_*Typing*_💻
_*🌻🌻HAMDEEYERH🌻*_©️ *HIKIMA WRITER'S ASSO.🌻*
_Home of peace, joint of entertainment,to educate & to enlighten our reader's._
_LITTAFIN KYAUTA._
*MALLAKAR*_ummien2018💜__*marubuciyar*_
1- _AYSHAT(complted)_
2- _ZATOH(completed)_
3- _NUNA SO GABAN KISHIYA(completed)_
4- _TA'UMMU KA (incomplete)_
5- _NIGERIA KO NIGER(incomplete)_
6- _ANYA KUWA...?(rate book)_
~and now~
7- _HAMDEEYERH_
_GARGAD'I! GARGAD'I!GARGAD'I❌_
_Ban yarda wata ko wani yajuyamin sigar labari na ba,koda kuwa kalma dayace! duk wannan ya aikata hakan a gareni zamu gamu a fadar mai sama!!_
_i dedicated the whole this book to all writer's of hikima writers association,k'ungiya d'aya tamakar da dubu🌻_
*charpter 10*
_Akoi way'anda suka son aci gaba da rubuta littafin ta'ummu ka!dan allah kubani lokaci na kammala wannan dana fara,idan yaso sai na maku ta'ummu kan,idan ba haka ba kuma sam bazan natsu na maku abin kirki ba a halin yanxu idan kukace sai anyi,sbd uzurirrika dasukamin yawa_
saida abdulbasid yayi wanka yacanza kaya kana ya shiga ainahin cikin gidannan!!
inda ya yadda nawwara da faruq zaune kan kujeru sunyi jigum jigum gwanin ban tausayi,suna ta t'sumayin jiran sakamakon halin da ake ciki,
a hanzarce duk suka mik'e jin an danna k'ararrawar sanarwa alamun akoi bak'o a waje!
faruq ne ya bude masa bayan ya shigo ciki suka tarkesa da tambayar halin da ake ciki? sbd faruq mamami bata masa iyaka da fita waje ba,hakan yasa yaje ya tambayi baba mai gadi kuma yashaida masa yadda ta kasance iya kacin abinda yasani!
hankalinsu ya tashi jin abinda yafaru,banda maimaita kalmar innalillahi wa'inna ilaihir raji'un,babu abin nawwara keyi cikin tashin hankali! faruq ma k'arfin hali kawai yakeyi,domin ko abin ya girgiza sa!! inda ya shiga d'akin bababi dake makwaftaka da dakin mamami domin dakko abinda zasu bukata ta fannin sutura!
k'arar kofar da mamami tajine yasakata fitowa daga bedroom nata idanunta yayi jajazur luhu luhu,alamun taci kuka ta k'oshi! sbd tunda tashiga daki take ta rusan kuka kamar wacce aka cema rabin rai ta mutu!
daga k'arshe ma wayarta ta dauka tanata trying na wani number amma is not reachable yake ce mata!
hakan yasakata ci gaba da sharb'an kukanta,kamar babu gobe! abubuwa da dama take kisimawa cikin ranta! a haka ta bud'e bedside drower nata ta fito da wani magani na tablet,kuma a dai dai wannan lokaci taji k'arar k'ofar d'akin bababi hakan yasakata fitowa domin ta gane ma kanta abinda yake tafiya!
ganinta yasaka abdul risinawa yakwashi gaisuwa a wajenta,inda ya jajanta mata abinda ya tunkaro rayuwar yar tasu,anan ne yake shaida masu ai ba ita kad'ai bace ma abin yafaru da ita,harda k'awar ta wato marak'isiyyerh,sbd yagane ta itama dukda ciwukan da ya dabaibaye mata fuskarta itama!
zuciyar mamami sai kai kawo takeyi ciikin zullumi da tashin hankalin jin abinda abdul ya shaida mata,fitowar faruq ne ya kat'se masu jajanta abin dasukeyi a t'sakaninsu,itama mik'ewa tayi zuwa kitchen ta dakko flast na ruwan zafi da basa rabuwa dashi har guda biyu,tare da babban gwangwami na madara da milo,da kwalin sugar,cups n spoon da duk wasu abubuwan daya kamata ayi jinyar mara lafiya saida ta had'o masu!
nawwara kuma ta kwaso masu darduma na kafet domin gabatar da salloliinsu,kai duk abinda kukasan mutum mai jinyar majinyaci dakuma majinyacin zai buk'ata saida suka harhad'a masu faruq yatayasa zubasu cikin motar,
nawwara nada shirin binsu,amma kuma kallon yanayin hararar da mamami ta antaya mata yasakata samin waje tana sharar k'walla gwanin ban tausayi!
faruq da abdul sukayi ma su baba sallama a cikin wannan daren suka wuce asibitin...!
mik'ewa mamami tayi ta dakko ruwan faro mara sanyi tazo takama hannun nawwara batare da tayi magana ba,ganin hakan yasaka bin bayanta batayi musu ba itama,
bedroom na mamami suka shiga,zama sukayi bakin gado inda ta umarci nawwara data shiga ta wat'sa ruwa,bayan sun kammala shirin bacci duk zuciyoyinsu babu dad'i,tausayin nawwara na nuk'urk'usar zuciyar mamami amma a wajenta hakan da tayi shine daidaiiii!
gado d'aya suka kwanta,kamar karamar yarinya haka nawwara ta shige jikin mahaifiyar tata tana ta sauke ajiyar zuciya,sam bacci ya gagari idanunsu,ganin hakanne yasaka mamami kudirta niyyarta ta farko!
ruwa da wannan tablet din ta b'allla tasama nawwara a baki,batayi gardama ba ta kwankwad'a,itama tasha,kana suka k'ara kwanciya,cikin minti goma shabiyar wani nannauyan bacci yayi gaba dasu!
――――――――――――――
zarya suke tayi baki d'ayansu,sun rasa mai yake masu dadi gaba d'aya,sbd jin shurun likitocin kimanin 4 houra kenan da shigarsu,zuwa wannan lokacin kuma tuni su faruq sun iso tare da iyayen marak'isiyyerh dasuka je sanar masu abinda yafaru,wanda hankalinsu ba k'aramin tashi yayi ba jin abinda yafaru da yar tasu k'wallin k'wal ta duniya,wacce suka d'auki soyayyar duniya suka d'aura mata,ko bacci zasuyi sai sun kaita har d'akinta sun tabbatar da baccin nata yayi nisa kamin su barota sbd gata,nanko basu san y'ar tasu a baibai yake ninke su ba,ballanta susan ainahin kalarta!! mahaifiyar ta k'awar mamami ce ta k'ud da k'ud,idan nace maku k'awaye ina nufin aminai da d'aya bata aikata abu idan ba da sanin y'ar uwarta ba,kuma duk a ta sanadiyyar k'awancen hamdeeyerh da marak'isiyyerh suka san junansu,mahaifin siyyerh babban mai kud'i ne shima na bugawa a jarida!
tare suka iso asibitin da iyayen yarinyar,sai kuka amma take tayi wato mahaifiyar siyyerh,dataji ance tare da deeyerh sukayi accident din,ita mamaki ma takeyi ta yadda suka had'u a wannan daren tare har k'addarar nan ta rufta masu,ga wasu surutai maras kan gano datake ta jerowa!!
sunanan sunyi abin tausayi sunata t'simayin fitowar likitocin aka k'ira sallah asubahi! akoi daya daga cikin ma'aikatan hamdeeyerh mai suna lubabatu wacce itace amintacciyar nawwara a asibitin ta bud'e masu office na nawwaran sbd akoi key itama a hannunta!
bababi ne yafara shiga bayin yayi wanka yafito bayan ya d'auro alwala,ya dakko jallabiya ya zura,sai abbu wato baban marak'isiyyerh shima ya dauro alwala yana fitowa suka fice tare da bababi zuwa masallacin cikin asibitin!
marwan,abdul da musa suma suka t'saftace jikinsu sukabi bayan iyayen nasu,kana maman siyyerh itama tayi alwaala tayi sallarta a cikin office din! itadai addu'arta da fatan ta allah ya tashi kafad'ar y'artata,addu'ar da take tayi kenan!
wajen na safe su bababi suka daqa daga masallaci a lokacin kuma amma ma tana bakin emergency!
zuwansu yayi daidai da fitowar wani likita da sai share zufa yakeyi,alamun dai a gajiye yake tulus...!!
duk kansa sukayi a hargit'se suna tambayarsa halin da ake ciki...?
pls don't forget to
vote
comment
share
follow me on wattpad @ ummie2018_UMMIEN2018_💜
YOU ARE READING
HAMDEEYERH!
Historical Fictionlabari ne mai cike da sark'ak'iya,idan kuna bibiye da alkalamin ummie2018 zai warware maku zare da abawa