part 20

41 6 0
                                    

_*Typing*_💻

          
       _*🌻🌻HAMDEEYERH🌻*_       

©️ *HIKIMA WRITER'S ASSO.🌻*
_Home of peace, joint of entertainment,to educate & to enlighten  our reader's._

   
_LITTAFIN KYAUTA._
*MALLAKAR*_ummie2018💜_
*💞oum muntaz💞*

_*marubuciyar*_

1- _AYSHAT(complted)_
2- _ZATOH(completed)_
3- _NUNA SO GABAN KISHIYA(completed)_
4- _TA'UMMU KA (incomplete)_
5- _NIGERIA KO NIGER(incomplete)_

6- _ANYA KUWA...?(rate book)_

     ~and now~

7- _HAMDEEYERH_

_GARGAD'I! GARGAD'I!GARGAD'I❌_

_Ban yarda wata ko wani yajuyamin sigar labari na ba,koda kuwa kalma dayace! duk wannan ya aikata hakan a gareni zamu gamu a fadar mai sama!!_

   *charpter 20*

ya audu bugun amma yake kamar yasamu kayan wanki,kuma duk ihun da takeyi bai sarara mata ba and babu wanda yayi yunk'urin karb'anta a wajen sbd haushinta dasuke ji!!

sai kukan marak'isiyyerh dake tashi itama sbd kunsan ance koma dai menene uwa uwace babu mai iya canza wa,tana da niyyan zuwa mahaifin nata ya janyota yayi hugging nata yana lallashinta cike da tausayawa dakuma t'sant'sar soyayyar y'ar tasa!

a d'ari baba yusufa ya danno kai cikin parlon batare da yayi sallama ba, wanda haka yasa suka zuba masa ido baki d'ayan su,hakan ko ba k'aramin mamaki ya basa ba ganin su zaune kamar babu abinda yake faruwa gaban idon su!!

ga kuma ana dukan matar aure gabansu sun gagara hanawa wanda ko dan girma,mutuncin dakuma kima da aure keda shi gurin uban giji yaci ace wani ya yunk'uro sbd karb'anta!

batare da b'ata lokaci ba yasamu ya shiga t'sakanin su da k'yar ya karb'ota a hannunsa,wanda zuwa wannan lokacin kuka harda hawaye ya audu keyi sbd takaicin bak'in hali kalar na kanwar tasa!

kowa tausayin ya audu ne yakamasa ganin yadda yake hawaye a mat'sayinsa na babban mutum mai kima da daraja,banda allah wadai babu abinda kowa keyi da halin hafsatu a wannan lokacin!

itakam tunda tasamu aka karb'e ta a hannun ya audu ta fice daga gidan a hargit'se kamar zata kife,babu wanda yayi yunk'urin bin bayanta ballanta asan inda zata tafii!

hakuri dai baba yusufa yayi ta basu kamin ya kad'a ma wandon sa iska ya fito yana tambayar kansa abinda yake faruwa cikin gidan nasu amma babu mai basa ansa,dan haka sai yaja bakinsa ya t'suke ya fuskanci aikinsa dake gabansa!!

saida aka k'ara nat'suwa a cikin parlon kowa yasamu waje yazauna,inda hamdeeyerh ke jikin ya marwan sai sauk'e ajiyar zuciya take sbd t'sananin kukan da tayi !!

   and ta zubama mamamu ido daga inda take tana kallonta cike da t'sant'sar soyayya tunda bata da wata uwar da zatayi tutiya da ita a mat'sayin tata idan ba ita ba!

sannan a labarin da amma tagama bayarwa a yanxu ta fahimci mamami ba k'aramin sonta takeyi ba,kawai dai laifin da mahaifinta ya aikata a mat'sayin ajizanci kalar na d'an adam da kuma kishi kalar tamu ta mata ya tusa nawa mamamin jin zafinta!!

wanda ta tabbata koda itace saii iya inda k'arfinta ya k'are idan mijinta yamata hakan,itakam ma ganin k'ok'arin mamamin tayi sosai,domin ko sai mai k'yakk'yawar zuciya kalar tata ne zai iya abinda tayi dan haka ko kad'an bataji ko da d'igon son da take ma mamami ya ragu a zuciyarta ba!

maganar da baba kamaye yafarayi ne yadawa dasu kowa cikin nat'suwarsa inda yafara magana "Alhmdlh ala kullu halin yabo da godiya sun tabbata ga allah mad'aukakin sarki mai kowa mai komai mai maida sarki bawa a duk lokacin lokacin da ya so!

HAMDEEYERH!Where stories live. Discover now