_*Typing*_💻
_*🌻🌻HAMDEEYERH🌻*_©️ *HIKIMA WRITER'S ASSO.🌻*
_Home of peace, joint of entertainment,to educate & to enlighten our reader's._
_LITTAFIN KYAUTA._
*MALLAKAR*_ummie2018💜_
*oum muntaz*_*marubuciyar*_
1- _AYSHAT(complted)_
2- _ZATOH(completed)_
3- _NUNA SO GABAN KISHIYA(completed)_
4- _TA'UMMU KA (incomplete)_
5- _NIGERIA KO NIGER(incomplete)_
6- _ANYA KUWA...?(rate book)_~and now~
7- _HAMDEEYERH_
_GARGAD'I! GARGAD'I!GARGAD'I❌_
_Ban yarda wata ko wani yajuyamin sigar labari na ba,koda kuwa kalma dayace! duk wannan ya aikata hakan a gareni zamu gamu a fadar mai sama!!_
*_ALHMDLH GODIYA TA TABBATA GA ALLAH MAD'AUKAKIN SARKI MAI KOWA MAI KOMAI DAYA BANI DAMAR KAMMALA RUBUTA WANNAN GAJEREN LITTAFIN NAWA WATO ~HAMDEEYERH~ !ABINDA NA RUBUTA DAIDAI ALLAH YABANI LADAR SA...! INDA NAYI KUSKURE KUMA ALLAH YA YAFE MANI BADAN NAKAI BA KONA ISA AMEEN...! ALLAH YASA KODA ABU D'AYA NE YAZAMANA DUK WAYANDA SUKA KARANTA LITTAFIN NAN SUN AMFANA DASHI DAMA DUK WAYANDA ZASU KARANTA SA AGABA ALBARKACIN ANNABI MUHAMMAD SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM(S A W) AMEN_*
🔚🔚🔚🔚 *charpter 30*🔚🔚🔚🔚
******Sabuwar rayuwa******
gadai hamdeeyerh gakuma abdul a k'ark'ashin inuwa d'aya ta ma'aurata dakuma y'arsu umaima da suka d'auki dikkan gatan duniya suka d'aurama yarinyar,wanda ko mot'si tayi har rige rigen tambayarta ko akoi wani abinda take so ne...? sangarta duniya kala kala sun dauka sun daura ma yarinya fa sunan tausayin maraicinta..! wanda hakan yasa su mamami niyyan d'auke ta daga gabansu amma sam sukace ba haka ba!
da sukaga za'a mat'sa masu ma kuka suka sanya ma su mamami ai dan sunga nawwara ta tafi tabarsu ne yasa aka fara nuna masu wariya bayan kuma ita tace amanarsu tabarma su mamami,wanda ala tilas aka bar masu yarinyar a bisa sharad'in gyara zamantakewae yarinyar tindaga yanxu basai ta girma ba sbd ice tin yana d'anye ake tankwara sa bawai sai ya gama bushewa k'ik'ir ba!
hakan yasa suka fara d'aura yarinyar kan hanya mai kyau dasuma suka fi jin dad'in hakan,amma dikda haka ba k'aramin son yarinyar sukeyi ba!
rasuwar nawwara yasa kowa zama so calm,shuru babu wani armashi bawai kuma dan suna jaa da hukuncin allah ba ne! kawai kunsan ance bawai mutuwa akeyima kukan ba sai sabon dakayi da mutum tunda kaima kasan cewa naka lokacin mutuwar nan nan zuwa! kullum cikin mata addu'ar samun rahama sukeyi wanda wannan ne kad'ae gatan da zasuyi mata a halin yanxu (allah kasa muyi kyakkyawan k'arshe)
mamami dasu bababi diksun dauki kaddararsu saibin yar tasu da kyakkyawan fatan dacewa a lahira sukeyi mata a kullum wayewar garin allah!
babu wanda ya kara daga abinda abdul ya aikata har yanxu hatta gasu mama habeba da suma ba k'aramin kewar nawwaran sukayi ba!
su ya marwan dasu ya faruq duk suma sukan kira akai akai suanjin lafiyar umaima data zama y'ar gata ta gaban kwatance cikin dangi suna fatan ta gado sanyi dakuma halin dattako kalar na mahaifiyarta!
aanyi auren musa da mardiyya wtan daya gabata batare da wani shagali sosai ba,suna cikin kano suma a unguwar redbricks (jan bulo)...!
bangaren zaman takewar hamdeeyerh da abdul kam zamu iya cewa k'adaran k'adahanne ne sbd dik abinda ya umarceta tayu masa babu musa ko gunguni take aikata hakan sbd cika alkawarin datayi ma yayarta...! kuma shima yana k'ok'ari wajen ganin ya kula da hakkinta daya dataya akansa! amma fa wani abu na kwanciyar aure bai tab'a had'a su ba har yanxu sbd bai nemeta ba! kuma itama tana tsoron kai kanta taje tasha wahala!
YOU ARE READING
HAMDEEYERH!
Historical Fictionlabari ne mai cike da sark'ak'iya,idan kuna bibiye da alkalamin ummie2018 zai warware maku zare da abawa