part 3

102 8 1
                                    

_*Typing*_💻

          
       _*🌻🌻HAMDEEYERH🌻*_       

©️ *HIKIMA WRITER'S ASSO.🌻*
_Home of peace, joint of entertainment,to educate & to enlighten  our reader's._

   
_LITTAFIN KYAUTA._
*MALLAKAR*_ummie2018💜_

_*marubuciyar*_

1- _AYSHAT(complted)_

2- _ZATOH(completed)_

3- _NUNA SO GABAN KISHIYA(completed)_

4- _TA'UMMU KA (incomplete)_

5- _NIGERIA KO NIGER(incomplete)_

6- _ANYA KUWA...?(rate book)_

     ~and now~

7- _HAMDEEYERH_

_GARGAD'I! GARGAD'I!GARGAD'I❌_

_Ban yarda wata ko wani yajuyamin sigar labari na ba,koda kuwa kalma dayace! duk wannan ya aikata hakan a gareni zamu gamu a fadar mai sama!!_

_i dedicated the whole this book to all writer's of hikima writers association🌻_

   *charpter 3*

    
"deeyerh bak'yajin magana wlhi!! miyasa kikemana haka ne? kina son ciwon zuciya ko hawan jini yakama mamami duk a ta sanadiyyar rashin jin maganarta da bak'yayi...? ko kuma so kike nima bak'in cikin halinda kika daura ma kanki yazama ajalina ne...?" daughter takare maganar cikin alhinin halin k'anwar tata...!

fuskar tausayi tak'ara yafawa bisa fuskarta bawai don tanajin zata iya daina ba,saidan kawai ta kwantar mawa yar uwarta da kuma mahaifiyarta da sauran yan uwanta hankali!! "am very sorry my anty,i promise you bazan sake ba,kuma kema ki tayani da addu'a plss" takare maganar cike da sangartarta a fili kamar yar shekara goma,murmushi antyn nata tayi tace "allah ya nunamin ranar da kanwata zata shiryu kamar ko wacce yarinya"  a k'asan leb'e rabin rai ta ansa da ameen!

hannunsu sark'e da juna suka fito parlo,inda suka tarda iyalan gidan baki dayansu zaune bisa dining,su kad'ai ake jira ansan dama kuma a daidai wannan lokacin suna tare!!

yaran gidan guda biyar ne,akoi _marwan_ wanda yakasance shine first born a gidan,tazarar shekara uku ne t'sakaninsa da daughtet,sai kuma daughter asalin sunanta _nawwara_ suna kiranta da anty,mamami kuma kan k'irata da daughter,sai kuma _umar_ suna kiransa da faruq yake bima nawwara wanda tabasa 2yrs,sannan _tahir_ wanda akoi tazarar shekara uku tsakaninsa da faruq,bayan shi kuma sai _HAMDEEYERH_ wacce takasance yar autar gidansu wacce idan kana son katabo bacin ransu toh ka taba wannan yarinyar ka gama k'wak'ulowa kanka jaraba hakan yasaka take tsula iya shegenta son rau!

asalin mahaifinsu sunansa alh adamu muhammad kwangila dan asalin garin misau ne,wanda yataso hannun matar ubansa mai suna inno nawwaratu,sbd yarasa iyayensa tun yana dan shekaru 3 a duniya,inno takasance mace mai faram faram da jama'a,kuma kowa ma nata babu ruwanta da wannan nawa wannan ba nawa ba dukda ma bata tab'a haihuwa ba a wannan lokacin!!

adamu dan gatan innno ne sosai ba kad'an ba sbd da soyayyar yara taso cikin zuciyarta amma allah bai bata ba,sannan dama basu da wasu dangi na azo a gani duk sun k'are,sauran dssuka rage kuma sun yada zumunci ballanta wani yayi tunanin d'aukarsa a matsayin jinin yan uwansu..!

da dadi babu dadi har adamu yakai shekaru 10 a hannun inno,har makarantar gwamnati tasaka shi da guminta,wanda a lokacin kuma allah ya yanke masu wahala domin ko wani mutumi ne mai arziki dayazo garin domin ziyartar abokinsa yaga inno kuma ya k'yasa,ba'a wani dau lokaci ba kuma suka samu fahimtar juna,da sharadin zai barta ta tafi da adamu,shima bayyi musu ba kasancewarsa yana son yara sosai ammma allah bai bashi ba,sanadiyyar hakane ma duk matar daya aura take rabuwa dashi,to inno ganin matsalarsu ma takusan zuwa d'aya sai kuma tazage dant'se suka taru suka rufana juna asiri bayan an daura aurensu suka wuce garin kaduna sbd acan gidan alhaji musa k'wadago yake a unguwar gomna road,rayuwa suka shimfida cike da gaskiya dakuma amana,shima adamu alh yasaka shi a makarantar kud'i,hakanne yasaka shi maida hankali sosai kan karatunsa sbd karatu shine burinsa...!

basu rufe shekara ba cikin ikon allah saiga ciki ya bayyaja jiki inno wanda hakan ba k'aramin farin ciki bane ya mamaye zuciyar wayannan ahalin,adamu kamar yazuba ruwa a k'asa yasha inno zata haifa masa kanwa ko kani shima!!

bayan wata tara ta sullub'o da yarinyar k'yakk'yawa ba laifi taci suna adama,ai kuwa gatan duniya nan adama na shanta a wajen iyayenta dakuma yayanta ko k'uda basa so yatab'ata!

_bayan shekaru sha biyar_

akayi auren adama da adamu wanda ba hadin kowaa bane saina inno sbd tasan babu wanda zai kula mata da yarinyarta da zuciya daya kamar adamu!! shima bayyi musu ba ya amince sbd babu abinda ake bukata a jikin ya mace da adama ta naima ta rasa,saidai kuma hali wanda baza'a rasa ba,gata da dan banxan kishi kamar me!? allah yayi ma alhaji musa rasuwa kuma dan haka adamu ya tarkata inno da matarsa xuwa garin kano a unguwar rigiyar lemo sbd kud'i bai fara shiga masa ba a wannan lokacin,anan suka tare a madaidaicin gidansu!!

adama tasamu danta namiji a haihuwar farko wanda aka saka masa suna _marwan_ mai sunan mahaifinsa na asali kenan,bayan three years takara haihuwa tahaifo ya mai kama da ita aka saka mata suna _nawwara_ wato mai sunar inno,saikuma _umar_ mai sunan kanin babansa,dagashi sai  _musa_  mai sunan babanta!! a lokacin allah yamawa inno rasuwa wanda ta tafi tabarsu ckin kewa,,,kuma allah yabud'a na adamu cikin harkarsa ta kwangila dayakeyi,ba adau lokaci ba sunansa ya shahara a fadin garin kano dama sauran state namu na gida nigeria!

a unguwar new gra ya dangara uban gininsa ya kwashi matarsa da yayansa suka tare a sabon gida,inda acan ne aka haifi auta _HANDEEYERH_ wacce take da kyawu na ban mamaki! yarinya mai sanyi hali da sanin yakamata mai tunanin manya! ba k'aramin son wannan yarinya bababi yakeyi ba kasancewarta mai sunan mahaifiyarsa yasaka mata! kullum zaka jishi yana mamana mamana!

kwat'sam rana daya ta t'sinci kanta a halin shaye shaye,wanda duk ranar da bata shaba babu zmana lfy,kuma bababi bashi da labari ko kad'an,ba karamin tashin hankali nauwara tashiga ba,mamami ce tasani ita da nauwara, kullum cikin fada da nasiha suke mata amma abin yaki ci yaki cinye wa!
ba k'aramin shakuwa bace t'sakanin nauwara da hamdeeyerh,wanda hakan kuma daga allah ne😚

a halin yanxu marwan nada 30yrs a duniya,sakuma nauwwara 27yrs kuma har yanxu batayi aure ba,sai umar 25,musa 22 saii auta 17yrs!!

sai zuwa bayan sallah idan allah yakaimu❤️
  
vote
comment
share

       _UMMIE2018_💜

HAMDEEYERH!Where stories live. Discover now