part 8

42 6 0
                                    

_*Typing*_💻

          
       _*🌻🌻HAMDEEYERH🌻*_       

©️ *HIKIMA WRITER'S ASSO.🌻*
_Home of peace, joint of entertainment,to educate & to enlighten  our reader's._

   
_LITTAFIN KYAUTA._
*MALLAKAR*_ummien2018💜_

_*marubuciyar*_

1- _AYSHAT(complted)_

2- _ZATOH(completed)_

3- _NUNA SO GABAN KISHIYA(completed)_

4- _TA'UMMU KA (incomplete)_

5- _NIGERIA KO NIGER(incomplete)_

6- _ANYA KUWA...?(rate book)_

     ~and now~

7- _HAMDEEYERH_

_GARGAD'I! GARGAD'I!GARGAD'I❌_

_Ban yarda wata ko wani yajuyamin sigar labari na ba,koda kuwa kalma dayace! duk wannan ya aikata hakan a gareni zamu gamu a fadar mai sama!!_

_na sadaukar da wannan page din zuwa gareka abin alfahari na ~suleiman a abba~😍😍❤️❤️😘_

_wannan na gobe ne pa,sbd bazan hau online ba_

   *charpter 8*

_flash back_

a lokacin da hamdeeyerh taga antyn nata sun shige dakin operation din(kasancewar dama fakon fitar tata takeyi,saida ta lek'a ta hujin kofa ta tabbatar ta shiga),babu b'ata lokaci ta wawuri key na motar yayartata domin zuwa wajen da zata kwankwad'i barasa...!

chan wajen gari ta tafi,inda take kyautata zaton zata samu k'awar tata a chan,wato marak'isiyyerh,wacce sanadiyyar raka deeyerh datakeyi gidan giya itama taji tana sha'awar shanta,sannan kuma ta d'auki dabi'ar rawa a gidan giya ta yafama kanta k'arfi dayaji itama...

tana isa ko ta iske k'awar tata sai kwasan shoki takeyi,maza tangararru sai lik'i suke mata...!bata bi takanta ba ta bada order akawo mata giya,ba'a b'ata lokaci ba aka kawo mata kwalba daya kamar yadda tasaba!

a yunwace tafara shansa,wanda a baya bata iya shanyewa duka kwalba saita rage amma t'sabagen yadda yau tayi missing na abin t'sap ta shanye ta naimi k'ari,sukuwa masu saida abin sab'on allah suka k'ara kawo mata cikin jin dadii abinsu,sbd sukam dama gaba takaisu gobarar titi a jos!

bakowa ne kan iya sayar kalar wannan giyar ba sai wane da wane sabida t'sadarta,saida tasha ta bugu iya buguwa sosai kamin siyyerh ta sakko daga daga step na rawan bayan ta gaji, tazo gefen k'awar tata ta zauna itama ta shanye guntun da k'awar tata tarage,duk suka bugu...

anan suka fito suna had'a hanya abinsu,motar nawwara da hamdeeyerh tazo dashi suka fada suna lullumshe idanuwa alamun bacci nason d'aukarsu,

a haukace hamdeeyerh ta fisgi motar kamar wacce zata tashi sama ko kallon gabanta mai kyau batayi,sukayo cikin gari,duk motar dake wucewa kan kwalta saisun basu hanya...!

har takai ta kawo ma basusan inda kan motar take ba tsabagen yadda idanunsu yarufe,basu ankara ba wata sharbebebiyar motar daf tayi fillinging dasu akan wannan kwaltar...

aikuwa take mutane suka fara tururuwa a wajen dukda ma dare yayi amma babban gari kamar kano bazaka rasa mutane ba koda wani lokaci...!

kowaa salati yafarayi,wasu kuma dashike dakikai ne maimakon suyi tunanin ta yaddda zasu ceci rai sai suka fara vedio na abin a wayarsu,wanda wannan abin shi yazama ruwan dare gama duniya cikin al'umma...!

kowa ya gagara zuwa inda motar take,kawai sun zuba mawa motar ido suna kallon ganin yadda jini ke malalowa ta jikin motar,sun sare da lamarin...

wani dattijo ne magidanci dayake wurin yayi k'arfin halin k'arasawa cike da sanyin jiki,sbd ganin waya a yashe, dayake kyautata zaton daga cikin motar ya fad'o,cikin sa'a kuwa wayar babu security

call log na wayar yashiga,inda yayi arangama da last mutumin data kira wato bababi,(takirasa amma abin bai shiga ba a lokacin datake asibiti)...!

baiyi k'asa a gwiwa ba yayi dialling kuma cikin sa'a yashiga,inda yashaida ma bababi abinda yake faruwa dakuma inda accident din yafaru,wannan shine dalilin dayasa bababi cikin firgici...!

      _back to labari_

kallonsa sukeyi cikin tashin hankali a lokaci da yake shaida masu abinda aka shaida masa ta cikin wayar,ba k'aramin tashin hankali suka shiga ba,wanda hakan yayi sanadiyyar yankewar ga nawwara ta zube sumammiya...

bababi baibi takanta ba,yayi waje a kid'ime sbd tashin hankali,marwan ya dauki key na motar yabi bayansa tare da musa...

faruq na shirin bin bayansu mamami data wani kat'sa masa wata t'sawar da babu shiri yaci burki...

cikin kuka da tashin hankali tafara magana" yanzu kuna ganin yar uwarku anan cikin tashin hankali saiku t'sallaketa kutafi chan gurin wannan shashashar yarinyar data zab'a ma kanta rayuwar shaye shaye...? idan ubanku yayi rashin hankali yabiyema son zuciyarsa baibi takanta ba ku a cikin yan uwanta sai a rasa wanda zai t'saya daga gurintaa? wato idan ma mutuwa zatayi ba damuwarku bace idan yar gwal zata t'sira da tata rayuwar...?"tak'are maganar tana kukan takaici halin ko in kula da bababi ya nuna ga nawwara...!
  

cikin sanyin jiki faruq ya fara bata hakuri,sbd shima sai yanxu yaga rashin chanchantar abinda suka aikata baki dayansu...

t'sugunawa yayi cikin tausayin yayar tasa ta ciccib'eta,sbd dama bawani nauyin kirki bane da ita,kan 3seater ya shiimfid'eta,mamami takawo ruwan faro mai sanyi ta zuba mata a fuska,

ajiyar zuciya mai nauyi ta sauke,bayan komae yadawo mata k'wak'walwarta na abinda bababi yafada masu yasamu kanwara tata...

kuka tafasa ta mik'e a gaggauce daniyar sauka,saidae kuma taji an danne ta takoma,hakan ne ya k'ara daga mata hankali,inda ta fuskanci wanda ya danneta

faruq ne yarike ta cike da tausayin yayar tasa,

"dan allah faruq kasakeni naje naga halin da yar uwarmu take ciki...! accident fa akace tayi...?miyasa batajin magana ta ne? saida nace mata karta fita amma saida ta t'sallake magana ta tafita...!wannan masifar dame tayi kama ni nawwara...??" tak'are maganar tana kuka gwanin tausayi wanda duk wanda ya kalleta sai ya tausaya mata...!

"jarababbiya kawai...! ai saida nace ki fidda miji kiyi aure amma kin gagara kin t'saya ruwan ido! kina cusa kanki inda baki da kwarjini...! waike a dole mai yar uwa ko...? to wallahi idan baki fita daga idanuwana ba idan ranki yayi dubu sai ya baci! shashasha wacce batasan abinda yake mata ciwo ba...! kuma wlhi ko nan da k'ofar parlo nan kika taka k'adarki kika fice _allah ya isa ban yafe maki ba!_

mamami takare maganar cikin dakewar zuciya da t'sananin b'acin raiii...

batabi ta kansu ba dasuke mata kallon mamaki ta haye d'akin ta ta banko k'ofar!

kuka nawwara ta fashe dashi sosai ba kad'an ba wacce take hannun faruq har yanxu,shikuma sai bubbuga bayanta yake alamun lallashi

"faruq ka duba kaga halin ko'in kula da mamami ta nuna akan rabin rai...? wannan abu dame yayi kamane? ko bataji abinda akace yasamu yar autarta bane?"

"shiii!! karkice haka nawwara,ran mamami ne yab'aci sbd halin ko in kula da mahaifinmu damu kanmu muka nuna akanki!! shiysa kikaga tana reacting haka"fadar faruq kenan!

cikin mamaki ta fuskance sa bayan ta t'saida kukanta tace "akoi wani abinda yafaru ne yanxun?"

nan ya shaida mata duk abinda yafaru,jikinta ne yayi sanyi,allah sarki mahaifiya ashe dai duk a dalilinta ne ma ran mahaifiyarta ya b'aci har haka!
haka dai suka zauna jigum jigum suna jiran suji halin da ake ciki

_bangarensu bababi kam_

_~pls idan kina wattpad follow me @ummie2018 my sister,na canza wattpad babu followers,and pls yan wattpad amin voting haka zan gane soyayyata t'sakanina daku,ina ganin masu karantawa amma bana ganin voters~_

vote
comment
share

       _UMMIEN2018_💜

HAMDEEYERH!Where stories live. Discover now