part 23

37 6 0
                                    

_*Typing*_💻

          
       _*🌻🌻HAMDEEYERH🌻*_       

©️ *HIKIMA WRITER'S ASSO.🌻*
_Home of peace, joint of entertainment,to educate & to enlighten  our reader's._

   
_LITTAFIN KYAUTA._
*MALLAKAR*_ummie2018💜_
*💞oum muntaz💞*

_*marubuciyar*_

1- _AYSHAT(complted)_
2- _ZATOH(completed)_
3- _NUNA SO GABAN KISHIYA(completed)_
4- _TA'UMMU KA (incomplete)_
5- _NIGERIA KO NIGER(incomplete)_
6- _ANYA KUWA...?(rate book)_

     ~and now~

7- _HAMDEEYERH_

_GARGAD'I! GARGAD'I!GARGAD'I❌_

_Ban yarda wata ko wani yajuyamin sigar labari na ba,koda kuwa kalma dayace! duk wannan ya aikata hakan a gareni zamu gamu a fadar mai sama!!_

   *charpter 23*

******Nasiha sosai ya audu yak'ara masu bayan nat'sar da kowa da yayi cikin hayyacinsa a wajen,wanda zuwan da yayi aka samu baba yusufa ya farfad'o daga gajeriyar sumar da yayi,musa ne ya ankare da sumewar da hamdeeyerh tayi wanda akasa mata ruwa itama kamin ta dawo hayyacinta,sai rarraba ido take kawai zuciyarta cike da k'unci!!

bababi ma yadawo hayyacin sa daga tarin daya sarke masa,sai kallon baba yusufa yake da d'umbin mamakin mai yamasa har haka da zafi...?

mamami,nawwara dasu goggo da inna ma duk kansu a duhu yaje sbd rashin sanin ma'anar abinda yafaru a yau dinnan t'sakanin su da mutanen da suke ganin mutuncin junansu...!

haka dai da kyar yasamu yakashe gobara ya tasa k'eyar su abdulbasid da sai harara suke aikama dasu faruq shida k'anwarsa kan da safe za'a warware mat'salolin!

ganin talabijin da ya audu yayi ne yadawo dashi gidan sbd ya k'ara basu hakuri sbd shima yasan wannan ba aikin kowa bane sai d only sister nasa!

      ******

bayan kowa ya nat'su cikin tangamemen parlon nasu a lokacin da aka gama gaishe gaishe sai harare hararen juna sukeyi wanda hakan yakan bama baba kamaye dariya da tare suka zo da ya audu bayan ya kork masa jawabin abinda yafaruu!

Baba yusufa ne ya shaida masu dalilinsa na abinda ya aikata daren jiya sbd buk'atar hakan da su baba kamaye sukayi,tunda koba komai sud'in sunyi iyaye dasu!

" *Kamar yadda kuka sani,deejama y'ar k'auyen mazigai ce data taso tare da yayanta datake matuk'ar so da k'aunarsa,haka shima anasa b'angaren ba k'aramin son k'anwar tasa yakeyi ba,wanda har takai takawo muddin tace tana son abu idan bai cika mata burin ta ba,koma menene,ji yake kamar bai kyauta mata ba sam...!*

*Akoi sa'anninta na cikin k'auyen dake zuwa aikatau cikin birni,wanda hakan yasaka ta d'agama yayanta hankali kan lallai lallai sai an sama mata aiki itama tabi ayarin k'awayenta kamar yadda taga sunayi,bakuma wai dan ta rasa ci da sha ba saidan kawai itama tazo taga yadda birni yake kasancewarta yarinya mai baki...!*

*Akoi wata goggon su wacce itace ke kawo yara aikatau cikin birnin kano idan suna buk'ata,wanda ta gurinta ne aka samu aka mawa deejama ciku cikun samun aiki gidan adamu kwangila suka lula bada son ran yayan nata ba saidan babu yanda ya iya*

*a hanyar dawowar goggo daga garin kano a lokacin da take dawowa daga kaisu deejama da tawagarta hat'sarin mota yasame su da y'an cikin motar,wanda hakan yazo da k'arar kwana,batare da ta gayama yayan deejama gida dakuma unguwar da takai k'anwar tasa da sunan aikatau ba aka kai masu gawarta...!*

*sunyi kuka a lokaci kamar me na rasuwar goggon tasu shida matarsa,kasancewar auren had'in gida aka masu da matar tasa mama habeba wanda a wannan lokacin suna da yaronsu guda d'aya wato abdulbasid d'an shekaru 12 a duniya,wanda kwata kwata t'sarar 2yrs ne t'sakaninsa da deejama data basa,hakan yasaka su tasowa kansu had'e kamar wa da k'ani... !*

HAMDEEYERH!Where stories live. Discover now