Hannah part 1

1.5K 69 3
                                    

💥 *Hannah*💥
   
         0️⃣1️⃣

*Maryam Abdullahi(Oumramadan)*
Whattpad@OumRamadan1

*Bismillah hirrrahmanu raheem*
*Alhamdulillah ina godiya ga ALLAH daya bani ikon kammala buk dina ga ni kuma dauke da wani sabo ,banyi dancin zarafin wani ko wataba haka wannan littafin kirkirarrene idan kinji yayi shige da baki lbr to akasi aka samu,idan da hali zan ringayi muku typing kullum idan ba hali kuka za,a ringa tsallaken kwana 1 Idan naga ruwan cmmnt har 2page zan ringa muku lol😅thanks*

_Na sadaukar da wannan littafin  gareku mutanan kirki masu halin halin kirki daban kuke a wajen oum Ramadan ina muku son so fisabilillah_

*Sadnaf*
*Mum irfan writer (cakwakiya)*
*Rufaida Omar (dan adam)*
*Aunty bilki*
*Aunty sadiya*
*Bloody aysha and khadija (ALLAH ya kawo miji nagari)*
*My auntyna ,aunty khadija (kuduba)*
*Kawar kirki fatima(special)*
  _Gaisuwarki daban take uwata abar alfaharina (mama rabi,atu) ALLAH ya kara miki lfy ya sadaki da annabin rahama ALLAH ya jikanki badan kin mutuba ya haskaka kabarinki_

Tukwici gaduk masu suna *Rabi,atu*

A nutse yake taka step din matattakalar benan,sanye yake da black suite  hannunsa rike da briefcase, fuskarsa tasha gyara  sajensa ya kwanta luf luf abinda sha,awa , tsintiyar hannunsa daure take da wani tsadadden agogo sai daukar ido yake ,daga yanayin yadda yake taka step d'in zaka fahimci gwarzon namijine ,
  Matar dake zaune a kayataccen parloun daya gaji da haduwa kallo d'aya zakai mata ka fahimci hutu da jin dadi sun zauna mata farace tass  fulanin usul kyakkyawa me kimamin shekara 50 sai dai kwata kwata bazakace takai hakaba ba saboda jin dadi da hutu da ya zauna mata,  k'arar footstep dataji a stairs  yasa ta d'aga kai  tanabin matashin saurayin dabai wuce 30yrs da kallo ba, lokaci ďaya ta saki murmushi tanabinsa da kallo harya k'arasa sakkowa,kana kallansa zaka hango tsananin kamar da suke banbancin haske da matar ta fisa danshi kalan fatar jikinsa chocolate ce me haske sosai ,
  D'an ranķwafowa yayi ya kama hannun matar cikin nutsuwa ya sumbata cikin cool voice d'insa yace "sabahul khairi ya mamii"
  Murmushi matar tai ta shafa kansa cike da jin dadi tace "aliyu haydar ya tashi lfy"  jinjina mata kai yayi yana d'an taune lips d'insa ,matar ta sake murmusawa tace "toh ga breakfast dinka can a dinning tun dazu daddynku ya fice yace akwai meeting din da za suyi da baki,"
  6ata fuska yayi yana duba agogon dake d'aure a hannunsa can d'an girgiza kai a hankali yace "mamii nayi latti ltr innaje office nayi a can"
  Mamii ta mike a hankali tace "toh bari na zuba ma  saika wuce dashi,make sure ka tabbatar kaci dan nasan halinka dak'in abinci"
  Bata jira cewarsa ba ta wuce kitchen, jim kad'an ta fito dauke da kwando data shirya masa breakfast d'in a ciki ,kar6a yayi a hankali ya sake yi mata kiss a hannu sannan yace "mamii na wuce"
  "Toh ALLAH ya tsaremin kai a duk inda kake "  cikin jin dadi ya amsa kana ya fice d'aga parloun,
  Da sauri sauri matashiyar budurwar take saka safarta  bayan ta zura gogaggun uniform d'inta sai kamshi budurwar take ,murd'a handle d'in kofar akai wata kyakkyawar budurwa ta leko da kanta tace "hanna kefa nake jira tun dazu me kika haka tun dazu kinaso kisa na makara"
  Wacce aka kira da hanna ta juyo da cute face d'inta  masha ALLAH na furta kyakkyawa ce fara tass da ita ,idanunta dara dara dan sosai tafi waccan budurwar kyau ,  turo baki tace "to aedai ganinan ko"  tana gama fad'a ta zura hijab d'inta,
  Tsaki budurwar tai ta fice hanna ta murguda baki tabi bayanta,
A dining ta sami budurwa harta had'a tea ta zuba Irish tanaci jan kujera hanna tai tace "yaya basma Aunty fa?"
  Sai da ta had'iye dankalin datasa sannan tace "tana bedroom "
"To ina yaya bassam"
  Hararta tai tace "kin kuma isheni haka"
  Murguda baki tai itama ta fara breakfast d'in,suna gamawa bedroom d'in mahaifiyar tasu suka shiga tana zaune bakin gado tana lissafi suka shigo hanna ta fad'a jikinta a shagwab'e tace "ina kwana aunty" 
Aunty tace "lfy lau auta kin tashi lfy, kun kusa makara yaufa"
  Basma tace "eh wlhy gashi nan da 30mnt zan shiga lecture " aunty tace "toh maza ku wuce ,ga kudi can akan madubi ku d'auka ALLAH ya tsare"  godiva sukai mata bayan sunyi addu,ar fita as usual kamar yadda mahaifiyar su take umartarsu ko yaushe sannan suka fice,
A parking space suka tadda fannah tsaye da uniform d'inta irin na hannah sak ,dai dai lokacin shima ya k'araso parking space d'in ,hanna tana ganinsa ta shige mota da sauri ,
  Basma da fanna had'a baki sukai sukace "yaya haydar ina kwana"  sai ya bude mota ya shiga sannan a takaice yace musu "lafiya"
  Hanna ta kyalkyale da dariya sanda suka shigo motar tace "kai amma dai ALLAH ya kara muku"
  Fannah ta watsa mata harara cike da jin haushi  tace "da akai me ? Naga dai ya amsa ko"
  Hanna tana dariya sosai tace "nidai banga sanda ya amsa ba gsky"  fannah tace "keda baki gaidashi ba ne bakiji ba mu munji"
  Basma ta hararesu tace "waiku duk sanda kuka had'u sai kun sawa mutum ciwon kai,to duk kumin shiru"
  Shiru fannah tai hanna kuwa sai da ta murguda baki sannan tai shiru,haka har suka k'arasa skul d'insu bayan an sauke su hannah driver ya wuce da basma Yusuf maitama sule university,
  K'arfe 1: na rana driver yayi parking a k'ofar skull d'insu hannah tare suke da kawarsu zahra ajinsu d'aya ,sai da suka shiga mota hanna tace "driven dazai daukeki bai zoba?"
  Zahra tace "eh mota zan hau bashida lfy shiyasa mum tace na hau napep"  fannah tace "ki shigo sai mu rage miki hanya"
  Zahra batai musu ba ta shigo sai da driver taga driver zai baud'e hanya sannan zahra tace "a saukeni anan saina k'arasa"
  Hanna ta harareta tace "ai baki isaba yau sai kinje gidanmu"
  Zaro ido zahra tai tace "nidai gsky aa in mum dina taga na dad'e fa"  fannah tace "bazaki d'ade ba ruwa kawai zakisha a maidaki gida"
  Shiru zahra tai har suka k'arasa gida ,hon yayi me gadi ya bud'e masa k'ofa,
  Zahra  bude baki tai tana kallan katon gidan da yake dauke da part har 4 ga shukoki na kayatarwa da suka malale tsakargidan cikin mamaki zahra tace "dama baku kad'aine a gidan kuba"
  Hanna tace "eh gidanmu gidan family house ne, asalin iyayenmu haifaffun kano ta dabone  su 4 iyayensu suka haifa dukkaninsu ALLAH yayi musu rasuwa hakan yasa su zama waje d'aya sbd zumuncinsu yafi karfi,waccan part d'in na big daddy Alhaji Abdullahi(big daddy), matarsa d'aya haj rabi(mami) da yaransa biyu yaya haydar sai yaya mus,ab, sai waccan part din nasu fannah su 3 iyayensu suka haifa Alhaji Aminu(small dad) da  haj Khadija(mum) , yaya farouk shine babba sai aunty maryam tana aure a abuja sai fannah, waccan part din kuma na alhaji Usman(papa) da matarsa d'aya haj aisha(mama) d'ansu d'aya yaya sameer amma suna zaune a lagos sai sunyi Hutu suke zuwa nan  sai part d'inmu da yake karshe mu uku iyayenmu suka haifa sunan mahaifina alhaji Yusuf (abba) sai mamanmu maryam muna ce mata aunty yaya bassam shine babba a sai yaya basma saini auta, "
  Zahra tace "cab nazata fa mamanku d'aya da fannah  naga kuna kama"   hanna tai dariya tace "abbansu wan abbanane ,da matar big daddy da mum na duk family d'ayane ya da kanwane "   fannah tabe baki tai tace "nifa yunwa nakeji kuzo mu wuce ciki"
  Zahra ta juya tace "gsky bazan shigaba, nazo in wuni wataran bye friends"
Bata jira cewar suba ta fice daga gidan,hannah ta d'aga kafad'a ta nufi part  d'insu,fannah ma part d'insu ta wuce cike da rashin jin dad'in abinda kawar tasu tai musu,
K'arfe 6 na yamma hanna ta sauya kayan jikinta bayan sun dawo daga islamiyya ,parlour ta dawo ta tadda aunty da bassam suna hira , zama tai cikin shagwab'a tace "yaya bassam shine ka fita banganka ko?" Bassam yayi dariya yace "parrot duk yadda akai akwai abinda kikeso "   hannah ta murmusa tace "eh yaya bassam kamar ka sani "  sai ta kwa6e fuska tace "ALLAH kwana biyu banci burger ba "
  Aunty ta tabe baki tace "abinda kika iya kenan ai kwad'ayi,ga kaya can maza ki kaiwa mamii"
  Tashi tai tana kallan bassam kamar zatai kuka, murmushi yayi yace "anjima zan taho miki dashi shikkenan "
Dariya tai har saida dimple d'inta ya lotsa tace "shiyasa nake ji dakai yaya bassam"  tana gama fad'a ta fice bayan tad'au aiken da aunty tai mata,
    Cikin sanyayyar muryarta me zak'i tai sallama a parloun,haydar ta hango akan dining yana danna loptop sai da ta hararesa sannan tai k'asa da murya tana turo baki tace
"Yaya haydar ina wuni "
D'ago da kansa yayi  ya watsa mata harara,turo baki tai ta haura upstairs da sauri ta shige bedroom d'in mamii,
  Haydar kuwa tsaki yayi dan sarai dazu ya ganta sanda ta shige mota yarasa meyasa hanna ta rainasa shiba gwanin wasa da yara ba ,kwafa yayi ya cigaba da danna loptop d'insa,
#Vote
#commt
#share
#oumramadan

HannahWhere stories live. Discover now