part 19

40 6 2
                                    

_*Typing*_💻

          
       _*🌻🌻HAMDEEYERH🌻*_       

©️ *HIKIMA WRITER'S ASSO.🌻*
_Home of peace, joint of entertainment,to educate & to enlighten  our reader's._

   
_LITTAFIN KYAUTA._
*MALLAKAR*_ummie2018💜_

_*marubuciyar*_

1- _AYSHAT(complted)_
2- _ZATOH(completed)_
3- _NUNA SO GABAN KISHIYA(completed)_
4- _TA'UMMU KA (incomplete)_
5- _NIGERIA KO NIGER(incomplete)_
6- _ANYA KUWA...?(rate book)_

     ~and now~

7- _HAMDEEYERH_

_GARGAD'I! GARGAD'I!GARGAD'I❌_

_Ban yarda wata ko wani yajuyamin sigar labari na ba,koda kuwa kalma dayace! duk wannan ya aikata hakan a gareni zamu gamu a fadar mai sama!!_

            *charpter 19*

banda salati babu abinda a al'ummar dake gurin keyi sbd shiga rud'u da tashin hankali dakuma t'sant'sar al'ajabi!

bama kamar hamdeeyerh data zama butum butumi a wajen ta gagara cewa uffan ballantana ta mat'sa daga inda take domin k'arin bayani tun lokacin da taji cewa wai ita d'in fa y'ar gaba da fatiha ce,sannan mamaminta ba mahaifiyarta bace ta ainahi,itadin marik'iyarta ce!

innalillahi wa'inna ilaihir raji'un,way'annan sune kawai kalmomin dake kai kawo cikin zuciyarta domin neman salama gurin uban giji!

mamami kam idan nace maku ga yanayin data shiga a wannan lokacin nayi k'arya,sbs abubuwan sun had'e mata ne goma da ashurin,na d'aya wannan uban gadar zare da amma ta d'aura masu ita da mijinta na t'sawon lokaci batare da sun farga ba!

na biyu ashe ma itace sanadiyyar da y'arta mafi soyuwa cikin zuciyarta ta gaza samu mashinshini na t'sawon good 27yrs,na uku itace sanadiyyar kamuwarta da hawan jini tun bata kai haka ba...? kai allah ya isa...! allah ya isa! allah ya isa ban yafe maki ba hafsat...! wayannan sune kawai kalmomin da mamami ke ambata ciikin fitar hayyaci ...!

bababi kam yazama speechless a wajen a zaune,ji yake kamar wanda aka d'aure masa jijiyoyin jikinsa baki d'aya t'sabagen shiga tashin hankali da bala'i!! wai dama duk wannan bad'akalar da yake faruwa da danginsa ba kowa bane yajawo sai shi akan k'aramin abu da bai taka kara ya karya ba...?

ashe dama har yanxu ana samun mutane kalar hafsat masu kalar zuciya na jahilan farko na shegen rik'on abu,da kuma d'aukar fansa a zuciyarsu...? shi kam matar nan ta cucesa duniya d lahira bazai tab'a yafe mata ba wlhi...!(allah ka rabamu da bak'ar zuciya da kuma hassada ameen)!

nawwara kam kukan bak'in ciki da takaici takeyi tun d'azu,matar nan annobace  cikin family nasu,wai duk a dalilin wani shirmen laifin da basu san dashi bama ko haifarsu ba'ayi ba a duniya da aka tashi d'aukar fansa sai ya sauk'a akansu? wannan masifa dame tayi kama fisabilillahi...? babban tashin hankalinta ma wai dear nata ba y'ar mamamin bace!? wasu sai su k'ira ta da kalmar _shegiya...?_ kai wallahi da sake dole a daukan masu mataki akan matar nan dan bazasu yadda ba! sbd cutar da ta masu yafi k'arfin a barta haka nan batare da an hukunta ta ba!

marwan,faruq da musa kam sunyi t'suru ne sbd basusan mai zasu iya cewa akan wannan abinba ko kad'an! a cikin zuciyar marwan kam ji yake ko marak'isiyyerh itace autar mata ya hak'ura da ita,duk kuwa da kalar d'umbin soyayyar dasuke ma junan su wanda babu wanda yasani illa hamdeeyerh,dan haka tun a lokacin ma yaji bazai iya auranta ba sbd bak'in halin uwar ta wata k'ila ta zuk'o a nono,hakan yasaka shi ke aika mata da wata k'atuwar harara daga wajen!

goggo salamatu da inna kam sun zama speechless suma,sbd sukam ashe suna canne a garin zubda zumuncinsu da sukayi abubuwa daya sun faru a _duniyar_ y'an uwan nasu batare da sanin d'aya daga cikin su ba,lallai duniya ta zama abinda tazama!

abbu...!! tunda hafsat tafara magana kansa yake k'asa sbd t'sananin t'sanar hafsat data masa dirar makiya da kuma takaicin wannan annobar dayake zaune k'ark'ashin inuwa d'aya da ita batare da saninsa ba!! shikam baiga dalilin dazaisa ya k'ara zama inuwa d'aya tare da mai bak'ar zuciya kalar tata ba!

ya audu da baba kamaye a mar'sayinsu na manyan wajen basu san ma ta inda zasu fara judjing wannan bala'in ba sbd abin na naiman yafi k'arfin su ne sukam,bama kamar ya audu da hafsat takansance k'anwarsa d'aya tilo da allah ya basa a duniya dayake matik'ar kaunarta!

marak'isiyyerh tuntini ta tashi daga jikin mahaifiyar tata zuwa gefen mahaifin ta tunda uwar tata ke bada labarin kalar t'siyar data shuka t'sawon shekaru batare da d'igon nadama ba a tattare da ita,ga wani kalar t'soron da ya mamaye zuciyarta na ganin yadda marwan ke aiko mata kallo na t'sant'sar t'sana da k'yama,wanda hakan ba k'aramin dukar zuciyarta yake ba!

amma mik'ewa cikin tattaki tayi tana zaga cikin yalwataccen parlon tana sakin wani murmushi na farin ciki,domin ko a cikin zuciyarta ji take ko yau ta fad'i ta mutu batayi asara ba tunda tasamu cikar burinta na ganin adama da adama cikin _GARARIN RAYUWA_ !!

wata kalar dariyar data shek'e dashi ne yadawo da kowa daga cikin suman wucin gadin dasuka shiga duk aka suba mata ido ganin yadda take kamar sabuwar kamu!

"mallam adamu k'yakk'yawan saurayi maiji da kansa mai wulak'anta em mata sbd farin jinin da allah yayi maka a baya,shin mai zaka iya cewa a yanxu dangane da abinda na maka...?" amma tak'are maganar cikin jin kai da kuma izza kamar wacce tayi wani abin arzik'i!!

babu wanda yasamu zarafin magana cikin parlon saima k'ara sake baki dasukayi sbd ganin t'sant'sar taurin kai kalar na jahilan farko a gurin amma tunda gashi babu alamar dana sani tattare da ita aka abubuwan data aikata t'sawon rayuwarta!

basu ga tashin hamdeeyerh ba,basu ga lokacin isowarta gurin ba,saijin k'arar wani gigitaccen marin daya rat'sa dodon kunnen jama'ar dake gurin baki d'aya yayi,wanda kamin su dawo daga suman wucin gadin suka k'ara jin karar marin daya gitta dodon kunnuwansu dayafi na farko!

da wani shimfidadd'en mamaki kwance bisa fuskar amma ke bin hamdeeyerh da kallo sbd yadda ta rufe idanuwanta ta wawwaska mata mari kamar bata haife ta ba!

"lalle yarinya kin d'aibo da zafinki tunda har kika iya d'aukar k'azaman hannunki a mat'sayinki na shegiya y'ar gidan mai aiki maciya amana kika mari fuska ta,zan tabbatar maki da cewa ke d'in karamar y'ar iska ce a yau basai gobe ba..." amma tak'are maganar da wani kalar emotion a fuskarta na t'sant'sar rashin imani da kota kwana!

ya audu ne ya mik'e cikin zafin nama yafara ball da amma kamar allah ne ya aiko sa ganin yadda hamdeeyerh ta durk'ushe a gurin ta fasa gigi taccen kuka mai matuk'ar tab'a zuciyar mai sauraro!

babu wanda yayi yunk'urin k'arbanta a cikin wannan parlon dukda kururuwar datakeyi wanda har baba yusufa dake baki gate saida yajiyo ta,hakan ne yasaka shi kwasowa  a dari zuwa cikin gidan!

  

  
vote
comment
share

       _UMMIEN2018_💜

HAMDEEYERH!Where stories live. Discover now