_*Typing*_💻
_*🌻🌻HAMDEEYERH🌻*_©️ *HIKIMA WRITER'S ASSO.🌻*
_Home of peace, joint of entertainment,to educate & to enlighten our reader's._
_LITTAFIN KYAUTA._
*MALLAKAR*_ummien2018💜__*marubuciyar*_
1- _AYSHAT(complted)_
2- _ZATOH(completed)_
3- _NUNA SO GABAN KISHIYA(completed)_
4- _TA'UMMU KA (incomplete)_
5- _NIGERIA KO NIGER(incomplete)_
6- _ANYA KUWA...?(rate book)_
~and now~
7- _HAMDEEYERH_
_GARGAD'I! GARGAD'I!GARGAD'I❌_
_Ban yarda wata ko wani yajuyamin sigar labari na ba,koda kuwa kalma dayace! duk wannan ya aikata hakan a gareni zamu gamu a fadar mai sama!!_
_na sadaukar da shafinnan zuwa gareku hikima writers officiall,allah yakara hade kanmu ameen!🌻_
*charpter 9*
_bangarensu bababi kam_baibi takan mota bama ya dumfari k'ofar gate na gidan,baba yusufa mai gadi da yaronsa suna t'saye kamar wayanda aka dasa su a wajen, sbd sun tabbatar yau ba lafiya ba,sbd dawowar bababi,gashi kuma basu ga shigowar yar lelensa ba,and kuma ga yanayin dasuka ga nawwara ta shigo bata cikin hayyacinta!!
ganin yana k'ok'arin fita ne yasaka marwan daga murya yace "baba dan allah karka bar bababi yafita" a lokacin dayake warming na motar,
hakan ko akayi ruf yarufo k'ofar yana k'ok'arin rik'e bababi amma yana zilllewa cikin d'imaucewa da tashin hankali shi abarshi yafita harda hawayensa kamar ba babban mutum ba duk ya susuce!
suna zuwa bakin gate musa ne yafito yakama hannun mahaifinnasa cike da tausayinsa yasaka shi cikin motar,yana jinjina soyayyar dake t'sakanin mahaifinnasu da kanwartasu!!
baba mai gadi ne ya umarci d'an nasa da zasuyi sa'anni da marwan kan yashiga motar shima ko zasu buk'aci taimakonsa,hakan ko akayi musa na gaba,bababi da _ABDUL-BASID_ kuma suna zaune a gidan baya!
baba yusufa ya wangale masu gate yana masu fatan adawo lafiya,marwan ya fisgi motar a 360! (kunsan cewa gudu da mota a gurin sojoji k'aramin abu ne sukam,idan basuyi ba sam basajin dadi,_garin haka kuma suka murt'suke napep dawata yarinya a ciki har yayi sanadiyyar mutuwarta a gaarin damaturu_ karfa ace nacika gulma dayawa yasin🙈😂🙈)!
cikin mintuna 15 suka iso inda accident din yafaru,wanda zuwa wannan lokaci mutane sunyi yam akan motar tasu,an samu nasarar fito dasu dak'yar,kamar matattu babu marabarsu da gawa,wanda mutane da dama ma kallon matattu suke masu kaawai tabbatarwa suke jira ayi!
fuskarsu ma idan baka masu cikakken sani ba,ba lallai ne ka ganesu ba!! sbd yadda tabi ta lalace gaba daya,ga sassan jikinsu dasuke jike da jinin jikinsu sharkaf...! duk wanda yaga yanayin dasuke ciki a daidai wannan lokacin koman rashin imaninka saika tausaya masu!
a kid'ime sukayi kan jama'ar dake zagaye dasu a gurin,kowa yanata tofa albarkacin bakinsa!
wani uban salati mai tafe da tashin hankali bababi yaja a lokacin da yayi tozali da yar tasa,kuka yake riris riris kamar ransa zai fita bayan ya k'ank'ame hamdeeyerh da babu alamun rai a tattare da ita!!
hankalinsu marwan ba k'aramin tashi yayi ba,ganin halin da yar uwar tasu take ciki,gakuma yanayin da baban nasu yake,wanda zuwa yanxu bababi ne yazama abin kallo a gurin mutane a mat'sayinsa na babban mutum!
abdulbasid ne daya daskare a gurin sbd t'sant'sar k'ara t'soracewa da hukuncin ubangiji! d'azunnan fa yaga hamdeeyerh da k'afafunta lafiya qlaou ta fita ammaa ga yadda allah yamaida ta cikin k'ank'anin lokaci cikin hukuncinsa!!
cikin mutanen ya kut'sa yakamo abba da k'yar ya b'anb'aresa daga jikin gawar hamdeeyerh dayake ta zurmuk'a uban kuka na fitar hayyaci!!
marwan gawar marak'isiyyerh ya dauka ya dumfari motar wani mutum dashi dayace asaka su aciki,kasancewar motar tasa mai dan girma ce,aciki ya shinfid'eta,musa kuma ya dakko hamdeeyerh aka sakata itama cikin mota sannan mutumin yazauna a zaman banza shikuma marwan yabama motar wuta zuwa asibitin _N and FAM HOSPITAL_ wato asibitin nawwara,
inda musa kuma yashiga driver sead na motar dasuka zo,abdulbasid ma yashiga da bababi ajikinsa dayake ta zaginsa akan yasake sa,ai dama ya lura ba son yar tasa yakeyi ba shiysa bazai barsa yak'arasa wajen ta ba!
shikam bai dauki maganar wata babba ba,sbd yasan cewa baama cikin hayyacinsa uban gidannasu yake ba ne!!
mutane suka wat'se kowa na tofa albarkacin bakinsa a wajen da masu fad'ar alkhairi da masu fad'ar akasin hakan
《》《》《》《》《》
a haukace marwan yak'e tuk'a motar,cikin minti sha'biyar suka iso asibitin,baiyi wata wata ba fito yafara kwallawa nurses k'ira,aikuwa a 360 su kusan goma suka fiffito suma hankulansu a tashe,wayanda suja kasance suna a duty na daren yau!
ciccib'ar hamdeeyerh yayi ya dumfari ainahin cikin asibitin,sbd yadda yaga sun t'saya kamar statue suna kallonsu!
dayan mutumin kuma ya dakko siyyerh wanda duk jikinsu ya b'aci da jini zuwa wannan lokacin,sukam nurses rasa abinyi sukayi ganin yadda aka shigo masu asibitin,domin ko sam basusan marwan ba a yan gidansu doctor nawwara
har nurses din zasu shiga sai suka ga motar doctor nawwara yashigo cikin asibitin,aikuwa duk suka iyo kan motar domin tambayar lafiya take kalar wannan gudun acikin asibiti? ita da tace doka ce kar amata gudu da mota cikin asibitinta? amma kuma saisuka tarar da akasin haka,mahaifin madam da kaninta dakansa suka gani a cikin wani hargit'satst'sen yanayi,hakan ba k'aramin kid'imasu yayi ba!
k'asa suka zube domin gayda shi amma baibi takansu ba ya shige cikin asibitin hakan yasa duk suka rufa masa baya,emergensy ya nufa sbd hango su marwan da yayi a bakin wajen a t'saye sunci birki!
ganin haka da nurses sukayi suka tabbatar tafiyar su daya aiko babu b'ata lokaci suka karb'e su deeyerh suka shige dasu ciki,wasunsu kuma suka had'o masu kayan aiki da duk zasu bukata dik da ma dai basuga alamun rai tattare da yaranba!
saida aka had'a komai aka rufo k'ofar emergency aka barsu bababi da safa da marwa a cikin ward!
abdulbasid ne ya naimi alfarmar abasa key na mota domin zuwa gida dauko masu abinda zasu buk'ata sbd yaga yadda jikinsu duk yab'aci da jini daga su har bak'on mutumin daya taimake su a motarsa!!! musa ya mik'a masa shikuma cikin hanzari ya karb'a ya fito ya tada motar ya fice!
yana isowa gida boise quaters na da zai samu iyayensa yayi sbd ya tabbatar suna can suna zullumin dawowarsa,aikuwa hakanne yana shiga ya iske su su uku sunyi jugum jugum,ga mahaifiyarsa ,mahaifinsa da kuma kanwarsa raihanatu suna zaman jiransa,ganin yadda yashigo cikin jini sai abin yabasu ts'soro inda duk suke tambayarsa cikin kid'ima akan mai yafaru? nan yazayyane masu duk abinda ake ciki da kuma abinda yadawo dshi gida...
share plssssssssss and follow me on wattpad @ ummie2018
vote
comment
share_UMMIEN2018_💜
YOU ARE READING
HAMDEEYERH!
Historical Fictionlabari ne mai cike da sark'ak'iya,idan kuna bibiye da alkalamin ummie2018 zai warware maku zare da abawa