part 16

42 7 3
                                    

_*Typing*_💻

          
       _*🌻🌻HAMDEEYERH🌻*_       

©️ *HIKIMA WRITER'S ASSO.🌻*
_Home of peace, joint of entertainment,to educate & to enlighten  our reader's._

   
_LITTAFIN KYAUTA._
*MALLAKAR*_ummie2018💜_
*💞oum muntaz💞*

_*marubuciyar*_

1- _AYSHAT(complted)_
2- _ZATOH(completed)_
3- _NUNA SO GABAN KISHIYA(completed)_
4- _TA'UMMU KA (incomplete)_
5- _NIGERIA KO NIGER(incomplete)_
6- _ANYA KUWA...?(rate book)_

     ~and now~

7- _HAMDEEYERH_

_GARGAD'I! GARGAD'I!GARGAD'I❌_

_Ban yarda wata ko wani yajuyamin sigar labari na ba,koda kuwa kalma dayace! duk wannan ya aikata hakan a gareni zamu gamu a fadar mai sama!!_

   *charpter 16*

    
"_Deejama_ ,y'ar aikina ce,ana gobe zaki zo aka kawota gidannan daga can k'auyen mazigai a mat'sayin mai tayani kula da gida,kinsan sha'anin aikin babban gida kamar wannan saida mataimaki"

"wannan haka yake k'awata,allah yasa ba maciya amana bace,yadda naga idanuwan yarinyar a t'satst'saye daga gani zatayi fit'sara da fi'ili,dan haka kiyi hankali da ita..."

"hmm,wlhi hafsat kamar kuwa kinsan abinda yake mint'sinin zuciyata game da wannan yarinyar! sam banajin dad'in zama da ita inuwa d'aya,sabida acikin jikina nakeji wani babban al'amari na shirin tunkarar rayuwar zaman aure na muddin ina tare da ita,gashi sam bata shakkata yarinyar,wanda hakan ba k'aramin mamaki yake bani fa,idanunta a t'sat'st'saye fa suke in gaya maki kamar t'sohuwar kilaki"

dariya na shek'e dashi a wannan lokacin da muke magana,domin ko na tabbata komai zaizomin da sauk'i akan tafiyata,tunda a maganganun adama na fahimci ita kanta tana t'soron faruwar wani lamari ne t'sakanin yarinyar da mijinta adamu!

"karki damu k'awata,insha allahu babu abinda zai faru,nasan ba komai ke d'awainiya dake ba saidan gudun oga adamu yace zai auro maki yar fulani ko kuma nace y'ar aiki a mat'sayin kishi..."

tun kamin na k'arasa adama ta kwashe ni da wani kalar marin da tunda uwata ta haife ni ba'a tab'amin irinsa ba,wanda saida naga gilmawar farin haske ta gefen idanuwana t'sabagen yadda marinnan ya rat'sa min jini da t'sokata!!

a lokacin idan nace maku bacin rai ma ba lallai ne ku fahimci abinda nake nufi ba jama'a,amma ko ni kad'ai nasan k'uncin dana shiga!

batare da na k'ara kallon shashin datake ba,ko kuma na mata magana ba na had'a kayana nabar gidannanta,tana ta huci kamar kububuwa!! ina fitowa naci karo da wannan yarinya da aka k'ira da deejama zaune k'ofar gida sai rusan kuka takeyi!

sassauta fuskata nayi domin jin ba'asin zamanta a wajen tana kuka...?

"anty dan allah ki taimake ni nakoma k'auyenmu wajen yayana,sunmin alk'awari a ranar zasu k'ira wayar hajiyar gidannan amma tun randa goggo na ta koma banji sun k'ira ba,kuma inason naji muryarsa sabida shi kad'ai yaragemin" fad'ar deejama tana sharb'an kuka!

k'ara sassauta murya nayi ta yadda zan k'ara bugar cikinta nace "amma miyasa kika damu da sai kinji muryar yayanki...? bacin kuma zuwan naki kwana 4 ne yau kwata kwata yau idan na lissafa daidai...?"

"wannan alhajinne na gidannan dan nace yana da kyau,ya aure ni  tunda nima a k'auyenmu ance ina da kyau shine ya mammare ni har kaina saida yayi ciwo d'azu..."

acikin zuciyata kam dariyar farin ciki nayi,domin ko fad'uwa tazo daidai dazama a wannan tafiyar tawa!

hak'uri nabata nace tayi ta hakuri tamaida komai ba komai ba insha allah adamu da k'afarsa zai dawo wajenta yana sonta,ita kuma a lokacin karta masa gaddama duk abinda ya umarce ta amsa masa,kuma duk randa nawado idan y'an gidan su basu zo d'aukarta ba dakai na zan dauke ta nakaita!

da wannan muka rabu da ita,na tafi da k'uncin da adama ta gasamin gakuma farin cikin ruguuguza rayuwar adamu da adama da zanyi a wannan lokacin!

deejama kam kasancewarta k'ank'anuwar yarinya bata san komai ba akan rayuwa sai murna takeyi,kan ance mata adamu da k'afarsa zai tako yazo inda take da sunan soyayya wanda ko tunanin mai zaije yadawo ma batayi ma rayuwarta!

adama kam sai bayan tafiyata ne ka tafarga da abinda tamin,wanda ta tabbata da ita akayiwa abin tabbas bazata hakura ba!

haka shima adamu daya gida bai ganni ba ko a kwalar rigarsa ballanta yaji yaushe na tafi!

komawata gida na tadda mahaifiyata na jinya wanda basu sanar dani ba daga ita har yayana wanda hakan ya d'agamin hankali har ya mantar dani bak'in cikin adama da mijinta baki d'aya muka fuskanci rashin lafiyar ta!

tana shan jinya sosai abinka ha jikin t'sufa wanda a wannan lokacin idan ka kallemu saika tausaya mana,domin ko mahaifiyarmu ce kad'ae ta rage mana bamu da kowa,sai kuma matar yayana da y'arsu guda d'aya!

saida muka shafe wata biyu muna jinyar hajiyarmu muka wayi gari babu ita allah ya anshi abarsa,wanda hakan ba k'aramin girgiza zuk'atan mu yayi ba! kuka kam dole daga baya muka hak'ura muka fawwala ma allah lamuranmu,

bayan kwana bakwai da rasuwar hajiya adama da adamu suka zo mana ta'aziya,bayan mun keb'e da adama takuma bani hakuri akan abinda tamin na nuna mata komai ya wuce a guri na karta k'ara tado maganar!

bayan anyi arba'in na mahaifiyata ne kuma na tafi wajen wani boka dana tab'a ji k'awaye na na makaranta sunayi domin neman cikar burinsu,kuma a yadda toshewar basirata da tunanina yabani kawai nima naje domin d'aukar fansa akan adama da adamu!

duk wannan budurin da akeyi yaya sam bashi da labarin komai,domin ko t'soronsa nakeji duk iskanci na sbd bayamin da wasa!

a tashin farko deejama dana manta da ita ta fad'omin a rai,banyi k'asa a gwiwa ba kwararowa boka buk'ata ta wanda ta taho da k'warin gwiwa gida, sabida yadda naji bokan nan ya zayyano min duk abinda ban ma ambata masa ba nasan aikinsa kam babu wasa!

a wannan lokacin ne allah ya had'a ni da mahaifin marak'isiyyerh wanda aka sha shagalin auren mu kamar babu gobe muka tarkato aka kawo ni kano nima,unguwar rijiyar zaki wanda hakan ba k'aramin dad'i yamin ba!

hajiya adama sune amara k'irjin biki,bayan biki na da wata d'aya ina zaune a parlo na na afka cikin tunani sabida jin shuru hae yanxu banji wani issue ba daga gurin boka na muruci!

kwat'sam saiga adama kamar wacce aka hankad'o ta, ta fa'domin gida babu sallama sau kwankwad'an kuka na fitar hayyaci takeyi kamar wacce akace mata uwarta ta mutu!

  
vote
comment
share

       _UMMIEN2018_💜

HAMDEEYERH!Where stories live. Discover now