_*Typing*_💻
_*🌻🌻HAMDEEYERH🌻*_©️ *HIKIMA WRITER'S ASSO.🌻*
_Home of peace, joint of entertainment,to educate & to enlighten our reader's._
_LITTAFIN KYAUTA._
*MALLAKAR*_ummie2018💜_
*💞oum muntaz💞*_*marubuciyar*_
1- _AYSHAT(complted)_
2- _ZATOH(completed)_
3- _NUNA SO GABAN KISHIYA(completed)_
4- _TA'UMMU KA (incomplete)_
5- _NIGERIA KO NIGER(incomplete)_
6- _ANYA KUWA...?(rate book)_~and now~
7- _HAMDEEYERH_
_GARGAD'I! GARGAD'I!GARGAD'I❌_
_Ban yarda wata ko wani yajuyamin sigar labari na ba,koda kuwa kalma dayace! duk wannan ya aikata hakan a gareni zamu gamu a fadar mai sama!!_
_i dedicated the whole this book to all writer's of hikima writers association🌻_
*charpter 22*
" *Labari da d'umi d'uminsu...!! a yau ne muka samu wani t'sohon vedio na shahararren d'an kwangilar nan dayayi fice ya shahara a k'asar mu ta nigeria dama wasu k'asashen mu waje,wato ALHAJI ADAMU KWANGILA na aikata alfasha da y'ar aikin gidansa ta hanyar nuna mata k'arfin ikonsa akanta wanda hakan yayi sanadiyyar dayasa tasamu ciki,kuma garin haihuwa allah ya ansa abarsa batare da tayi tozali da d'aya daga cikin danginta ba! kuma ba kowa bace wannan yarinyar da aka haifa face wata fitinanniyar yarinya da kowa yasan ta a garin sbd shan ruwan barasa data maida sa ba'a bakin komai ba! ga k'adan daga cikin k'wakk'warar shedar da muke da shi wanda zaku kalla kai t'saye daga wannan gida ta talabijin"*
mai bada labaran ne yaja fasali da zance nasa inda aka hasko fuskar bababi b'aro b'aro cikin akwati nan talabijin suna kokawa da marigayiya deejama a lokacin da yake k'ok'arin aika aikar,wanda ga fuskarta nan ma tar a lokacin! wanda da k'yar yasamu yaci galaba akanta ya haye ruwan cikin ta dif aka dakatar da vedion!
wanda hakan yasaka duk mahaluk'in dake kallon talabijin a wannan lokacin ya jik'e sharkaf da zuba da kuma t'sant'sar tashin hankali...!!
bababi kam tun a lokacin da yayi arangama da abin ya daskare a gurin sbd t'sant'sar shock na tashin hankalin abinda yayi tozali da shi,tabbas a wannan vedio din ba k'arya bane ba,shi d'inne for d first time da zai fara sex da y'ar aikin nasa! hamdeeyerh kam tun lokacin da aka hasko fuskar mahaifinnata na kokawa wacce aka kira da mahaifiyarta ta sume a gurin batare da kowa ya ankare ba!
nawwara kukan da take sharb'a allah ne kad'ai yasani,gasu gwaggo kam banda salati babu abinda sukeyi sbd ganin wannan aika aika b'aro b'aro bama kamar inna! marwan,faruq da musa ma ba abarsu a baya ba,bama kamar ya marwan dayasan babu wanda zayyi wannan aika aika idan ba amma ba,wanda kuma yaci alwashin saiya koya mata hankali idonta idonsa wanda ya tabbata abin bazai masu da kyau ba!!
mamami ma kukan takeyi kawai sbd wannan abin na naiman fin k'arfinta,idan ka kalle wannan a halin a daidai lokacin saika tausaya masu ko kai ka kawo rashin imani,gwani ban tausayi!
kamin kowa yasamu zarafin magana sukaga an bankad'o k'ofar d'akin da k'arfin gaske kamar za'a balle masu k'ofar wand hakan yasaka su farkowa daga suman wucin gad'in dasukayi,baba yusufa ne ya shigo cikin tashin hankali wanda kana hani zaka san a mugun kid'ime yake,yana shigowa bai wata wata ba ya tinkari adamu kwangila yana zuwa yayi masa wani mugun shak'a a wajen yana ta muzuraii!
wanda hakan yasaka kowa mik'ewa cike da mamaki da kuma shock na abinda yake faruwa a cikin gidan! faruq ne a zuciye ya mik'e ganin yadda mahaifin nasu ke fidda numfarfashi a wajen,gashi kuma yak'i karb'an kansa daga hannun wannan villeger d'in!
YOU ARE READING
HAMDEEYERH!
Historical Fictionlabari ne mai cike da sark'ak'iya,idan kuna bibiye da alkalamin ummie2018 zai warware maku zare da abawa