part 7

59 6 0
                                    

_*Typing*_💻

          
       _*🌻🌻HAMDEEYERH🌻*_       

©️ *HIKIMA WRITER'S ASSO.🌻*
_Home of peace, joint of entertainment,to educate & to enlighten  our reader's._

   
_LITTAFIN KYAUTA._
*MALLAKAR*_ummie2018💜_

_*marubuciyar*_

1- _AYSHAT(complted)_

2- _ZATOH(completed)_

3- _NUNA SO GABAN KISHIYA(completed)_

4- _TA'UMMU KA (incomplete)_

5- _NIGERIA KO NIGER(incomplete)_

6- _ANYA KUWA...?(rate book)_

     ~and now~

7- _HAMDEEYERH_

_GARGAD'I! GARGAD'I!GARGAD'I❌_

_Ban yarda wata ko wani yajuyamin sigar labari na ba,koda kuwa kalma dayace! duk wannan ya aikata hakan a gareni zamu gamu a fadar mai sama!!_

_i dedicated the whole this book to mamana da babana allah yakara nisan kwana mai albarka ameen_

   *charpter 7*

jin yadda ake shafa mata gefen fuskarta ne cikin bacci yasa tafara mik'a tana babbank'arewa babu addu'a ballanta salatin annabi domin neman kariya!!

ganin tafarka yasaka antyn nata shigewa toilet ta d'auro alwalar azahar domin ko har lokaci yad'an shige masu...!

bayan tafito ta tarda kanwartata tak'ara komawa baccin nata,hakan ne yasakata yarfa mata ruwan alwala daya mak'ale mata a hannu,

a shagwab'e ta k'ara tashi tana yayyat'sina fuska sbd jin ruwan yamata sanyi a fatar jikinta,anty bata kulata ba tana shimfid'a babbar darduma ta tada kabbarar salla!

ganin hakanne yasakata kallon agogon dake mak'ale jikin bangon office din,babu shiri tamik'e tafada toilet itama sbd duk iya shegenta bata wasa da sallah,nat'suwa tayi addu'oi bayan idar da sallah ne kawai ke mata wuya!!

alwala ta dauro bayan tafito itama ta sank'ama hijap na antyn nata sbd already ita tariga da ta idar,ta fuskanci alk'ibla ta tada kabbara sallahrta!

abin mamaki...? yadda naga tana sallar tata cikin t'sant'ar ilmi na addini abin yaban mamaki,komai cikin nat'suwa da sanin hukunce hukuncen saallr takeyi,bayan ta idar ta mik'e ta ninke hijap da dardumar ta maida su mazauninsu!

kallon yar uwar tata tayi da hankalinta yanaga kan wani file datake ciccikesu sbd zata sallami wasu maras lafiya!

"anty na,wlhi yunwa nakeji! ciki na kamar an mani yasa" tafada tana wangale k'aramin bakin wato hamma!

dago kanta nawwara tayi bayan ta dakatar da abinda takeyi ta zubama kanwartata ido tana kallon cike da tausayawa,sbd dama duk mutumin dake shan barasa baya tab'a jumurin jure yunwa ko k'adan,a baya sam hamdeeyerh bata son cin abinci sai anyi da gaske,amma yanxu kam...? ko ba'ace taci ba dagudu take naima dan kanta!!

batare da tayi mata magana ba ta d'auke idanunta akanta ta danna k'ararrawar sanarwa zuwa reception na asibitin,babu b'ata daya daga cikin messangers na asibitin yayi knocking, tabasa izinin shigowa, bayan ya shigo ta lisafa masa abin da take buk'ata wanda zay ishesu suyi lunch dashi!!cikin girmamawa ya ansa kud'in ya fice!!

suna nan zaune suna hirarrakinsu na yau da kullum daya dangancesu...,
cikin hikima da dabara daughter ke nuna mata illar shaye shaye a mat'sayinta na likita,dadai duk abinda yakamata a fahimtar da ita,daya kamata tasani ko allah zaisa tayima kanta fad'a ta fuskanci rayuwa...!

itama hamdeeyerh data kasa kunne tanajin yayar tata,bawai d'auka take ba! yana shiga ne tanan yana fita ta daya...,sbd  itafa komai akeyi bata tunanin zata iya daina shaye shaye koda kuwa daidai da rana daya ne...!yanxunma kawai jiran lokacin da ta k'aidade takeyi ta fece taje ta tuttulawa cikinta domin ko harta fara jinta wata kala daban,da bata je ba!!

suna nan suna tattauna mat'salolinsu messager yakawo masu takeaway din daya sawo masu a wani restaurant mafi kusa dasu...,zama sukayi suka ci abincinsu t'saf,bayan sungama kuma daughter taci gaba da  cike ciken files dake wajenta na marasa lafiya!

k'arfe 6:30 na yamma bayan sunyi sallar magriba duk a asibitin,akoi operation na gaggawa da nawwara zata shiga wanda aka kawo a emergency na wata matashiyar budurwa da appendix ya fito mata,basu ankara da abinba saida yaci k'arfinta...,saida ta zaunar da hamdeeyerh  ta k'ara mata gargad'i kan karta kuskura ta fita ko nan da bakin kofa!! ta ansa mata da "toh" amma kuma fa bawai har cikin birnin zuciyarta ba!!

sun shiga operation lafiya qlaou wajen k'arfe bakwai,sun shafe kimanin awa uku lafiyayye,sai k'arfe goma suka fito,wanda a gajiye suke tulus da sauran ma'aikatan nata!!

tana shiga office nata toilet ta fada,ta tari ruwan dumi tayi wankanta t'saf tafito tazo ta saka simple gown nata datayi guzirinsa tun daga gida tayi sallar isha'i,taci guntun abincin da take kyautata zaton rabin rai ce ta ajiye mata daga nan ta had'e duk abubuwan datasan masu amfani ne, amma bata ga key na motar tata ba,hakan yasa taja office nata ta fito zuwa harabar asibitin,amma wayam babu kalar motarta babu dalilinta sai t'sirarrun motoci na ma'aikatan dake k'ark'ashinta wayanda suke night duty!

ita a tunaninta hamdeeyerh ta gaji da zaman guri daya ne,shiysa ta taho mota domin ta jirata,amma gashi kuma hasashenta na naiman zama ba gaskiya ba...??

hakan ba k'aramin d'aga mata hankali yayi ba,bata t'saya b'ata lokaci ba ta fice daga asibitin ta tari dan taxi zuwa gidannansu domin dubawa ko ta koma gida!!

isanta gida ta tarar da abinda yak'ara daga mata hankali,babu motarta babu dalilinta,saima motocin bababi data iskesu fak'e a parking load na gidan da bababi ke amfani dashi, alamun yadawo daga tafiyar sati dayan data kamasa...!!

tun daga bakin k'ofar shiga main parlo nasu take jiyo hayaniyar yan uwannata dakuma iyayennata,alamun suna cikin farin cikin dawowar bazatar da mahaifinnasu yayi...!!

parlon ta shiga cikin sanyin jiki dakuma fargabar abinda zata tarar yau din!!

kaminlallen dattijon wanda kallo daya na masa na fuskanci inda handeeyerh ta kwaso kamanninta,domin ko kamarta daya da mahaifinta saidai ita mace shikuma namiji ne...!

sun sashi a tsakiya sai hirarsu sukeyi,amma kuma ga dukan alamu su ake jira...

cikinta ne ya bada sautin k'ulululuuu! sbd yanda taga sun zubo mata ido,duk mik'ewa sukayi suna kallonta sbd ganin yanayin datake ciki,babu yanda ta iya haka ta shigo da sanyin jiki tana rarraba idanuwa!

fara'ar fuskarsu ne yafara gushewa izuwa damuwa,bama kamar bababi...!!domin ya tabbata ba lafiya ba,tunda yaga yar tasa haka, gashi kuma baiga hasken idaniyarsa ba hakan yasa zuciyarsa fara lugude...!

mamami kam kanta yana k'asa ballantana nagane maku yanayin furgicin data shiga na rashin ganin rabin rai nata...!

suko sauran yan uwanta musa,umar da marwan dayake hutun sati daya dauka wanda sanadiyyar hakanne yake gida a halin yanzu duk sunyi tunanin b'uya deeyerh tayi sbd tayima bababi wasa dasuka saba!

ganin yanayin yadda nawwara tashigo alamun damuwa sai duk suma suka shiga damuwar domin ko sun tabbatar ba lafiya ba!!

babu wanda yasamu zarafin magana acikinsu wayar bababi yadauki ringing,baiyi k'asa a gwiwa ba yayi recieving domin jin sautin k'iran yar lelensa abin alfaharinsa, duk suka zuba masa na mijiya ganin yanayin yadda yamike a firgice!!

    

pls don't forget to :

vote
comment
share

       _UMMIE2018_💜

HAMDEEYERH!Where stories live. Discover now