part 5

73 7 2
                                    

_*Typing*_💻


_*🌻🌻HAMDEEYERH🌻*_

©️ *HIKIMA WRITER'S ASSO.🌻*
_Home of peace, joint of entertainment,to educate & to enlighten our reader's._


_LITTAFIN KYAUTA._
*MALLAKAR*_ummie2018💜_

_*marubuciyar*_

1- _AYSHAT(complted)_

2- _ZATOH(completed)_

3- _NUNA SO GABAN KISHIYA(completed)_

4- _TA'UMMU KA (incomplete)_

5- _NIGERIA KO NIGER(incomplete)_

6- _ANYA KUWA...?(rate book)_

~and now~

7- _HAMDEEYERH_

_GARGAD'I! GARGAD'I!GARGAD'I❌_

_Ban yarda wata ko wani yajuyamin sigar labari na ba,koda kuwa kalma dayace! duk wannan ya aikata hakan a gareni zamu gamu a fadar mai sama!!_

_i dedicated dis page to merh faty😍❤️😍 dukda ma daiii......!!🌻_

*charpter 5*


Cikin murmushi da annashuwa kwance bisa fuskarsu suka k'araso dining area dake ta cikin parlon!! deeyerh direct jikin mamami taje ta narke mata,inda itakuma take shafa mata lallausar dogon gashinta mai gazar gazar kasancewar yololon gyalen dake kanta ya zame!

"mamami nah ina kwana" "lafiya qlaou rabin raina,fatan kin tashi lafiya?" mamami tak'are maganar tanaa manna mata peck akan goshinta bayan ta d'ago deeyerh data narke mata a jiki!!

lumshe dara daran idanunta deeyerh tayi,fes ta sauke shi bisa fuskar mahaifiyar tata! takuma chanza fuska kamar baby dol cikin sangartar yan autancin daya motsa mata tace "mamami shine kika barni na kwana ni kad'ai bacin kinsan cewa bababi baya gari koh...?"

har yanzu dai wannan murmushin dake fuskar mamami bai b'ace ba tace "amin afuwa yar gidan bababinta,baza'a sake ba kinji rabin raina...?" takare maganar tana dan shafa kumatunta alamun lallashi!

murmushin lalacin data sabayi tayi tace "dole ai rabin rai taima mamaminta afuwa!! sbd gudun sa idon su oh'oh da oh'oh" takare maganar tana sakin wani murmushi mai tafiya da sasssanyar dariyar dayasa kumatunta lob'a wa,da alamu dai tsokala ta k'wak'ulowa kanta!

aikuwa dukkansu sai gasu sun fara k'yak'yata dariyar sbd sunsan bada kowa takeyin tsokalar tata ba sai musa da umaar!!

b'ata fuska musa yayi shima yace "allah mamami ki jama yarinyar nan kunne,ta raina ni dayawa idan ba haka ba kuma zan fasa ma yarinya baki yau dinnan a gidannan" yakare maganar yana zare idanuwa shi ala dole yaya babba!

nanma dai dariyar suka somayi masa,sbd bayau suka saba ganin y'ar t'samar dake tsakanin musa hamdeeyerh ba! ita t'sokala shikuma rashin hakuri!

mikewa tayi daga jikin mamami taje ta zauna a tsakiyar ya marwan da anty nawwwra! gayshe sa tayi cike da girmamawa shikuma ya ansa yanaa sakin mata murmushi!

saida suka gama shiriritarsu kana aka k'ara sabon gaysuwa,daganan kuma nawwara ta mik'e tayi serving nasu,daga nan kuma suka fara bama cikinsu hakkinsa,saida suka kammala tsap, daya daga cikin ma'aikatan gidan mai suna raihana wacce takasance t'sarar hamdeeyerh ce itama tazo ta kwashe komai takai kitchen !

suna nan zaune a gurin nawwara tafito cikin simple shigarta,lapcot naata rataye bisa kafad'arta tamasu sallama inda ta kad'a kan deeyerh suka wuce tare,bata son barinta a gidan,sbd zata kai dare a wajen aiki,kuma tasan tsaf idan deeyerh tasamu guri saita tafi gurin shan barasar tata na jaraba!

sunxo wajen motar suka tarda baba mai gadi tare dansa a zaune wajen jan benchi! dan risinawa nawwara tayi ta gayda baba yusufa wato mai gadin su!!

"ina kwana baba" cike da walwala ya ansa da "lafiya qlaou yar albarka,har an fito za'a wuce wajen aikin ne...?" "eh wlhi baba gashi ma nayi letti,agaidamin mama idan na dawo zan shigo mugaisa insha alllahu" "karkiji komai y'ar albarka,kijeki dawo din allah yabada sa'a yamaku albarka" "amen baba" ta ansa masa itama cike da farin ciki!

waigowa tayi inda wannan saurayin yake tagaishe sa,shima ya ansa mata kadaran kada han!!
hamdeeyerh mma gaishe da baba tayi amma kam ko kallon inda wannan matashin yake batayi ba ballantana yasaka ran zata gaishesa!

tafiyar minti goma yakaisu asibitin _N & FAM HOSPITAL_ cike da girmamawa likitocin ke gaysheta,itama tana ansawa cikin sakin fuska a haka har suka k'ara office nata!

samun guri deeyerh tayi ta zauna kan daya daga cikin bed rest dake office din!!saida nawwara tayi cike ciken files din da duk yakamata kana ta mike tazo ta zauna gefen deeyerh ta kamo hannunta,ta rike su t'sam, tana mai fuskantar yar uwar tata,
"dear na rok'e ki da girman allah karkije ko nan da k'ofar office dinnan...! idan har kina sona da zuciya daya,domin ko nasan yanzu haka fakon fita ta kikeyi kije ki yad'a halin!"

cike da yanayin damuwa ta kwanta jikin y'ar uwar tata "anty na wlhi nima ba laifi na bane yasaka nake shan wannan abin,kullum inaso na daina amma sainaji kamar wanda ake k'ara tunzurani izuwa shan barasa,wanda idan ban sha ba sam banajin dadin rayuwata,sainaji kamar ana yankan naman jikina,amma ki tayani da addu'a allah ya yaye mani wannan masifar yar uwata" tak'are maganar tana sakin siririn kuka mai cike da tausayin kanta!!

idanunwaan nawwara ne yaciko da hawayen tausayin yar uwar tata,bata samu zarafin magana ba akayi nocking saida ta goge ma yar uwar tata hawayenta,ta kwantar da ita ta bata pect kana ta tatttari duk files din daya kaamata ta fice,inda suka had'u da daya daga cikin nurse suka wuce wars domin dubo marasa lahiya!!

lumshe idanunta hamdeeyerh tayi hawaye ta kwaranya daga cikin idanunta na tausayin kanta !! itama tanason ace ta daina wannan banzan dabi'ar tata da ta farashi cikin shekara daya amma abin yaci tura,kwata kwata da dinnan bata da rashin kunya sai girmama na gaba da ita,amma yanzu duk wasu halin yarinya mara kirki ta sayosu ta yafa ma kanta,wanda batasan dalilinsu ba!!

ita batasan ma idan bababi yaji labari ya zasu karke dashi ba ,harma tsoron ranan da zai fuskanci halin da take ciki takeyi!fatan ta dai allah yasa kar yamata mummunar fahimta,ya fahimce t kamar yadda mamami da yar uwarta suka fahimceta!!!

a haka dai wani wahalallen bacci yayi gaba da ita mai cike da sark'ak'iya da mafarkai marasa kan gado!!

pls idan kika karanta kimin forwding dan allah and then comment!!


vote
comment
share

_UMMIE2018_💜

HAMDEEYERH!Where stories live. Discover now