_*🌻🌻HAMDEEYERH🌻*_
©️ *HIKIMA WRITER'S ASSO.🌻*
_Home of peace, joint of entertainment,to educate & to enlighten our reader's._
_LITTAFIN KYAUTA._
*MALLAKAR*_ummien2018💜_
*💞oum muntaz💞*_*marubuciyar*_
1- _AYSHAT(complted)_
2- _ZATOH(completed)_
3- _NUNA SO GABAN KISHIYA(completed)_
4- _TA'UMMU KA (incomplete)_
5- _NIGERIA KO NIGER(incomplete)_
6- _ANYA KUWA...?(rate book)_~and now~
7- _HAMDEEYERH_
_GARGAD'I! GARGAD'I!GARGAD'I❌_
_Ban yarda wata ko wani yajuyamin sigar labari na ba,koda kuwa kalma dayace! duk wannan ya aikata hakan a gareni zamu gamu a fadar mai sama!!_
*charpter 13*
fisge fisgen da takeyi ne ya haut'sinama bababi hankali a lokacin daya k'arasa shigowa ward din datake ciki,ga likitoci nan akanta suna iya bakin k'ok'arinsu domin a t'saigaita daga yunkurin datake kan lallai lallai saita fita,wanda a dalilin hakan ciwukan dake jikinta suka fara t'sat's t'safo da jini domin an fame su!
wanda duk wani mahaluk'i mai burbushin imani idan yaganta a wannan stage din sai ya tausaya mata,goggo da inna idan banda sharar hawaye babu abinda sukeyi sabida raunin zuciya irin na mata!
"mamami dan allah kixo kice subarni natafi naje nasha kozanji sauk'in dana keji a cikin k'wak'walwata,zan mutu!wayyo anty na kizo ki ceci rayuwata a gurin wayanda basu san amfaninta a gareki ba! bababi kayi sauri kazo ka taimake ni daga hannun wayannan azzaliman!wayyo ya faruq kuzo ku ceci kanwarku,shikkenan yau rayuwata tazo k'arshe bata da amfani!"
wayannan sune kad'an daga cikin kalmomin da hamdeeyerh ke ambata cikin kuka da fusge fusge na fitar hankali!
"innalillahi wa'inna ilaihir raji'un",wayannan sune kalmomin da amma mahaifiyar marak'isiyyerh keta nanatawa cikin zuciyarta,
bababi ne da yayi tsaye daga bakin k'ofa ya gagara k'arawa tun d'azu ya daga k'afarsa zuwa bakin gadon,wanda hakan yasa d'aya daga cikin likitocin dake kanta,tabasa guri yashige
aikuwa hamdeeyerh nayin tozali da mahaifinnata batabi ta ciwukan dake jikinta ta fad'a masa jikinsa ta kanainayesa,tana runtuma ihu wanda hakan yasaka adamu kwangila fashewa da kuka kamar bana miji ba! yafara tofama yar tasa duk addu'ar data zo bakinsa,cikin ikon allah kuwa sai gata tafara lafawa da iface ifacen da takeyi!
wanda hakan yasaka mutanen wajen fara tofa mata addu'oi,sabida fahimtar wani abu da masu hankalin cikinsu sukayi! aikuwa kamar anyi ruwa an d'auke,saiga ta ta koma bacci wanda hakan ba k'aramin dad'i yamasu ba!
kamin k'iftawar ido da bismillah saiga ihun marak'isiyyerh ya karad'e cikin asibitin baki d'aya wanda tafara fisge fisgen dayafi ma na wanda hamdeeyerh tayi a karamin lokacin daya shud'e!
hakan ba k'aramin hargit'sa wayanda ke gurin yayi ba,bama kamar amma data ke ta mai maita kalmar "na shiga uku na lalace"
a dai dai wannan lokacin mamami suka iso asibitin tare da nawwara dakuma wata dattijuwar mata,da d'aya daga cikin ma'aikatan gidan wato raihanatu k'anwa ce ga abdulbasid,dattijuwar kuma mama habiba ce wato matar mai gadinsu baba yusufa!
yanayin dasuka gansu ba k'aramin kad'a masu hankali yayi ba,bama kamar nawwara data sulale a k'asa tafara rusan kuka kamar wacce allah ya aikota! mamami kam tazama statue,ta gagara mat'sawa ko nan da can illah kallon b'angaren da hamdeyerh da marak'isiyyerh suke kwance da takeyi!
idanunta ne yafad'a kan aminiyarta da tinda abin yafaru basu had'u ba sai yau!gabanta ne yafara lugude yana dukan uku uku! ta tabbata alhaki ne ke bibiyar rayuwar y'ar aminiyar tata a halin yanxu!
aiko suna had'a idanuwa,amma ta taso a hargit'se takamo hannun mamami zuwa gaban gadon da marak'isiyyerh ke kwance wacce likitoci sukayi nasarar surkud'a mata alluran bacci,
"adama kinga halin da y'ata tafada ciki duk a sanadiyyar cikar burinki,wannan masifa dame tayi kama sabida allah da annabi,kin cuceni adama kuma nima na cuci kaina,dukdama nice babbar doluwa bake ba!
dama haka mutum yakeji a duk lokacin da akace d'ansa yafad'a halin shaye shaye? allah na tuba kayafeni! allah karkasa abinda aka fad'amin akan yata ya tabbata yazama gaskiya,idan ko haka ta faru,na kad'e har ganye na ni hafsatu,!"duk mutanen dake gurin ido suka zuba ma mamami da amma a wannan wajen domin ko maganar da ke fitowa a bakin amma ba k'aramin kad'a hanjin cikin mutane da dama yayi ba!
mamami kam ji tayi kamar tasaki zawo a wando a wannan gurin,domin ko tasan yau watab k'arshen k'aryarta ta kama! bababi da ya t'sinci ma'anar wasu abubuwa da amma ta amma bata idan banda salati babu abinda yakeyi cikin zuciyarsa,dakuma dana sani!
nawwara mai kuka ma t'sir tayi kamar anyi ruwa an d'auke tana bin fuskar mahaifiyartata domin son gano wani abu!
mama habiba da raihanatu kam sunyi shuru kansu na k'asa domin ko basuyi mamakin kalma ko guda d'aya ba,idan sukayi comparing da abubuwa da kunnuwansu kan jiye masu a gidan iyayen aikin nasu lokaci zuwa lokacii!
mahaifin marakisiyyerh zuciyarsa sai dokawa takeyi sabida t'soron abinda zaije yadawo a wajen,ganin yanda kowa ya zurma masu idanuwa yasaka amma k'arfin halin bud'e bakinta tace "dan allah idan bazaku damu ba inaso zanyi magana daku baki d'aya"
"kowa ya fiskanci abinda ke gabansa zamu tattauna koma minene daga baya" bababi yayi k'arfin halin fad'a sbd shi yanxu bata komai yake ba sai jinyar tasa!
bayan sati uku
jikinsu kam yariga da yayi sauk'i said'an abinda ba'a rasa ba,wanda ake saka ran komai zaizo da sauki bada jimawa ba!
kullum idan kazo asibitin n and fam zaka samu manya manyan mutane dake kai kawo domin duba maras lafiya! wanda hakan ba k'aramin k'ara d'aukaka asibitin yayi ba,inda mutane da dama sukasan dazamansa a cikin garin kano,!
wanda wasu sukanyi tunanin idan sunada mara lafiya sai an fita dashi asibitin k'asan wajene kawai ake samun k'wararrun likitoci,nanko basusan nigerian ma muna k'wararrun ba,kawai rashin kayan aikine yake k'ara dak'ushe mana espiriance na likitocin namu da rashin samun t'sayayyun shuwagabanni na gari!
har yanxu goggo da inna ne kwana da hamdeeyerh a asibiti,a duk sa'anda hamdeeyerh tafara fisge fusge addu'oi ake tofa mata sai abin ya lafa,wanda a take a gurin kuma marak'isiyyerh ma zata fara nata wanda sai anyi dagaske ake samun abin yalafa!
yau aka sallame su baki d'aya inda aka dunguma zuwa gidan adamu kwangila domin a saurari da wacce kalar magana zata bullo masu...?
vote
comment
share_UMMIEN2018_💜
YOU ARE READING
HAMDEEYERH!
Fiksi Sejarahlabari ne mai cike da sark'ak'iya,idan kuna bibiye da alkalamin ummie2018 zai warware maku zare da abawa