chapter 3

14 2 0
                                    

🌀🌀🌀🌀🌀🌀
*UWAR MIJINAH*
~{Hawan jininah💔}~      
🌀🌀🌀🌀🌀🌀
                NA
   *🤍Fahnaan🤍*

_MARUBUCIYAR: MA'ESHERH(ANNOBA)_
       
©🎆
*AL'UMMA WRITER'S ASSO...* ✍🏻
  _A• W• A•_
_{Al'umma writers, Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane gsky al'umma sai dan Al'umma, Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}._
 
بسم الله الرحمن الرحيم...

         *Chapter  3*

Glass cup din dakedake hannunta ya ku6uce ya fadi, Nan danan ya fashe ji kake tangarararar...

    Firgigit suka dawo cikin hayyacin su , Suka waiga Saitin da suka jiwo Kara,

    Tsoro, Firgici, da kunya duk suka hadu suka Dabaibaye su gabaki daya

   Aryaan ya sunkuyar da kai yana Dan Sosa Kai Yace "Ehm,Umma Kin tashi lafiya?"

    "Ah Sannu Mara kunya, nace Sannu ba, Ai kai ne da Sannu, Ka tashi lafiya?....baka amsa ni ba nace ka tashi lafiya?, ko da yike Ba abin mamaki bane Dan in kana tare da yar boko zakayi fiye da haka mah " Ta kalleshi, Yayi tsaye yana kallon ta tace" zaka 6ace min da gani ko sai na sa6a maka"

  Ya wuce sumi-Simi kaman wani Mara gaskiya.

  Ta juya da kallon ta ga Ramla wacce ta kame wuri guda zazzaro  Saboda tsananin tsorata da tayi "Look young lady, kar ki Ga ina Hana miki Wasu abubuwa kiyi zaton bana sonki ne ko kuma ina son takuraki, To ki bude Kunnuwanki kijini da  Wannan mijin naki dakike lilliqe mawa Hoto ne dashi da babu duk daya, ina nufin ko kun kasance tare bazai iya ta6uka miki komai ba, dana nakasasshe ne baya haihuwa"
Da sauri Ramla ta dago Ta dube ta a tsorace,  lokaci Guda heart Dinta yayi beating, tadafa kirji tana adduar Allah ya tasheta daga mummunar mafarkin da takeyi😭
     Muryan Umma taji tana cewa "Gara ma Tun wuri kisan yanda zakiyi Tun bai gama dake ba,Dan ko shi bai San da lalurar nan ba"

    Kasa jure maganganun Umma tayi ta haye sama da gudu tana hawaye mai sauti
    Umma tabita da kallo ta kwashe da dariya "Yarinya kadan kika gani, indai ina Raye dana bazai ta6a kusantar ki ba , jibeki fa wata bunsura dake Mtsswww aikin banza"

    *****
Aryaan kam ya na fita kai tsaye parking space ya nufa ya shiga mota ,ya jingina da backseat din motan yana tunanin mafita akan Wannan sarkakiyan
  Shawara ce ta fado mishi ya  kira Abokin Shi Hilal, Ringing daya ya daga kafin yayi magana Hilal ya rigashi "Ango kasha kamshi , Kar kace min har kun tashi"
  Aryaan ya katse shi da cewa "See you ,ni fa yau idona biyu ban ritsa ba Dan bacci gagarana yayi"

Hilal yayi dariya "Ai dole ne ,An kwana ana Raya Sunnah..."
"Mtsww, Raya sunnan ko Raya tension"

   "Ai dole ta baka tension, Nima Allah ya bani wata tayi wuf dani nima na  raya Tension😆"

"Amma dai Anyi  Soko anan, nifa ba irin wannan Tension din bane nawa, ni Tun da aka kawo min Amarya ta ko hannunta ban ta6a rikewa ba sai yau da safe .................. Nan ya labarta mishi Abinda Ya faru

    Hilal yaja Dogon numfashi yace ai in Dan wannan ne ai me sauki ne " bude kunnenka kaji ya zaka yi " Nan ya fada mishi yanda zaiyi( Meye na kallo na kuma?, nifa banji abinda Abinda ya gaya mishi ba😒)

     Duk suka kwashe dariya Aryaan yace"Amma fa kai Dan iska ne,duk Salon yaudara kai ka'iya, Allah ya barmun kai Buddy, "

Hilal ya amsa da Amin Suka cigaba da hirar su cikin So da kaunar juna

     Karfe 2:30pm muka fito daga  lectures Nida hafsah da Jannan Muna Dan taba fira Dai dai wurin mai café Muka ga Ks daud yana zuba takardu cikin Wani Envelope,

    Na kalle Su Hafsah nace "Gafa mutumin mu"
Jannan ta rage murya cikin Alamun rada tace"Ke Lower your voice yana jin mu fa"

"Harararta nayi nace" To yayi ta jin mu mana ni ina ruwa na?, Nasan ko yajini Babu abinda ya isa yamin Wanda ya wuce ya bani CO kuma in CO ne a rigar kowa take, idan ka shigo Uni kafita baka ta6a samun CO ba to ba karatu kayi ba your are just moving around ba karatu kike ba"
A dai-dai lokacin gama kwashe takardun ya juyo yamin wani Shu'umin murmushi Ya kadai kai ya wuce
   Kallon da ya min yasa gabana faduwa, Tsoro da fargaba suka dira min a zuciya, Muryan Hafsah naji tana cewa "Yau mun Shiga Uku kashin mu ya bushe ,Nasan wlh babu Mai raba mu da Ks sai Allah" ta karashe magana kaman zata yi kuka

   Harararta nayi tare da turo baki gaba " Matsoraciya kawae Wa ya gaya miki hakan?,  Nifa yunwa Nike ji , Abege let's Go''

Daga nan babu Wanda ya kara magana kowa da abinda yike saqawa aransa.
   A mota ma haka ta kasance kowa yayi shuru babu mai magana duk cikin mu Ganin shurun yayi yawa yasa na Kunna Sauti nace "Jaan kar ki bani kunya mana ban sanki da tsoro ba,Na kalle hafsah wannan Abin itace matsoraciya a cikin mu, koda Mr Ks zaiyi mana Abu bai kamata muji tsoro ba , kin manta yanda mukayi Wa Malam Suleiman Oga lab din mu kenan ?"

  Jannan tayi yar dariya "Ni Wa yace mike ina tsoro?, Aa ni Dan naga kinyi shuru ne shi yasa ni kama baki na"
Daga nan fira ta 6arke a tsananin mu har muka isa gida

    
    A falo muka tadda su sunyi jugum-jugum yaya Aryaan yana zaune yana latse latsen waya Ramla kuma tana kallon Tv Umma na tsakiyan su ta wani hakimce a kujera,
  Ai bansan lokacin da dariya ya kubce min ba na shiga darawa harda rike ciki, Duk suka waigo suna kallo na harda su hafsah
     Ganin na kure su da kallo ina darawa yasa yaa Aryaan fahimtan abinda yasa ni dariya , Ya banka min harara nima na rama harda murguda baki , Ya min Alama da ido zan kamaki yarinya ,
  Na karasa na zauna kusa da kujerar su na wage murya ina fadin "Umma nifa ban gane ba kurame kuka zama ne?"

Kafin Umma tayi magana har hafsah ta rigata da fadin  "Uhm Umma ki kyale yarinyannan duka take so....,Nifa  yunwa Nike ji babu abinci ne a gidan?"

Nace "Food monger, ba yanzu kika gama cin abinci ba?"
Tace "kuka gama ci dai"

Muryan Aryaan ya katse mu "Enough!, Kun Shigo mana gida babu ko sallama balle gaisuwa kun  wani ishe mutane da surutun Tsiya"
    Hafsah da Jannan suka gaida su niko turo baki nayi nace "Wlh babu uban da zan gaidar,Ai da na shigo da harara aka fara tarya na"
Na kalle Ramla nace "Anty Ga Qawas  fa Tazo cin cin-cin ne"

Tace "Ayya Sannu kawarmu ya sunanta"

Nace "Jannan sunanta amma Nida hafsah muna kiranta jaaan",
Wow Jannan  nice nameTo sannu barina debo maku
   Umma ta tashi ta shige daki nabita da kallo ina ta6e  baki
Yayinda Ramlah ta mike ta nufi Daki Dan Dibo mana cin - cin
   Na kalle yaa aryaan dake ta faman latse waya nace " Mutun ya wani kanainaye a tsakiyan mata ko kunya bayaji*
  Sarai yasan dashi Nike amma sai yayi min banza

     Sharenin daya yi ya ta6a ni sosai sai na cire takalma da mayafina  na cilla gefen ShiShi ....

Manage pls🖋️

MASU SHARING A GROUPS GODIYA DUBU A GARE KU

MASU KARATU BASU COMMENT KAR NIKE KALLON KU😎

MASU ZUBA MIN SHI (COMMENT BA) INA YINKU IRIN TOTALLY A CIGABA DA ZUBASHI😁







Duk wacce comment dinta tafi burgeni next chapter nata ne💃💃💃

Share
And
Comment

Bye

Fahnaan🖋️
12august2k20

HAWAN JININA (Uwarmijina)Where stories live. Discover now