part 11

45 7 2
                                    

_*Typing*_💻

          
       _*🌻🌻HAMDEEYERH🌻*_       

©️ *HIKIMA WRITER'S ASSO.🌻*
_Home of peace, joint of entertainment,to educate & to enlighten  our reader's._

   
_LITTAFIN KYAUTA._
*MALLAKAR*_ummien2018💜_

_*marubuciyar*_

1- _AYSHAT(complted)_

2- _ZATOH(completed)_

3- _NUNA SO GABAN KISHIYA(completed)_

4- _TA'UMMU KA (incomplete)_

5- _NIGERIA KO NIGER(incomplete)_

6- _ANYA KUWA...?(rate book)_

     ~and now~

7- _HAMDEEYERH_

_GARGAD'I! GARGAD'I!GARGAD'I❌_

_Ban yarda wata ko wani yajuyamin sigar labari na ba,koda kuwa kalma dayace! duk wannan ya aikata hakan a gareni zamu gamu a fadar mai sama!!_

   *charpter 11*

"Alhmdlh alhaji mu godewa allah domin ko allah ya tak'aita ma bayinsa wahala,ma'ana dai an samu sun farfad'o amma bacci sukeyi a halin yanxu sbd allurar baccin da muka masu"

ai kuwa take suka fara hamdala ga uban gijin talikai daya nuna masu ikon shi,sbd kaf cikin su basu tunanin jin daddad'an labarinnan ba,gashi kuma babu wayonsu ballantana dabarar su allah ya nuna masu ikon sa!

gaba d'ayansu suka d'unguma zuwa inda yayan nasu suke kwance,bababi kam dama kan yarsa yayi,amma da abbu kuma sukayi kan yar tasu!

gasu a kwance flat kamar gawawwaki,amma kuma ganin yadda suke sauk'e numfashi ne kawai ya kwantar masu da hankali da tabbacin rayayyu ne!!

bandeji ne nannad'e jikinsu,ko sutura babu,ga goshi hamdeeyerh dake daure shima da bandejin,

dare d'aya ta k'ara zama y'ar shafal da ita duk ta zurma!! ba halin tab'ata a bisa umarnin likita,hakama iyayen siyyerh sun sakata a gaba!! idanun amma sai t'siyayar hawayen da ita kad'ai tasan na mainene takeyi!

sai yanxu hankalin bababi dasu ya marwan yadawo jikinsu,inda kuma rashin zuwan mamami ya dami bababi sbd shifa shaf yama mance da batun nawwara daya t'sallaketa a sume daren jiya!!

marwan ne ya fara tariyo abubuwan dasuka faru jiya,sbd rashin ganin mahaifiyar tasu a wajen!

mik'ewa yayi a hargit'se yana sakin salati wanda hakan yajawo hankalinsu baki d'aya zuwa garesa!

"lafiyarka kuwa babana...?" fad'ar bababi kenan yana mai kafe d'an nasa da idanuwa,

"bababi nawwara!! jiya mun barota cikin mummunar yanayi,gashi kuma dukkan mu nan babu wanda yasan halinda take ciki tunda babu wanda ya t'saya yabi takanta sannan nabar wayoyinmu a gida ballantana musan halin da ake ciki yanxu"  

duk shuru sukayi a wajen,hatta ga faruq domin so yake yaga reaction dinda mahaifinnasu zayyi,musa kam sai yanxu ma yatuno da sumar yayar tasa!!

amma da mahaifin siyyerh ma kallonsu suke domin naiman k'arin bayani

anan faruq ya shaida masu abinda yafaru tiryan tiryan abinda yafaru! suma shiru kawai sukayi sbd maganar ba huruminsu bane!

bababi kam da tun d'azu ya dafe kansa na k'asa ya gagara d'ago kansa ballanta suka yanayin dayake ciki,shi kad'ai yasan abinda yake sak'awa cikin zuciyarsa!

iyayen siyyerh k'iran dangi sukayi na nesa dana kusa suka shaida masu abinda yafaru ta waya,kan kace me? har asibitin yacika da yan uwa da abokan arziki,duk wanda yagansu kuma sai ya tausaya masu dukda ma halinsu ne yajawo masu,sbd an samu yan tsurkun dasuka san daga inda suke abin yafaru,kunsan ance an daina kiwob dabba yanxu saina d'an adam!

HAMDEEYERH!Where stories live. Discover now