part 25

51 4 0
                                    

_*Typing*_💻

          
       _*🌻🌻HAMDEEYERH🌻*_       

©️ *HIKIMA WRITER'S ASSO.🌻*
_Home of peace, joint of entertainment,to educate & to enlighten  our reader's._

   
_LITTAFIN KYAUTA._
*MALLAKAR*_ummie2018💜_
*oum muntaz*

_*marubuciyar*_

1- _AYSHAT(complted)_
2- _ZATOH(completed)_
3- _NUNA SO GABAN KISHIYA(completed)_
4- _TA'UMMU KA (incomplete)_
5- _NIGERIA KO NIGER(incomplete)_
6- _ANYA KUWA...?(rate book)_

     ~and now~

7- _HAMDEEYERH_

_GARGAD'I! GARGAD'I!GARGAD'I❌_

_Ban yarda wata ko wani yajuyamin sigar labari na ba,koda kuwa kalma dayace! duk wannan ya aikata hakan a gareni zamu gamu a fadar mai sama!!_

   *charpter 25*

************
5 MONTH LETTER************

Ayau aka tashi da rububin d'aurin auren nawwara,y'a mace ta fari gidan adamu kwangila...! wanda duk inda kashiga ka fita a unguwar gra dama fad'in garin kano kowa nada labari,tare da angonta abin alfaharinta abdulbasid yusuf mazigai,namji d'aya tamkar da dubu...!

        ******************

Komai yazama nomal t'sakanin gidan adamu kwangila da mahaifin marak'isiyyerh kamar ba'ayi ba an share komaiiii,wanda hakan yasa suka zama abokanai...!

amma kam dama har yanxu babu ita babu dalilinta tun wannan fitar tata daga gidan adamu kwangila,ga marak'isiyyerh da mahaifiyarta ta jawo mata bak'in jini gurin masoyinta abin alfaharinta sbd har yanxu bata ishe sa kallo bama ko kad'an ballanta a kai ga zancen wani soyayya sai cin mutunci dake biyo baya...!!

bata da mat'sala da komai yanxu,sbd zamanta ma yadawo k'ark'ashin kulawar mamami da bata rik'e siyyerh da abinda mahaifiyarta tamasu ba,kamar yadda take kula da y'ay'anta haka take kula da siyyerh tunda ansan ba laifinta bane,kuma itama yanxu wannan shaye shayen dukta wat'sar dasu,bata da mat'sala saina amma da marwan...!!

hajiya hamdeeyerh duniya sabuwa ta mata dad'i,bata da mat'salar komai,way'anda take tare dasuma masu mata bak'ar magana duk sun shige taitayinsu yanxu an koma kamar baya babu zancen shaye shaye...!

nawwara da abdul kamar zasu cinye junansu sbd soyayya,gakuma ya faruq da raihanatu suma ba'a barsu a baya ba wajen nunama junansu t'sant'sar soyayya...! hamdeeyerh kam dama bata da saurayi t'sawon rayuwarta wanda hakan kuma daga allah ne,kuma bai dameta ba ko kad'an sbd tasan koman daren dad'ewa allah na sane da ita...! hakan yasaka bata d'aga hankalinta ba...!
dangi na nesa da kusa duksun zo d'aurin aure..!

     ***********************

K'arfe biyu na ranar juma'a aka d'aura auren _NAWWARATU ADAMU KWANGILA DA ABDULBASID YUSUF MAZIGAI_ a k'ofar gidan adamu kwangila daya tara manyan k'asa na nesa dana kusa,wanda duk inda ka gilma zaka ga manyan motoci na alfarma ne dakuma manyan mu na k'asa masu fad'a aji...!

inda idona ya sauk'a kan ango abdulbasid dake t'sananin farin ciki,wanda idan baka masa farin sani bama bazaka fahimci hakan ba,sbd yadda yake miskilin namiji da wuya ka fahimci inda yasaka a gaba cikin al'amuransa,banda godiya ga allah babu abinda yakeyi cikin zuciyarsa...!

yana cikin bugaggagiyar shaddarsa k'irar gezna kalar milk,da akayi mata d'inkin manyan kaya dayasha aikin surfani mai kalar brown!!agogo da takalmi duk kamfanin _versace_ daya matuk'ar k'ara fiddo da ainahin k'irarsa ta maza masu jini a jika wanda yafara cin ganiyar k'uruciyarsa a halin yanxu da masu garin suke cikin rat'sa sa!

HAMDEEYERH!Where stories live. Discover now