_*Typing*_💻
_*🌻🌻HAMDEEYERH🌻*_©️ *HIKIMA WRITER'S ASSO.🌻*
_Home of peace, joint of entertainment,to educate & to enlighten our reader's._
_LITTAFIN KYAUTA._
*MALLAKAR*_ummien2018💜__*marubuciyar*_
1- _AYSHAT(complted)_
2- _ZATOH(completed)_
3- _NUNA SO GABAN KISHIYA(completed)_
4- _TA'UMMU KA (incomplete)_
5- _NIGERIA KO NIGER(incomplete)_
6- _ANYA KUWA...?(rate book)_~and now~
7- _HAMDEEYERH_
_GARGAD'I! GARGAD'I!GARGAD'I❌_
_Ban yarda wata ko wani yajuyamin sigar labari na ba,koda kuwa kalma dayace! duk wannan ya aikata hakan a gareni zamu gamu a fadar mai sama!!_
*charpter 17*
Da kyar nasamu tayi shuru,sbd kukan fitar hayyacin danaga tanayi har abin yasoma bani t'soro,bayan ta nat'su ne,na t'sare ta da tambayoyin abinda yasameta cikin kuka...
"yau kusan kwana bakwai nake ganin abinda yake firgita min tunani na t'sakanina da ya adamu,ashe yaya adamu zai iya wat'si dani a duniyarsa har ya nuna cewa wata can bare zuwan wata biyu da d'auriya ta fini mahimmanci a gurinsa hafsat...?
can u imagine wai adamu a godon mu na sunna yake kwanciya da y'ar aiki na a mat'sayin karuwarsa ta cikin gida wanda hakan sam ba d'abi'arsa bace...? kuma idan na kuskura nayi masa magana yace a bakin aure na...? ashe dama da gaske ne da ake cewa duk mutumin daka d'akko shi daga inuwa kadawo dashi rana shi sai yayi k'ok'ari wajen ganin ya ingiza ka cikin rana fat'so fat'so...?"
takare maganar tana mai fashewa da kuka bilhak'ki,wanda a lokacin da za'a tono can k'ark'ashin zuciyata babu abinda za'a gani sai farar takadda kal mai shegen haske t'sabagen farin ciki...!
amma kuma duk mahaluk'in da yayi duba da fuskata sai acema ni nafi adamar shiga cikin t'sanani tashin hankali,koda kuwa kaine uban y'an bin k'wak'k'wafi na duniya!
kukan nima nafarayi cikin fitar hayyaci,ina cewa "allah ya isanki wlhi adama,adamu ba bazai gama da duniya lafiya ba,duk kalar fad'i tashi da mahaifiyarki tayi akansa dama zai iya cin amanar d'iyarta _bayan ranta_ ...? ki dubi kalar yadda mahaifinki yayi d'awayniya dshi wanda koni shaida ce akan ko ke baki samu kalar gatan da adamu yasamu ba daga babanki,amma yanxu an wayi gari babu su a _duniyarmu_ zaici amanarsu...?
lalle adamu ya d'akko da zafi,kuma ya d'ebo ruwan dafa kansa,sannan kuma kema ai da naki wautan,dan kawai yace maki idan kikayi magana a bakin aurenki saiki t'saya a cuceki a banza a wofi! auren banza auren wofi! shi adamun shi kad'ai ne namiji a duniya ko kuwa shine autan maza,da zaki t'saya wai har yana maki wannan isgilancin...? wlhi adama kin bani kunya sosai ba kad'an ba...!
sannan kuma tun ba yauba nasha fad'a maki namiji ba d'an goyo da zani bane amma kika bad'awa idanunki toka kikace min sam ba haka ba,kin yarda da adamu kan bazai tab'a wat'sa maki k'asa a ido ba,ai kuwa yanxu kin gani da idanunki basai an baki labari halin d'a namiji ba! saidai ke ki bama wani"
nakare maganar tawa cike da zigi,domin ko banni da burin daya wuce aure t'sakanin adama da adamu ya mutu a wannan ranar,ai kuwa nayi nasara,domin ko adama tayi fam,tahau kan maganata ta zauna kan lallai ayau zata koma mijinta ya saketa,bazata iya zama da mazi naci ba!
wani tunani ne ya gilma cikin k'wak'walwata a lokacin,(na tabbata muddin aure t'sakanin adama da adamu ya mutu a yau bazanyi farin ciki kamar yadda yakamata ba! zanfi so ace anayin komai a gabanta,ta yadda mugun hawan jini zai mata mummunar kamu,sanin danayi cewa babu inda kishin adamu bazai kai adama ya baro ba!),dan haka a lokacin ansan yadda zanyi na t'sara adama harta hak'ura da batun saki!
haka fa rayuwar gidan adama yabi ya tab'arbare,adamu da deejama zai shek'e ayarsu sukeyi,wanda bakomai bane hakan sai aikin sihiri (kunsan ance sihiri gaskiyar meshi),domin ko duk saida boka ya mantar dasu allah dakomai suka t'sunduma wannan aikin!
ga uban rashin kunya da deejama ke ganawa adama a gidan, duka ! zagi! hantara babu wanda adama bata fuskanta daga gurin adamua da deejama a wannan gidan,ta koma kamar itace ma y'ar aikin ba deejama ba! wanda ba kowa bane silar faruwan hakan ya saini!
inda allah ya tak'aita abinma gaba d'ayansu yaran suna makarantar kwana hatta da musa wanda yakasance d'an autan adama,suna torkish kaduna,wanda tun daga pre-nursery yaran gidan kan fara makarantar!,duk wannan bad'akalar da akeyi basu da labari!
duk mai imani idan yaga adama a wannan lokacin sai ya tausaya mata amma bandani,da zuciyata ta gama k'ek'ashewa da d'aukar fansa,ko d'igon tausayin ta babu cikin zuciyata!
kwat'sam aka wayi gari adama ta tashi da ciwon hawan jini da yayi mata mugun kamu! abinka ga aikin sihiri da bai tab'a zama dindindin jikin duk wani musulmi asirin jikin adama da deejama ya karye wanda sam bani da labari sbd laulayin k'aramin ciki daya sakani a gaba!
kalar tashin hankalin da adamu ya shiga a lokacin da yadawo hayyacinsa ma b'ata baki ne,yabi ta susuce gaba d'aya ya t'sagwami kansa,wanda yara abinda ya hau kansa ta t'suga wannan b'aran b'aramar tunda sai basusan cewa aikin sihiri bane!
deejama kullum cikin kuka take da bama adama hakuri akan abinda suka mata kan wlhi wannan ba halinta bane,wanda haka yayi tasiri a zuciyar adama harta fara jin tausayin mijin nata da kuma y'ar aikin nata! wanda itama kanta sheda ce kan mijinta ba fasik'i bane,wannan d'imma k'addara ce ta auka masa da y'ar aikin nasa!
zaman gidan dai gashi nan yakoma k'adaran k'adahan,babu hayaniya babu hantara,kullum adamu naiman hanyar da zai wanke ma matarsa bak'in fentin daya shafa ma zuciyarta yakeyi,kuma yaci nasaran hakan!
har yanxu kuma babu wani daga gidansu deejama daya zo daga k'auyensu na mazigai,wanda hakan ba k'aramin d'aga mata hankali yayi ba! sun shirya da adama kan zasuke k'auyen nasu domin a dubo ko lafiya aka jisu shuru,deejama tafara wani kalar jinyar daya matuk'ar d'aga masu hankali, d'aga adama har adamu,!
basuyi k'asa a gwiwa ba suka dumfari likita inda gwajin farko yashaida masu ai deejama nada shigar juna biyu har na t'sawon wata biyar...!!
wanda hakan ba k'aramin girgiza zuk'atansu yayi ba baki d'aya,deejama ta buk'aci a zubda cikin amma sam adama da adamu suka hana kan kar aje garin naiman gira a rasa ido,badan taso ba saidan ba yanda ta iya ta hak'ura taci gaba da rainon cikinta da taimakon adama!
marwan,nawwara,faruq da musa duk sun dawo hutu har suka koma basu fuskanci komai ba a gidan,marwan 12-13yrs,nawwara 9-10yrs,faruq 7-8yrs sai kuma musa 6yrs dayake nursery 3!
na sauk'a lafiya inda na haifo d'iyata mace ranar suna taci suna marak'isiyyerh,
komawarsu marwan makaranta cikin deejama keda wata7 ,bayan wata biyu kuma ta sambad'o kyakkyawar yarinyarta mai kama da adamu hak kamar yayi kaki,saidai kuma yarinyar ta d'akko hasken mahaifiyarta!
ba kowa nace wannan yarinyar face _*HAMDEEYERH*_ !
a daidai wannan lokacin kuma allah yayi ma deejama cikawa batare da ta k'ara had'uwa da yayanta ko d'aya daga cikin danginta datake yawan ambataba...!
vote
comment
share_UMMIEN2018_💜
YOU ARE READING
HAMDEEYERH!
Historical Fictionlabari ne mai cike da sark'ak'iya,idan kuna bibiye da alkalamin ummie2018 zai warware maku zare da abawa