part 14

41 7 1
                                    

_*Typing*_💻

          
       _*🌻🌻HAMDEEYERH🌻*_       

©️ *HIKIMA WRITER'S ASSO.🌻*
_Home of peace, joint of entertainment,to educate & to enlighten  our reader's._

   
_LITTAFIN KYAUTA._
*MALLAKAR*_ummie2018💜_
*💞oum muntaz💞*

_*marubuciyar*_

1- _AYSHAT(complted)_
2- _ZATOH(completed)_
3- _NUNA SO GABAN KISHIYA(completed)_
4- _TA'UMMU KA (incomplete)_
5- _NIGERIA KO NIGER(incomplete)_
6- _ANYA KUWA...?(rate book)_

     ~and now~

7- _HAMDEEYERH_

_GARGAD'I! GARGAD'I!GARGAD'I❌_

_Ban yarda wata ko wani yajuyamin sigar labari na ba,koda kuwa kalma dayace! duk wannan ya aikata hakan a gareni zamu gamu a fadar mai sama!!_

   *charpter 14*

Zirga zirgan da mamami keyi a gidanta duk wanda yagani yasan bana lafiya bane,takasa zaune takasa t'saye,nawwara kam dakanta ke duhu,allah allah take domin ko duk wannan bad'akalar da akeyi  tana so a sallamo su hamdeeyerh domin taji kan zare da abawa!

kamar daga sama sukaji sallamar da inna ta doka, wanda ahalin gidan kama daga y'an aiki da y'an gida duk suka firfito parlon domin taryan bak'i tunda dama ansan da cewa yau za'a sallamo su daga asibiti,kowa barka yake masu da fatan samun lafiya d'aurarriya!

nawwara kam baki har kunne ganin y'ar uwar tata na tafiya da k'afafunta,kamar batayi wani ciwo ba,domin ko idan ba fatar jikinta aka gani ba baza'a ce,ita tayi wannan accident din ba,kasancewar yadda fatar tata tabon accident din basu gama gushewa ba!

cike ta farin ciki da rungumo y'ar uwar tata,wanda sukayi ta murnar ganin junansu,mamami dakanta ke k'asa tanata addu'ar samu sassauci akan komai!

"sannunku da zuwa goggo" fad'ar faruq da shigowarsa cikin parlon kenan,wanda hakan yaja hankalin mutanen parlon baki d'aya zuwa kansa,

cike da t'sokala inna dake k'ok'arin zama kan d'aya daga cikin lunt'suma lunt'sumar kujerun dake cikin parlon na alfarma tace "yawwa gauro mara iyali,duk da ma bani aka cema sannu da zuwa ba"

wanda hakan yasaka mutanen cikin parlon darawa baki d'ayansu,cikin k'arfin hali da murmushin yak'e mamami tafara masu maraba da zuwa nanko aka zauna aka k'ara jajantawa masu jiki,marak'isiyyerh na jikin uwarta itama!

hamdeeyerh kam zubama mamami ido kawai tayi tana kallonta,wani abu mai kama da k'wallon goruba ya tokare mata mak'oshi,sabida takaicin halin ko in kula da mahaifiyar tata ke nunawa a kanta data fad'a halin rashin lafiya,dukda ma dai tasan ko wani kalar reaction mahaifiyar tata,ta nuna akan ta ita ta janyo ma kanta!

idan tayi la'akari da yadda a kullum wayewar gari na duniya saita mata nasiha kan halin shaye shaye,gakuma kullum tana cikin kuka da hawaye duka a ta dalilinta,ita a nata fahimtar ai wannan ba k'wakk'waran hujja bace da zaisa mamami tak'i zuwa duba lafiyarta a asibiti sai sau d'aya tak! a zaman da tayi a asibiti na t'sahon sati uku da kwana biyar,duk kalar soyayyar datake nuna mata!

zunguro ta da nawwara tayi ne yadawo da ita cikin hankalinta,inda ta fuskance ta,sai a lokacin ta lura  ma su biyu ne cikin parlon duk an wat'se an barsu!

"anty na! yanxu har laifin danayi ma mamami yakai ace ta d'auke kanta a kaina batare da ta nuna murnar dawowata gida ba...? kuma bacin k'in zama datayi dani a yayin danake jinya, murnar dawowata ma cikin koshin lafiya bazatayi ba...?_ANYA KUWA ...?_ mamami tana sona kamar da anty? ji nake kamar an canzamin mahaifiyata dana san mai k'aunatace a duk halin dana t'sinci kaina,zuciyata tanamin zafi sos......" kasa k'arasa maganar tata tayi sabida yanda kuka yaci k'arfinta, wanda allah ne kad'ai yasan rad'ad'inda takeji cikin mak'wallaton wuyanta,gakuma wani kallo dataga ni a fuskar antyn nata mai kama da _KE KIKA JAWO MA KANKI_

cikin kuka taci gaba da magana "anty na ki taimaki rayuwata,bana son fushin mahaifiya ta akaina,laifukan zasumin yawa,ina da laifi a gurin ubangiji na wanda bani da tabbacin dalilin dayasa nake aikata shaye shaye daya kasance ba halin mutanen kirki bane,..." tak'are maganar tana mai k'ara t'sananta kukan nata t'sakani da allah,wanda hakan yasaka nawwara rungumuta a jiki tana lallashinta kamar itama zatayi kukan!

saida ta tabbatar da tayi shuru kana tace "abinda nake so dake yanxu,ki tashi muje muyi sallah,bayan mun idar saiki je d'akin mamami ki bata hakuri kuma ki tabbatar mata bazaki sake aikata abinda bata so ba! idan kikayi hakan nima namaki alk'awarin zan tayaki bata hak'uri har mu tabbatar da cewa ta hakura,amma fa bazan bata hak'urin ba,har sai kin tabbatarmin da cewa bazaki k'ara aikata halin mutane marasa kamun kai ba!"

nawwara tak'are maganar tana mai kafe ta da idanuwa,anan dai suka gama alk'awarirrikansu t'sakaninsu kana suka mik'e zuwa d'akin hamdeeyerh dake down stairs na cikin parlon nasu!

bayan sun idar da sallar azahar suka fito parlo,inda suka tarda mamami,amma,inna,goggo,siyyerh,ya faruq,ya marwan da dawowarsu kenan daga masallaci! sun fara lunch,dan haka suma suka jona su bayan an gama aka zauna zaman hira t'sakaninsu,wanda duk ya ta'allak'a ne akan jinyar su hamdeeyerh,sai nasiha su goggo suke masu!

suna cikin hira sukaji sallamar da bababi yayo daga bakin k'ofar shiga parlon,saida suka kikkint'sa kana aka basu iznin shigowa,tare yake da abbu wato mahaifin siyyerh da wasu maza daga bangaren abbun!

wat'sewa akayi aka barsu sukayi lunch suma,bayan sun kammala raihanatu tazo ta tattara kayan zuwa kitchen,bayan tagama ta wuce b'angaren iyayenta itama!

bababi,mamami,ya marwan,nawwara,ya faruq,hamdeeyerh,goggo,inna, amma,abbu,ya audu(yayan amma),baba kamaye(yayan abbu),marak'isiyyerh!

gabaki d'ayansu sun had'u domin maganar da amma tace zatayi da kowannensu,amma babu musa babu dalilinsa,wanda rabon dasu saka shi a ido tun dare jiya!

saidaa aka nat'su fes kamin amma ta bud'e baki zatayi magana,aka hankad'o labulen shigowa parlon a hargits'se,wanda ba kowa bane sai musa daya shigo cikin yanayi na cikakkan d'an k'waya,domin ko a buge yashigo wanda haka yasaka ahalin mik'ewa cikin kid'ima da tashin hankali!

mamami data zunduma wani uban ihu sai gata a k'asa warwas ta zube sumammiya,amma kam wani kalar dariya data fashe dashi saida ya bama kowa mamaki!

idan kika karanta kimin share nasa plsssssssssssssss

    
yan wattpad kumin voting idan kuka karanta dan allah!

yan group dina bakwamin comment why nerh...?
  
vote
comment
share

       _UMMIEN2018_💜

HAMDEEYERH!Where stories live. Discover now