part 18

51 8 2
                                    

_*Typing*_💻

          
       _*🌻🌻HAMDEEYERH🌻*_       

©️ *HIKIMA WRITER'S ASSO.🌻*
_Home of peace, joint of entertainment,to educate & to enlighten  our reader's._

   
_LITTAFIN KYAUTA._
*MALLAKAR*_ummien2018💜_

_*marubuciyar*_

1- _AYSHAT(complted)_

2- _ZATOH(completed)_

3- _NUNA SO GABAN KISHIYA(completed)_

4- _TA'UMMU KA (incomplete)_

5- _NIGERIA KO NIGER(incomplete)_

6- _ANYA KUWA...?(rate book)_

     ~and now~

7- _HAMDEEYERH_

_GARGAD'I! GARGAD'I!GARGAD'I❌_

_Ban yarda wata ko wani yajuyamin sigar labari na ba,koda kuwa kalma dayace! duk wannan ya aikata hakan a gareni zamu gamu a fadar mai sama!!_

_Thanks for your prayers sisters,allah yabar zumunci_

   *charpter 18*

    
a wannan ranar adama da adamu ba k'aramin tashin hankali suka shiga ba,wanda idan na t'saya fasalta maku ma ba lallai ne ku fahimta ceni dai dai ba,sunyi kuka iya kuka,sannan babu wanda yasan duk bidirin da akeyi cikin danginsu na misau!

hatta ga cikin unguwarsu ma babu wanda yasan cewa deejama na da ciki balllantana asamu y'ankai t'surku,wanda hakan yasaka adamu da adama rufe zancen t'sakanin su kan yarinya y'ar adama ce!

a ranar akayi wankan gawan deejama batare da sanin danginta ko wani nata ba aka mik'ata gidanta na gaskiya,a kuma wannan ranar adama ta fara shayar da hamdeeyerh a bisa umarnin adamu! wanda ba k'aramin soyayyar yarinyar bane yamata mugun kamu!

a ranar ana jimamin mutuwar deejama, kuma farin cikin samun k'aruwar yarinya da akayi way'anda basu san maike tafiya cikin gidan ba,kuma har zuwa wannan lokacin adama bata k'irani ta fad'amin abinda ke faduwa ba!

a ranar da akayi kwana bakwai da rasuwa deejama aka rad'a ma yarinya suna _hamdeeyerh_ da taci sunan mahaifiyar adamu,wanda nima kuma a daidai lokacin yawon arba'in d'ina ya hankad'o dani izuwa gidan adama na tadda daddad'an labari,babu abinda dama ta b'oyemin tun dafa farko har k'arshe!

naji babu dad'i sosai da naji mutuwar deejama amma kuma abinka ga zuciyar rashin imani ko d'ar banji ba na abinda na aikata,ballanta kuma na tuba na wat'sar da makaman yak'i na,a raina kam naji zan iya sarara masu inga iya gudun ruwan su akan komai kamin na ci gaba zuwa wani lokaci!

a haka fa rayuwa ta fara gangarawa harsu nawwara suka dawo gida suka tarda daddad'an labarin samuwar sabuwar k'anwarsu,ba k'aramin son yarintar suke ba wanda hakan duk yana daga cikin aikin adama,sbd yadda take son yarinyar yasaka ta tusa ma y'ay'anta ma daddad'ar soyayyarta!

komai suka samu baby hamdeeyerh,bama kamar nawwara,kasancewar ta ita kad'ai mace cikin y'an uwanta,tunda an sama mata y'ar uwa kam ai abin sai wanda yagani!

rayuwa na gangawara,seconni na shud'ewa,mintina na wucewa,hakama awanni na tafiya,kwanaki na sama satittika,satittika na watanni,watanni na zama shekaru!!

kwanciyar hankali,arzik'i mai t'safta,soyayya,da kuma fahimtar juna ne ke kai kawo cikin gidan adamu kwangila,a lokutan baya har k'auyen mazigai bababi da mamami suka je domin neman dangin deejama amma kuma babu wani daddad'an labari!!

domin kuwa ma an shaida masu ai yayan nata ma yashiga birnin kano domin a naimo k'anwar tasa amma har yanxu basu dawo ba,kuma tare da matarsa suka tafi!

haka suka dawo da jimamin rashin samu ahalin deejama,kuna har zuwa wannan lokacin amintaka da adama yana nan daram bai canxa ba!

a b'angaren nawwara ma data kasance babu wani namijin daya tab'a tunkarar ta da kalmar soyayya ba aikin kowa bane saini hafsatu! wanda tun tana k'arama na had'ata da wannan sihirin,sanin danayi cewa adama kaf cikin y'ay'anta na cikinta na fi k'aunarta,ni kuma duk hanyar da adama da adamu zasu samu farin ciki nake bak'in cikin gani,nafiso naga sun dawwama a cikin k'unci har k'arshen rayuwar su!

wani abin mamaki ma kuma shine,yadda naga hamdeeyerh ta taso yarinya mafi soyuwa a zuciyar mahaifinta,wanda a tunani na bazai so yarinyar kamar yadda zaiso yayansa na sunna ba amma sai naga akasain hakan,domin ko,koma a ina yake soyayyar hamdeeyerh na daban ne cikin zuciyarsa koda a gaban kowa ma babu ruwansa!

idan d'aya daga cikin yaran suna son abu,muddin y'ar lelensa tace bata so to kuwa ya zauna damar mar,babu gudu babu ja da baya!

hamdeeyerh da marak'isiyyerh k'awayene na k'ud da k'ud tun suna k'anana tare suka taso,hatta makaranta ma tare sukeyi abinsu,hakan ne yasaka ra'ayinsu yazamto d'aya a koma menene!

zuwa lokacin da hamdeeyerh takai matakin shekaru 16 sai yazamana,soyayyar da fifikon da bababi ke nunawa t'sakanin yayansa abin yafara mint'sinin zuciyar adama kasancewarta mace mai t'sant'sar kishi!

wanda kuma tasha mawa bababi magana amma sai yace tadaina shiga t'sakaninsa da y'arsa,sbd bata da kowa kamarsa,ita kuma ganin yadda yake mata ne abin yafara k'ular da ita,tunda dai ita tasan zuciya d'aya take zaune da yarinyar kaman sauran y'ay'anta ballantana yace tana ma yarinyar mugun hali ko wani abu!

nima kuma abin sai yake bani haushi ganin yadda yarinyar ta taso mai shiga ran jama'a da farin jini gurin kowa sbd kyawawan halayanta! dan haka na yunk'uro domin ida nufi na akanta,ni kuma y'ata bata da wannan farin jinin!

lokacin da adama tazomin da mat'salarta idanunta ya rufe yake, kawai mafita take nema a lokacin na ganin adamu yadaina nuna ma hamdeeyerh soyayya akan yayanta,dan haka nayi amfani da damata na tusa mata ra'ayin zuwa wajen boka domin biyan buk'atarta,kuma bansha wahala ba a lokacin ta amince sbd masifar kishin y'ar mijin nata daya sakata a gaba!

tare da adama mukaje wajen boka aka turama hamdeeyerh bak'ak'en aljanu a lokacin tana makaranta,wanda hakan yasakata fad'awa halin shaye shaye gadan gadan,wanda duk ranar da bata shaba babu zaman lafiya tare da ita!

kuma har zuwa lokacin babu wani namjin daya tab'a tunkarar nawwara da sunan soyayya ta auratayya ko kuma wani abu makamancinsa,sannan adama da nawwara ne kawai suka san cewa handeeyerh na shaye shaye wanda kuma nawwara na k'ok'ari wajen ganin ta hana y'ar uwar tata zuwa amma abin yaci tura!

    anan ke amma taja burki da maganar tata,tana bin a halin cikin parlon dasuka jik'e da zuffa sharaf t'sabagen tashin hankali dakuma kad'uwa dajin wannan mummunar labarin da hafsat tabasu!

  
vote
comment
share

       _UMMIEN2018_💜

HAMDEEYERH!Where stories live. Discover now