part 29

37 5 0
                                    

_*Typing*_💻

          
       _*🌻🌻HAMDEEYERH🌻*_       

©️ *HIKIMA WRITER'S ASSO.🌻*
_Home of peace, joint of entertainment,to educate & to enlighten  our reader's._

   
_LITTAFIN KYAUTA._
*MALLAKAR*_ummie2018💜_
*oum muntaz*

_*marubuciyar*_

1- _AYSHAT(complted)_
2- _ZATOH(completed)_
3- _NUNA SO GABAN KISHIYA(completed)_
4- _TA'UMMU KA (incomplete)_
5- _NIGERIA KO NIGER(incomplete)_
6- _ANYA KUWA...?(rate book)_

     ~and now~

7- _HAMDEEYERH_

_GARGAD'I! GARGAD'I!GARGAD'I❌_

_Ban yarda wata ko wani yajuyamin sigar labari na ba,koda kuwa kalma dayace! duk wannan ya aikata hakan a gareni zamu gamu a fadar mai sama!!_

        *charpter 29*

******** "A iya t'sawon zamana da nawwara idan nace yau ga abinda tayimin na rashin d'a a ba k'aramin k'azafi nayi mata kasnacewarta mata mai t'sanani biyayya akan dik abinda na umarce ta dashi a mat'sayina na mijinta dan haka dik abinda zan fad'a a halin yanxu son zuciyata ce ta kaini ga aikata abinda zan fad'a maku a halin yanxu wanda na tabbata bazaima kowa dad'i ba,dan haka tin kamin nafara fad'ar komai ina fatan zan sami sassauci akan dik wani hukunci dazan fuskanta daga gareku..."

kowa kallonsa yakeyi a wajen jikinsu a sanyaye sbd sunsan cewa ya aikata wani babban kuskurene tunda yakwantar dakai yana naiman yafiya tin kamin ya furta abinda ya aikata...!

nawwara da hamdeeyerh kansu na k'asa sun gaza fuskantar junansu ko kad'an sbd ba k'aramin naurin nawwara hamdeeyerh keji ba a halin yanxu,ita kuma nawwara nama hamdeeyerh kallon maciya amana ne!

"tin a lokacin da mukayi aure da nawwara kowa yasan cewa hamdeeyerh na yawanta zama a tare damu sbd yanayin shak'uwarsu su biyu basa  iya cikakken kwana biyu batare da sun saka junansu a cikin idanuwa ba!

hakan yasa ko bayan munyi aure ma rabin kayan hamdeeyerh na gidan namu harma d'aki ne da ita nata nakanta,so yadda nikuma naga haka sai shak'uwarmu harma tazarce nada t'sakanina da ita,hatta da abinci ma wata rana tare mukeci da ita dikda sunan shak'uwa,ina cemata k'anwata tana cemin yayana!

a wannan zaman namu har yazamana hamdeeyerh sam bata damu da dik shigar dake jikinta ba muddin ina guri sbd ita kallon yayanta kamar su marwan takemin,bata tunanin nid'in ba muharraminta bane,ita kuma nawwara bata d'auki hakan a mat'sayin komai ba dan haka bata bada hankalinta a wajenba ballantana ta taka mata birki!

wanda nikuma hakan danake kallo yake dasa min mat'sananciyar sha'awarta dikdama dai nasan matata bata rageni da komai ba amma haka nan naji na kwad'aitu da suffar hamdeeyerh wanda muddin ban samu nat'suwa daga gareta ba banajin zan iya samun nat'suwar hankali na...!

daga nan nafara tunanin hanyar da zanbi domin cikar buri na inda nayi wani tunani ni kad'ae na yanke shawara batare da tunanin abinda zaije ya dawo ba...!!

jiya ne nasamu damar aiwatar da kud'iri na,na t'sawon shekara biyu danake jira...!

na rubutama nawwara takaaddar saki d'aya jiya da rana misalin k'arfe d'aya na rana wanda a halin yanxu ma ina tare da takaddar a tare dani..."

fasali yajama zancen nasa yana binsu da kallo na ganin yadda dik suka k'walalo idanuwa jin kalmar saki daya ambata bama kamar nawwara dake binsa da wani kalar kallo dana gaza gane fahimtar na minene...?

babu wanda yasamu zarafin magana acikinsu ya fiddo da linkakkiyar peper ya mik'ama mamami dake kusa dashi tana kallonsa da mugun mamaki...!

karb'a tayi tafara warwarewa cike da tashin hankali wanda abin ke rubuce b'aro b'aro ga dikkan alamu a cafe aka rubuta sbd yadda taga abin,gashi kuma daga k'asan pepern an rubuta time d'in da akayi printing dakuma date d'in wanda hakan ya tabbatar masu dagaske d'in jiya ya rubuta!

HAMDEEYERH!Where stories live. Discover now