.
Direct billy gidan zuby tawuce,alredy tashirya itakawai take jira tahau motarta sukatafi,ganin hanyar dasuke bine yasa zuby cewa"bae yanaga kina nunamin hanyar anguwar dakuke zaune,kada kicemin yarinyar anguwar take""Eh anguwar take"
Daga haka billy batakara cewa komi harsuka iso kofar gidan taji billy tace tatsaya anan tayi parking.
Cike da mamaki zuby tafito ganin sundoshi kofar shiga gidanne yasa zuby tsaya tace"baby cemaki nayi kikaini gidansu yarinyar da mijina yake nema da aure,banan nace kikawoniba"Ko jiyowa batayi tabata amsa dacewa"kede kishigo inatunanim yarinyar tananan gidan"
Haka sukasa kai suka shiga,kwance sukatarar da ita tanata kuka zuby tayi saurin cewa"subhanallah,deena miye tasameki kike kuka,kobakyajin dadine"Ko arzikin dagowa deena batayiba balle tabata amsr tambayar datayimata.
Shiru yadan biyo baya sana daga bisani billy tace"anty zuby aiba kowabace wadda mijinki keson aure illah deena,kuma naci alwashin deena bazatataba auran mijinkiba inde inaraye baza'ayi wannan cin amanar daniba"Daskarewa zuby tayi a inda take,jitayi kafafuwanta sunkasa daukarta nan take tadurkeshe kasa tana ajiyar zuciya,dago kai zuby tayi takalli billy tasakarmata murmushi tace"Allah sarki my love,ashe son dakikemin haryakai haka,kidanne farin cikin yar uwarki domin kifarantamin,lalle yau kinkara tabbatarmin dacewa keta musammance agareni,kuma haka yakarasakamin sonki acikin raina,inde nice zubaida nayarda kuma na'amince madeena ta'auri mijina,kuma wallahi namaki alkawari madeena zamuyi zaman lafiya dajuna,don haka inde akan wannane kishare hawayenki,nide agareni babu wata matsala kinji yayar baby"
Dago fuskarta tayi wadda takumbura tadaura idanuwanta akan fuskar zuby,tabbas tahango alamun gaskiya a idon zuby,to amma ita yanzu batada tabbacin shin mijin nata zata aura kokuwa,kafin ta iyacewa komi billy tabarko wata uwar ashar"narantse da allah bazata sabuba,idanma asiri tamaki garama yasakeki dan deena bazata taba hada miji dakeba dear,haba dan Allah,wannan wane irin katobarane kadafa kimanta deena tasanki,tasan koke wacece agabantama cina kikeyi sana kuma kice kinyarda ta auri mijinki,tabudeme gindi yaci kamar yadda yake cinki,ina bazatataba sabuwaba"tamurguda baki.
Wani wawan mari taji yasauka afuskarta,dafe kunci billy tayi tana mamaki"kika mareni deena,yau nice kike daga hannu kimara,lalle wu.....aibata karasa mizatafadaba deena takara wanketa dawani sabon marin sana tadaura dacewa"billy nagaji dawanan halin ko inkula dakikeyi agareni,wadda kike takamar karewa to ita kanta tace tayarda na auri mijin nata,kinje kinhadani da dr sambo akan yazo yanemi aurena,to wallahi kibude kunnanki dakyau kiji mizam fadamaki,aurene de kikeso kirusa ko,billy baki isa kihana abibda Allah yariga yakaddaraba,kuma bazan auri samboba sadiq shizan aura,kinje kifadama matarsa tazo itama ta amince to miye kuma kike bukata,narantsemaki da girman Allah gab nake danabayyana abinda muke boyewa ga iyayenmu muddin bazaki fita daga sabgataba kinji nafadamaki"Wani murmushin takaici billy tasaki"kibayyana,to saimi idan kinbayyana,sai miye,kece ke bakisan abinda yake wakanaba,amma nikam from a to z nasan komi,don haka bajin tsoron kowa sai wanda yahalicceni,tun kafin kikaiga fadama iyayenmu halin damuke ciki wata zatarigaki fadamasu,kumani ashirye nake danadauki duk wani abinda zaitunkaroni ehhe"
Tsawa zuby tadakamasu su duka biyun"ya isahhhh,haba miye hakane,kuna abu kamar wasu kananun yara,ke billy am warning uh,wannan magabar abarta,tundade nace na"amince to kema yazama wajini ki amince kodan farin cikina,idan harna isa dake to narokeki da kada nakarajin kince wani abu akan maganar auranan idan kuma bam isaba kije kiyi duk abinda zakiyi"
"Shikenan naji kuma nadauki abinda kikace,dande kince nakyale ammde shikenan kawai"
Haka zuby taja hannun billy sukafita daga gidan tajata sukatafi gidanta.
Yau takama laraba,tun safe deena taji gabanta nafaduwa amma saita lazamci innalillahi wa'inna ilaihi raju'un.
Billy ko baccin asara kawai takeyi don yau basu shiga skul ba,karfe shabiyu mahaifinsu yakirasu akan gashi akofar gida,tashi tayi tasaka long hijab dinta,hartakai bakin kofa tatuna da wayoyinsu tadawo tadauki tata takashe,ta billyn ma takashe tasakasu acikin akwati sana tafita tabudeme gidan,sai yaken dole takeyi wanda baikai cikiba,atare suka shigo,nan takawome ruwa da lemu masu sanyi tazauna suna gaisawa.
"Madeena ya karatu"?
"Abba karatu alhamdulillah"
"Waccan ragguwar ko ciwon kainne haryanzu"
"Aah abba kawaide baccine,nima wayarkace tatadani"
Kafin abba yayi magana har billy tafarka,ware idonta tayi akan nama haifinsu aiko tayi saurin sakin salati tare da dirowa daga kan katifar takifa kasa tana kwasar gaisuwa,cike dajin dadi ya amsamata tareda tambayrya karatu tabasa amsa da lafiyalo.Yananan zaune akakira sallahr zuhr yatashi suka sakamai ruwa abuta yayi alwala yafita zuwa masallaci,kafin yadawo deena tayi saurin shiga kitchen tadafamai jelof din taliya Takawo dakin ta'ajiyeme sana tafita tayo alwala tazo tayi sallah.
Bawaini jima da fitaba yadawo,zama yayi yadanci abinci deena tadubesa kai asunkuye tace"abba dama akwai maganar danakeso nayima"
Kallonta billy tayi tadanji gabanta yafadi.
"Inajinki madeena go on""Am uhm,dam..am"
"Dama mi?kiyi maganarki mana"
"Abba dama wanine yadameni akan yanaso yazo gurinka domin yanemi izinin zuwa wajena".
Ajiye cokalin abba yayi yadubeta da kyau yace"amma madeena kinsande cewa bana aurar da yarana harse sungama karatu ko?,kiyi hakuri tunda kinkusa gamawa sai yazo ayi magana,ala barshi kinyi service din agidansa""Amm abba damacewa yayi zaizone domin asan dashi,shine naceme yabari nafadama naji mizakace"
"Ohk badamuwa,kiceme yajira kikammala karatunki sana sai yafito,kinjini ai"
"Eh abba kuma zanfadamasa sakonka"
"Yawwa bari natashi,akwai aikin dazamuyi gobe zamuwuce"
Kafin yamike sukaji ana bubbuga gida,wata irin faduwar gaba tariskesu suduka biyun,domin basusan waye zaishigo gidanba.
Lallabawa deena tayi tace"abba bari naga kosuwaye yanzu haka assignment din dana arane akamedomin" tafice tanadafe kirji.
Bude gidan tayi idanuwanta sukamata tozali da anty,jitayi gabanta yatsananta faduwa,kuma taki kaucewa antyn tashiga harseda antyn itada kanta tayi magana"ranki shidade kibani hanya nawuce kinyi tsaye kina kallona kamar wadda batasanniba,kode bakiyi farin ciki da zuwanabane kina gani yau harda bakuwa nazo"
Yake deena tayi wanda yafi kuka ciwo,dan ita ayanzu anty haushinta takeji,bude baki tayi bakin nata nakyarma tace"am...a...m..dan Allah anty kiyi hakuri abbanmu yazo yanzu haka yanacikin gidanan kuma idan yaganku ahaka wallahi munbani,tsautsauran ra'ayi garesa,yanzu zaitafi yamatashi kenan naji bugun gidan,koda cikin motane kutsaya idan yatafi saiku shigo plss"
Wani murnushin mugunta anty tasaki tareda kallon suby ta bakin glass dinta itama tasakarnata murmushi"am baby bazaice komiba kawai kibari mushiga,basai mucemasa mu yan class dinku bane"tanafadin haka kawai tajanye deena sukasa kai acikin gidan,deena saurin binsu tayi tanafadin"nashiga ukku ni deena"Ko sallama basuyiba suka daga labulan tareda sakai aciki,ai wata irin razana alhaji yayi dayagansu,bakinsa har kyarma yakeyi wajen fadin"wayace kubiyoni nan,nafadamaku zandawo yanzu"
.wata dariya anty tasheke da ita tareda cire bakin space din dake fuskarta tace"cool ur ming alajina,ni bakai nabiyoba,gurin yaranka nazo"Cike da mamaki alhaji yace"yarana kuma,miye hadinki da yarana,cikin wata kakkausar murya"?