_*Typing*_💻
_*🌻🌻HAMDEEYERH🌻*_©️ *HIKIMA WRITER'S ASSO.🌻*
_Home of peace, joint of entertainment,to educate & to enlighten our reader's._
_LITTAFIN KYAUTA._
*MALLAKAR*_ummie2018💜_
*oum muntaz*_*marubuciyar*_
1- _AYSHAT(complted)_
2- _ZATOH(completed)_
3- _NUNA SO GABAN KISHIYA(completed)_
4- _TA'UMMU KA (incomplete)_
5- _NIGERIA KO NIGER(incomplete)_
6- _ANYA KUWA...?(rate book)_~and now~
7- _HAMDEEYERH_
_GARGAD'I! GARGAD'I!GARGAD'I❌_
_Ban yarda wata ko wani yajuyamin sigar labari na ba,koda kuwa kalma dayace! duk wannan ya aikata hakan a gareni zamu gamu a fadar mai sama!!_
*charpter 28*********Haka nan kawai taji zuciyarta ta gagara nat'suwa guri d'aya hankalinta yayi gida gashi gabanta sai faman lugude yakeyi!
ganin yadda tafara yin kwab'a a aikinne d'aya daga cikin likitocin tace "doctor ki tafi gidama kawai tunda munci k'arfin aikin bari doctor faysal yakaiki gida,naga kamar bak'yajin dad'i"
aikuwa kamar jira take tace hakan ba yamata,dacta faysal na shigowa babu b'ata lokaci ta had'a jakanta da kwamut'santa...! har k'ofar gida ya ajiyeta,mai gadi da idanunsa biyu zuwa wannan lokacin tunda ko goma ma batayi ba yamata sannu da zuwa ta dunfari cikin gidan zuciyarta sai bugawa yakeyi!
tana shiga cikin parlon kukan umaiman ta ne yafara mata welcome kamar wacce ake zarema rai haka yarinya keta cancara ihu,a sukwane ta wuce d'akin inda ta d'auki yar tata tafara lallashinta,tayi tunanin hamdeeyerh na toilet,saida ta tabbatar da umaima ta koma bacci kamin ta mike ta rage kayan jikinta amma shuru har yanxu bataga billowar hamdeeyerh ba!
tura k'ofar toilet tayi nanma shuru babu alamun hamdeeyerh,sai tayi tunanin kotana d'akinta ne tan wani uzirin,wanka tayi ta shirya cikin kayan bacci baya ta feshe jikinta da turare mai dad'in kamshi ta tin kari turakar mijinta!
tun daga bakin k'ofa tafara jin wani kalar nishin mijin nata wanda zata iya rant'sewa idan ba sex yakeyi da ita ba bata tab'a jin kalar wannan nishi da gurnanin!
zuciyarta na bugawa ta tura k'ofar d'akin,abinda tagani ne ya matuk'ar girgiza mata tunaninta ,yakuma d'aga mata hankali ta gagara ma magana sai nuna su kawai take da hannu,numfashinta na kai kawo kamar zata t'saga k'irjinta ta fito amma ta gaxa furta koda kalma d'aya ne!
sannan kuma ta gagara d'auke idanunta akansu saima wani uban tagumi data zuba hannu bibbiyu kamar doluwa tana kallonsu,hawaye na malalar ambaliya bisa ga fuskarta!
wai k'anwarta dasuke uba d'aya ce wannan suke aikata alfasha t'sakaninta mijinta ko kuwa dai wata ce daban ba hamdeeyerhn ta data sani bace wannan...?
sannan k'anwar tata bada kowa ba saii mijinta data mik'a masa kula da ragamar zuciyarta baki d'aya...? wannan masifa dame tayi kama dan allah?
"shin wai wannan abdulbasid miji na ne kuma mahaifin umaima ke lalata da k'anwata ta jini..." wannan shine maganar da nawwara keyi cikin zuciyarta batare da tasan cewa a fili ta aikata hakan ba...!
wanda a daidai wannan lokacin abdul yagama samun nat'suwarsa,wanda wannan kalmar da nawaara tayi har cikin k'ok'on k'wak'walwarsa,kamin yagama tantance wa yaji wani uban tarin da nawwara keyi wanda babu tantama tabbas ita d'ince sbd had'a idanuwa dasukayi...!
jini ne ta baki ta hanci ga kuma ta k'asanta yake malala sbd t'sananin tashin hankali! a wani kalar mugun razane abdulbasid ya diro daga kan gado ya rarumo jallabiya ya zura ko boxes bai saba ya sungumi nawwara daketa uban tari sai jini dake t'sartowa...! a 360 ya fice daga gidan da ita zuwa asibiti,cikin minti 6 suka iso!
YOU ARE READING
HAMDEEYERH!
Historical Fictionlabari ne mai cike da sark'ak'iya,idan kuna bibiye da alkalamin ummie2018 zai warware maku zare da abawa