_*Typing*_💻
_*🌻🌻HAMDEEYERH🌻*_©️ *HIKIMA WRITER'S ASSO.🌻*
_Home of peace, joint of entertainment,to educate & to enlighten our reader's._
_LITTAFIN KYAUTA._
*MALLAKAR*_ummie2018💜_
*💞oum muntaz💞*_*marubuciyar*_
1- _AYSHAT(complted)_
2- _ZATOH(completed)_
3- _NUNA SO GABAN KISHIYA(completed)_
4- _TA'UMMU KA (incomplete)_
5- _NIGERIA KO NIGER(incomplete)_
6- _ANYA KUWA...?(rate book)_~and now~
7- _HAMDEEYERH_
_GARGAD'I! GARGAD'I!GARGAD'I❌_
_Ban yarda wata ko wani yajuyamin sigar labari na ba,koda kuwa kalma dayace! duk wannan ya aikata hakan a gareni zamu gamu a fadar mai sama!!_
*charpter 15*
banda kuka babu abinda mamami keyi bayan farfad'owar ta daga suman shock d'inda tashiga na ganin autan ta a bige cikin maye,bata tab'a jin t'sanar son zuciya kalar tata ba sai yau! wai dama haka duk uwa takeji a lokacin da akace mata yau y'arta ko d'an ta na aikata shan miyagun ruwar barasa ko kuma hayak'i domin gusar da hankali...?
kowa yasakata a gaba sai rarrashinta akeyi,hatta musa dake zaune yayi kalar tausayi domin ko ya dad'e da farfad'owa daga marisar tasa sanadiyyar ruwan lemon t'samin da goggo sala ta d'irka masa tun a lokacin da mamami ta sume wanda hakan ya taimaka wajen dawowarsa cikin hayyacinsa da gaggawa!
kowa tausayin mamami ne yake cin zuciyarsa a wajen ganin cikin y'ay'anta mafi soyuwa a zuciyarta na halin zuk'ar hayaki da kwank'wad'an giya!!
banda amma dake ta dariyar zuciya abinta,domin ko duk wannan abubuwan dake faruwa ba k'aramin dad'i yake mata ba,tunda har y'arta ma tana shaye shaye to uban kowa ma yasha ko a kwalar rigarta wlhi...!
saida aka k'ara nat'suwa kamin amma tafara magana kamar haka...
kamar yadda duk kuka sani,ni y'ar asalin garin kaduna ce,wacce muka taso mu mu biyu a hannun mahaifiyarmu,domin ko mahaifinmu ya dad'e da rasuwa tun kamin musan ma mai duniya take ciki...!
tun tasowata unguwarmu d'aya da adama(wato mamami),a cikin kaduna unguwar gomna road,aminai ne mu,irin wanda in akace aminau ana nufin aminai na amana da gaskiya dakuma rik'on amana!
mun taso kanmu had'e ne,koman mu kuma ya adamu(bababi)! yanaji da k'anwarsa dinnan kamar t'soka d'aya a miya wato mamami! wanda ni kuma baya nuna wannan kulawar a gareni ko kad'an,wanda hakan ba k'aramin sukar zuciyata yakeyi ba!
ba k'aramin k'aunar yaya adamu nake ba,har takai takawo na cisge kunya ta,ta y'ay'a mata da akasanmu dashi na furta masa cewa ina sonsa amma sam ya bad'awa idanunsa toka yace min bai san zancen ba!
domin ko shi akoi wacce yake dakon soyayyarta tun tana k'ank'anuwar yarinya,yanxu haka ma jiran lokacin da ya dace yakeyi ya amar mata da abinda ke cikin zuciyarsa,wanda hakan ba k'aramin bak'antamin zuciyata yayi ba! naci alwashin koma wacece wannan yarinyar indai ina raye, sai na d'au fansar kalaman da adamu yagayamin akanta koma wacece!
muna da 15yrs nida ita muka wayi gari wai an d'aura auren adamu da adama,wanda hakan yakawo cece kuce t'sakanin mariga alhaji musa(mahaifin mamami) da jama'ar gari,domin ko babu wanda yasan cewa adamu ba d'an inno nawwara bace na cikinta sai akan wannan auren da aka d'aura masa da adama!
nayi kuka k'warai a wannan lokacin sabida ba k'aramin so nakema ya adamu ba,amma babu yadda na iya,domin ko dana k'ara tunkararsa da batun soyayya ma cewa yayi da ya aureni gwanda ya auro tinkiya,wata k'ila zata fini daraja a idanunsa,sabida a mat'sayi na na d'iya mace dana fara furta masa kalmar soyayya bashi yafara fad'a man ba,wanda a tunaninsa wannan ma k'wakk'waran hujja ce da zai k'ini! sannan kuma ya shaidamin ba kowace yarinya bace yayi dakon soyayyar tata face adama(mamami)!
inaji ina gani aka shagulgulan biki na kece raini a cikin unguwar ya tare da amaryarsa,koda adama taji labari inason mijinta itama har gida tazo tamin kashe di na fita daga harkar mijinta idan ba haka ba komai ma kan iya faruwa t'sakaninmu!
hakuri na bata nace mata nama hak'ura dama tuntuni allah ya had'a kowa da rabonsa! hakan yasaka adama sararamin kasancewarta mace mai t'sananin kishin abinda takeso,haka mukaci gaba da k'awancenmu harma yafi nada,domin ko abu ko daidai dana second d'aya ne daya bata iya b'oye ma y'ar uwar ta!
sun k'auro garin kano unguwar rijiyar lemo wanda tare ya taho da inno da matarsa,nikuma ina kaduna,a haka har suka haifi d'an su nafarko aka saka masa suna marwan banyi aure ba kuma har zuwa wannan lokacin sbd ina tunanin wata k'ila zuwa gaba ya adamu zaiji tausayi na ya aureni ashe ni bansaan ma yariga da ya shafeni a bababin rayuwarsa ba!
saida adama tayi haihuwa hud'u da adamu na kawo masu ziyara wanda badan kowa ma iyo wannan tafiyar ba saidan t'sohon masoyi na adamu,wai ko allah zaisa ya saurareni yaji tausayina!
gidansa nafara sauk'a wanda adama ba k'aramin farin ciki tayi da zuwa na ba,sabida wannan amintar tamu ta da har yanxu tana nan bai canza zani ba a wurinta ammma banda ni,sabida ba k'aramin rik'on abinda adamu yayimin ata dalilinta ba cikin zuciyata! unguwar new gra wanda ko sati biyu basuyi da komawa ba alokacin!
amma haka na dake na nuna komai ba komai ba muka sha hirar yaushe gamo! abin takaici da kuma ya k'ara tunzurani izuwa d'aukar fansa ga ahalinsa,sai na nuna cewa da yayi bai gane ni ba! wanda na tabbata ba haka bane,sai dan rashin mutunci irin nasa daya sabayima emmata duk a ta dalilin son da yakema matarsa! kasancewarsa asalin cikakken bafilatani yasa mata dayawa ke mutuwa akansa tunda k'yakk'yawa ne ajin farko!
ana gobe zan tafi ne na had'u da wata k'yakk'yawar bafilatana a cikin gidan a mat'sayin sabuwar er aikin da aka kawo masu na sabon gidansu wanda kallo d'aya na mata na kissima abubuwa da dama cikin zuciyata game da ita,wacce na tambayi sunanta a gurin adama tacemin _DEEJAMA_ !!!
vote
comment
share_UMMIEN2018_💜
YOU ARE READING
HAMDEEYERH!
Historical Fictionlabari ne mai cike da sark'ak'iya,idan kuna bibiye da alkalamin ummie2018 zai warware maku zare da abawa