part 21

39 6 2
                                    

_*Typing*_💻

          
       _*🌻🌻HAMDEEYERH🌻*_       

©️ *HIKIMA WRITER'S ASSO.🌻*
_Home of peace, joint of entertainment,to educate & to enlighten  our reader's._

   
_LITTAFIN KYAUTA._
*MALLAKAR*_ummie2018💜_
*💞oum muntaz💞*

_*marubuciyar*_

1- _AYSHAT(complted)_
2- _ZATOH(completed)_
3- _NUNA SO GABAN KISHIYA(completed)_
4- _TA'UMMU KA (incomplete)_
5- _NIGERIA KO NIGER(incomplete)_
6- _ANYA KUWA...?(rate book)_

     ~and now~

7- _HAMDEEYERH_

_GARGAD'I! GARGAD'I!GARGAD'I❌_

_Ban yarda wata ko wani yajuyamin sigar labari na ba,koda kuwa kalma dayace! duk wannan ya aikata hakan a gareni zamu gamu a fadar mai sama!!_

   *charpter 21*

4- _D'AN/Y'AR AUTA_  _wasu kuma dama soyayyar y'an auta daban yake dana sauran y'ay'an su cikin zuk'atan su,wanda idan ba'ayi da gaske ba,sai kuga yaro ya taso a sangarce ,yazamana yana shukama yayunsa rashin kunya iya son ransa amma kuma basu isa su zartar da hukunci ga wannan yaron ba sai iyayen sun d'auki mataki koma su d'auki fushi da dik wanda yayi yunk'urin tab'a d'an auta koda kuwa wannan autan ne da laifi,sai kaji ana cewa ai k'aramin yaro ne zuwa gaba zai daina,wasu iyayen ma har sukance yaron yarama dukan da yayan nasa yamasa,wanda hakan ba k'aramin gagarumar mats'ala yake haddasawa ba t'sakanin y'ay'a koda kuwa uwa d'aya uba d'aya ne(allah yasa mu dace)!!_

5- _MAMAN BABA/BABA,BABAN BABA/MAMA_  _hmmm wannan ma wata hanya ce dake kawo b'araka t'sakanin wa da kani ko kuma kanwa,sometimes kuma zaku ga idan d'aya daga cikin y'ay'a yazamana yaci sunan maman baba/mama ko kuma baban baba/mama,zaku ga yanayin soyayyar da iyayen ke nuna masa ya banbanta dana sauran y'an uwansa,kamar a cikin wannan gidan,na tabbata ba komai bane yasaka adamu nuna ma hamdeeyerh t'sant'sar k'auna saidan kasancewar ita taci sunan mahaifiyarsa daya rasa na shekaru da dama,kuma shi yana kallon hakan kamar ba wata matsala bace wanda ko hakan aikata babban kuskure ne!_

6- _MAI KUD'I_  _hmm anzo wajen,idan nace mai kud'i ina nufin d'aya daga cikin y'ay'anku ya fita zakka allah azurtasa da samun arziki fiye da sauran y'an uwansa,wanda haka zaisa shine yakan kyautata maku ta hanyar kautar kud'i,sutura,abinci da dai sauran buk'atunku nayau da kullum,wanda idan iyayen baku kai zuciya nnesa ba sai kuga kun fara hantarar sauran y'ay'an naku harma ku kanyi nasu gori wanda hakan zaisa saka masu burin samun kud'i kota wace hanya ce sbd suma ku yabe su kamar yadda kuka yabi d'an uwansu,wanda hakan shine the biggest mistake da uwa ko uba zaku aikata a rayuwarku muddin d'anku ya fad'a naiman kud'i koda kuwa ta wacce hanya ce!! danku kanyi iya zama gagarumin b'arawo ko kuma ince d'an fashi da makami,yakan iya zama dan cultism dukdan yasamu kud'in da shima zaku yabe sa kamar yaddda yaga kunayi ma yayansa ko k'aninsa,dama kuma already kun riga da kun raba kawunan y'ay'anku tun farko(allah yasa mu dace)_

7- _ILMI_ _wannan ma na d'aya daga cikin abinda iyaye mata har maza kan iya nuna wariya t'sakanin y'ay'ansu,kamar yanzu y'ay'an ka biyu ne kuma dukkansu mata,sai ya zamana d'ayar tafi d'ayar ilmi ko kuma fahimtar karatu a makaranta harma takanzo na d'aya,biyu ko uku idan akazo k'arshe zango(term),ita kuma wannan d'ayar kamin ta fahimta sai anyi dagaske wanda wani zubinma ko yaya za'ayi da ita bazata tab'a fahimtar wannan abinba sbd yanayin k'wak'walwarta da daidai fahimtarta a karatu! hakan sai kuga iyayen sukan sukan d'ayar da munana kalamai kamar doluwa,dak'ik'iya,mai k'wak'walwar kifi da dai sauran kalmomin da basu chanchanci ace sun jefi y'arsu ta cikin su da shi ba a gaban d'aya y'ar uwar tata mai k'ok'arin,a nan zakuga koda kuwa itace babba to kuwa tabbas gagarumin raini ne zai shiga t'sakaninsu wanda idan ba'ayi da gaske ba zazzafar k'iyayya ce zata gitta t'sakanin way'annan yara wanda kuma azo ana kokowa daga baya kuma anan ma laifin ba kowa bane saina iyaye,,,yabama goni yazama dole inji hausawa,amma fa sai asan ta yadda za'ayi a yabama gwanin batare da an bata wani gurin ba wajen neman gyara!_

wannan itace tak'ai tacciyar wasik'ata zuwa gareku allah yasa mu amfana koda kuwa da kalma d'aya ce cikin abinda na fad'a"

baba kamaye yakare maganar tasa yana mai zuba masu idanuwa ganin yadda duk jikin su yayi sanyi wanda hakan ke nuni da nasiharsa ya isa zuwa inda yake so!

hannu baka hannu k'warya zuka karb'i nasihar tasa sai godiya suke masa kuma kowa yayi realize na mistake nasa a wajen wanda a wannan ranar wannan family ji sukayi kamar an d'auke masu wani gagarumin dut'se mai nauyi daya tokare masu mak'oshin su! mamami ta naimi yafiyar kowa a wajen,kuma duk an yafe mata a take a wajen!


musa dama bisa rad'in kansa yake shaye shaye wanda a wannan ranar yama iyayensa alk'awarin ya dai har gaban abada kuma yanaimi alfarmar su saka shi cikkn addu'oinsu sbd naiman kariya daga fad'awa wata mummunar hanya!

bayan sunyi sallar la'asar baba kamaye,ya audu,abbu da marak'isiyyerh suka wuce gidan su siyyerh,kuma har zuwa wannan lokacin bata samu kallon arziki ba daga masoyin nata datake matik'ar so da zuciya d'aya,gashi kuma amma ma shuru babu wanda yaji d'uriyarta kuma babu wanda yayi jimamin ina ta tafi,a haka suka wuce unguwar rijiyar zaki!

gidan su mamami ma komai nml kamar babu abinda yafaru mamami,nawwara,hamdeeyerh,raihanatu mai aikinsu suka shiga kitchen sukayi masu lafiyayyar dinner na tuwon semo,miyar d'anyar kub'ewa da taji wadatacce naman rago! (my favorite ne wannan fa)!
magari ba suka kammala komai aka jera su a dining sukayi salla magriba aka deba ma su baba yusufa raihanatu ta tafi masu dashi wanda kullum daman hakan akeyi!

bayan sallar isha'i suka hallara baki d'ayansu cikin happy family harda su goggo sala sukaci dinner nasu gwanin sha'awa sai raha akeyi kamar babu abinda yafaru,hamdeeyerh kam na mak'ale da mamaminta da takeji bata da kamar ta a duniyar nan sai t'sokalarta ake tayi mamami na tare mata!

bayan sun kammala suka yada zango a parlo aka zauna kallon,kamar wanda aka hankad'a bababi yacanza masu tashar dasuke kallo wato zee world zuwa nta !! maganar da suka jiyo mai gabatar da program da wannan ranar keyine yamaido da hankalinsu kocokan zuwa garesu izuwa ga tv da wani kalar tashin hankalii sbd ganin kalar vedion da ake haskowa...!

bakwa min comment yadda yakamata yan group dina!!!
  
vote
comment
share

       _UMMIE2018_💜

HAMDEEYERH!Where stories live. Discover now