_*Typing*_💻
_*🌻🌻HAMDEEYERH🌻*_©️ *HIKIMA WRITER'S ASSO.🌻*
_Home of peace, joint of entertainment,to educate & to enlighten our reader's._
_LITTAFIN KYAUTA._
*MALLAKAR*_ummie2018💜_
*oum muntaz*_*marubuciyar*_
1- _AYSHAT(complted)_
2- _ZATOH(completed)_
3- _NUNA SO GABAN KISHIYA(completed)_
4- _TA'UMMU KA (incomplete)_
5- _NIGERIA KO NIGER(incomplete)_
6- _ANYA KUWA...?(rate book)_~and now~
7- _HAMDEEYERH_
_GARGAD'I! GARGAD'I!GARGAD'I❌_
_Ban yarda wata ko wani yajuyamin sigar labari na ba,koda kuwa kalma dayace! duk wannan ya aikata hakan a gareni zamu gamu a fadar mai sama!!_
*charpter 27*
wani gagarumin abu ne ya t'sirgama abdulbasid game da k'anwar tasa na ganin yadda albarkatun k'irjinta ke mot'sawa wanda hakan ba k'aramin k'ara rurata masa wutar sha'awarta keyi ba,gashi kuma babu halin ya d'ana sbd nauwara data masa babban gatanga!
wanda tin ba yauba ya fahimci k'aunar k'anwar matar tasa dakuma t'sant'sar sha'awar ne yake d'awainiya dashi,ba kuma wai dan nawwara ta gaza masa ko kuma baya gamsuwa da ita ba! sbd idan yace ga wani bak'in hali mara k'yau da nawwara ke masa a iya t'sawon zamansu yamata babban sherri a rayuwa...!
sukam basu sanma yanayi ba sbd kansa na kallon k'asa ballantana susan yanayin dayake ciki,saida ya saisaita kansa kamin yad'ago idanuwansa da har yad'an chanza launiii...
anan dae sukayi sallama nawwara tawuce asibiti sbd akoi operation d'inda zata shiga 7:30am d'innan gashi yanxu kuma har wajen bakwai takawo kaiiiii!
bayan wucewarta hamdeeyerh tabar umaima da babanta ita kuma ta koma kitchen ta girka msu abin karyawa sbd yanxu kam ta k'ware a fannin girki sai d'an abinda ba'a rasa ba abinka ga d'an adam!
bayan ta gama takai masu dining,tare sukayi breakfast nasu su uku kamin abdul yayi masu sallama yawuce campanyn su shida bababiiiii!
ita kuma bayan tayi wanka suka fito da k'afa suka taka zuwa gidansu inda suka tarda mamami a parlo nan suka yada zangooo!
********A nan zauna abinsu suka sha hirar su,har ya musa ma yadawo daga gurin aiki ya tarda su,sai ana k'iran magriba ya maida su gida...! sbd acan nawwara ke yawanta zama yanxu!
shigansu gida ma babu wanda yadawo a cikin masu gidan,dan haka hamdeeyerh ta shiga kitchen ta masu dinner umaima na tayata hira da gwarancinta!
bayan ta kammala takai dik abinda zasu buk'ata dining ta d'auki umaima dake kiranta da ammi na zuwa d'aki,wanka tayi mata itama tayiwa kanta daga nan suka shirya cikin sleeping dress sai zuba k'amshi sukeyi,saida sukayi sallar isha'i kamin suka fito parlo sukaci iya cinsu daga nan kuma hamdeeyerh ta kwanta kan 3seater ta d'aura umaima akan cikinta dake k'ananun kukan ta na naiman umminta...!a haka har wani daddad'an bacci yayi gaba dasu! tana mai jin wata kalar fad'uwar gaba!
******** can cikin baccci taji ana d'an jajjan yat'sun k'afarta,hakanne yasakata mik'ewa zaune bayan ta kwantar da umaima tana mut'sit'st'sika ido alamun baccin bai isheta ba sai bank'arewa tayi wanda hakan yakusa zautar da abdul dake t'saye akanta yana binta da wani mayen kallo!
ganin sa akanta haka saida gabanta ya fad'i amma saita mazge tafara masa sannun da zuwa,tana da niyyan mikewa ya dawo da ita tazauna a gefensa wanda hakan yasaka zuciyarta fara bugawa kamar ana buga ganga,kallonsa take kamar bashi na,sbd wannan ne karo na farko daya tab'a mata haka dikda kusanci dake t'sakaninta dashi!
YOU ARE READING
HAMDEEYERH!
Historical Fictionlabari ne mai cike da sark'ak'iya,idan kuna bibiye da alkalamin ummie2018 zai warware maku zare da abawa