part 12

39 6 2
                                    

_*Typing*_💻

          
       _*🌻🌻HAMDEEYERH🌻*_       

©️ *HIKIMA WRITER'S ASSO.🌻*
_Home of peace, joint of entertainment,to educate & to enlighten  our reader's._

   
_LITTAFIN KYAUTA._
*MALLAKAR*_ummien2018💜_

_*marubuciyar*_

1- _AYSHAT(complted)_

2- _ZATOH(completed)_

3- _NUNA SO GABAN KISHIYA(completed)_

4- _TA'UMMU KA (incomplete)_

5- _NIGERIA KO NIGER(incomplete)_

6- _ANYA KUWA...?(rate book)_

     ~and now~

7- _HAMDEEYERH_

_GARGAD'I! GARGAD'I!GARGAD'I❌_

_Ban yarda wata ko wani yajuyamin sigar labari na ba,koda kuwa kalma dayace! duk wannan ya aikata hakan a gareni zamu gamu a fadar mai sama!!_

_na sadaukar da shafinnan ga marubutan k'ungiyar hikimta,d'aya tamkar da dubu_

   *charpter 12*

    

isarsu asibitin ma sun tarda iyalan su siyyerh dasuka buga sammako domin gaisuwar mara lafiya,wasun ma badan allah fa suka zo ba? sunzo ne kawai sbd son abin duniya,domin ko muddin yayan maras karfin cikinsu ne aka wayi gari babu lafiya ba lallai ne suzo ba! saida subada uziri su wani nado 2k su aiko,su a tunaninsu kud'insu ne ladan duba mara lafiya bawai zuwan nasu ba!

har zuwa wannan lokacin babu wacce tafarka cikinsu,bakaramin tausaya masu mutane da dama sukayi ba,sai yanxu da hankalin bababi yadawo garesa kana komai da ake fad'a akan yartasa da kawarta yadawo masa k'wak'walwarsa!

wato wai akan hanyar dawowarsu daga gidan giya wannan kaddarar ta rufta dasu...? wannan masifar da mai tayi kama...? ba fata yakeyi ba idan yanxu wannan accident din nasu yazo da ajalinsu zuwa lahira mai zasu je sucewa ubangijinsu...? domin ko shan barasa na daya daga cikin abinda allah ya haramtawa duk wani mumini amma sai gashi wai ashe acikin gidansa ma akoi mai aikatawa!

wanda duk inda mutum yashiga a fadin garin kano zakaji ana cewa yar gidan _alhaji adamu kwangila_ tayi accident akan hanyarta ta dawowa daga gidan giya? wasu ma dasuke jin haushinsa kance allah ya kara!!

ta inda allah ya takaita abinma asibitin na yarsa ne,babu wanda yake da damar zaginsu cikin asibitin!

a nan dai suka wuni cikin asibitin goggo salamatu da inna luba suka zauna sauran kuma a ranar suka koma garin nasu na misau!

wajen k'arfe shabiyu na dare zuwa lokacin masu kwana ne a asibitin kawai suka rage,bababi,ya marwan,faruq,musa da abdulbasid duk sun wuce gida,goggo sala da inna luba ne kawai suke nan,wanda badan sunyi dagaske bama yau bababi yace shi zayyi jinyar yarsa,sbd yana da bukatar mata wasu yan tambayoyi da zarar ta farka!

suko rashin cancantar haka dasuka gani ne yasa su kada sa dan dole,domin ko inna luba a matsayin yaya take a gurin bababi itama,yar gidan yayan marigayi marwan ce itama,kenan yan maza biyu ne ita da shi!

bangaren iyayen marak'isyyerh mahaifiyarta dakuma wata yar uwarsu ne suka kwana da ita,

sha biyun dare dai dai hamdeeyerh ta farko daga alluran baccin da aka zurmuk'a mata,wanda hakan ba karamin farin ciki su goggo sala suka shiga ba!

basu bata lokaci ba wajen kiran likita,yazo yayi mata aune aune,kuma komai alhmdlh an dace kamar yadda ake fata,karaya guda biyu ne jikin hamdeeyerh,kafarta daya dakuma hannunta wanda aka dakko mai gyara dazai gyarata da zaran ta farka!

siyyerh kam alhmdlh babu karaya saidai buguwa ne da tayi amma babu karaya!

godiya sukayi ga allah amma basu kira gida ba,sanin dasukayi cewa tunanin bababi kadannne(🙊🙉)

babu jimawa siyyerh ma tafarka,wanda hakan ba karamin dadi yayiwa mahaifiyartata ba amma babu halin a rukunkumesu a bisa umarnin doctor!

hamdeeyerh idanunta a lumshe yake hawayen na gangarowa wani na koran wani,sbd yadda takejin fatar jikinta kamar ana hura mata wuta dan tsananin azaba! zafin da takeji kuma ya wuce misali

gashi wani kalar kishi takeji kuma masu karatu karkuyi tunanin na ruwa fa! barasa take bukata tasha domin ko dukda bata hayyacinta tasan a kwance tayi ni batare da tasha ba!

lallashinta kawai suke tayi,domin ko sun tabbatar kukan nata bana lafiya bace,itako idan banda tsine masu babu abinda takeyi cikin zuciyarta! ta tabbata da ace basa gurin babu abinda zai hana ta tashi ta tafi koda kuwa uban ciwo ne a jikinta!

ganin hakannne yasa suka saka likita zurmuka mata allurar bacci amma ba wanda zaisa tayi 24hrs ba!hakan ko akayi babu bata lokaci takoma baccinta

wanda duk abinda yake faruwa kab idanuwan amma ne wato mahaifiyar siyyerh! wani abune yatokare mata a makoshi,wanda haka yasa hawayen fara zirya bisa kuncinta wanda nagaza fassara maku shi!

dauke kanta tayi daga garesu domin hana kowa fuskantar yanayin datake ciki ta fuskanci yar tata datake ta sauke ajiyar zuciya wanda lumfashinta ma dakyar yake fita!

karfe bakwai na safe yamawa bababi da ya marwan a asibitin,wanda zuwa wannan lokacin hamdeeyerh tafarka,kuka take tasha bilhakki ita abarta ta tafi gidan giya amma kuma sun hanata,ma'aikatan asibitin kam mamakin hali irin nata sukeyi!

alokacin datake ta zunduma uban ihu suka iso wanda tun daga bakin reception bababi ke jiyo kukan yar tasa,a sukwane ya karasa shiegewa kuwa!

pls ayi manage babu yawa!
  
vote
comment
share

       _UMMIEN2018_💜

HAMDEEYERH!Where stories live. Discover now