chapter 19

9 1 0
                                    

🌀🌀🌀🌀🌀🌀
     *HAWAN JININA*
     ~{UWAR MIJINA}~      
🌀🌀🌀🌀🌀🌀
                NA
   *🤍Fahnaan🤍*

_MARUBUCIYAR: MA'ESHERH(ANNOBA)_
       
©🎆
*AL'UMMA WRITER'S ASSO...* ✍🏻
  _A• W• A•_
_{Al'umma writers, Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane gsky al'umma sai dan Al'umma, Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}._
 
بسم الله الرحمن الرحيم...

Oh ni 'ya su!! wannan ruwan comments haka ai saiku sa Ummah ta yankomin sammaci,to dai Alhamdulillah naji Dadi kwarai da Gaske Kuma Ina godiya ga addu'oinku gareni love yhall* 💖

    *_Chapter 19 _*

Aaryaan Na dawowa ya Ajiye Ledar da ya Riqo Sannan ya Ajiya,sannan yaje kitchen ya wanko ,Plate da Cup,Sai a lokacin Ramlah ta Fito daga Toilet Shima ya Shiga yayi wanka.

Tana Zaune akan Rug har ya Fito yana Goge jikinshi da Towel, Ta kawar da kai tana murmushi, A zahiri Fuskarta babu yabo babu Fallasa Amma Abadini bazaka So Kaga yanda Gabanta ke Faduwa ba.

Tunani takeyi Akan maganGanun Umma na jiya Da kuma na Ranar nan da ta Gaya mata ,ta rasa Gane inda maganar Ta  ta dosa ,

Saukar Ruwan da taji A Fuskarta ne yasa ta dawo daga duniyar Tunanin da ta shiga ,Ta Dago ta kalleshi yayi mata murmushi Yace " Tunanin me kikeyi ne?"

Tayi murmushi kawai ba tareda ta bashi Amsa ba

Ya jawo ledar da ya Shigo dashi,Gasassun kajine da Fresh Milk mai Sanyi..

Sannan ya zuba kajin cikin plate, ya kuma Zuba Fresh milk Cikin Cup

Saida Sukaci Sukayi nak Sannan Suka Dauro Alwala .

Yana gaba tana bayansa suka gabatar da sallah raka biyu  Wanda Annabi Muhammad (S A W) ya umurce mu da muyi a darenmu na farko."

Bayan sun sallame sallah ya dafa goshinta yayi Addu'a suka tofa gaba d'ayansu.

Daga nan na fita na ja msu kofa.

          ****

A Gida kuwa Umma in hankainta yayi dubu toh ya Tashi ne, Tunda taga Anyi magrib su Aaryaan Basu dawo ba ta Shiga TO AND FRO a Tsakar parlor ita kadai kamar Wata Tsohuwar mayya

A   A haka muka Shigo muka taddda ta Hafsah tace"Umma lpy kuwa na ganki ke kadai kina Zirya ko kina Neman wani Abu ne?"

Umma tace"Auta Ina Aaryaan ya tafine Tun da safe ina ta kiranshi bai Daga wayan ba, inaji a jiki na babu lfya fah"

Hafsah tace "Toh fah ,Ai gidan su Aunty Ramlah ne,Amma bari na kira numbern shi Inji?" Ta fada tana Fito da wayarta

Fizge wayar nayi ina Hararar ta "Wlh babu Wanda Zaki kira,Shi Aaryaan din Yaro ne?, Da har zaa yi cigiyarsa Sbd ya uni bai dawo Gida ba?,Da ace Wata qasar ya tafi Binshi zakiyi kenan, Mtswwwww" naja wata doguwar tsaki Tareda Jan hannun Hafsah muka bar wajen,Kai tsaye dakin mu muka shiga,ina wani Huci kaman Wacce tayi fada da Zaki

~Na tsani takura ko maqiyi na banason A takura mishi Bare kuma jinina~

Hafsah ta katse min Tunani da cewa "Nayfee, ya kamata Kisan irin maganganun da Zaki Ringa Faduwa Umma,Ko babu komai Ta ci Albarkacin Ita mahaifiyata ce mana!"

Hararar ta nayi nace"And so fucking what!?,Ni ta Haifa?, keda ta Haifa ke ya Shafa, kinga A Halin yanzu banida Uwa banida Uba bare inyi fargaban innayi zaayi Wa iyayena,So keda kike dasu Saiki datse damtse wajen Biyayyah ko Zaki Samu Aljanna ta wajen Su"

Na fada ina Miqewa, na Nufi Fridge na Dauko Apples da Strawberries dinda yaaAary ya siyo mn jiya na Dau Strawberries din na fita da shi, kaitsaye  dakinsu YaaJunayd na nufa nayi Sallama,Abdool da yaaJunayd suka Amsa sannan na Shiga na bawa Abdool Roban Strawberries din batare da nace komai ba har na juya zan fita najiwo muryan yaa Junayd yana cewa "My Rigimatu yau Aljannun Rashin magana ne suka kama mana ke ne?"

Batareda na juyoba Nace"Am just Feeling upset, Kuma bacci nakeji,Sai da safe" ina fadin hakan na banka kofa na rufe, Sukabi kofar da kallo .

WasaWasa Har 10:00pm babu su Aaryaan babu labarin su,Gabaki dayan mu munyi barci Ummace kawai take kai komo a Falo

Turo kofan da akayi ne ya sata maida hankalin ta ga mai Shigowa,Abba ta Gani Ya shigo

Ta ja Yar karamar tsaki ,Abba yace"Lfy Haleema daga Shigowa babu Sannu da zuwa babu komai sai tarbar tsaki?"

Umma ta Qarajan tsaki "Alhaji Wai ace Tunda yarannan Suka Fita basu dawo ba haryanzu ,ka dubi Agogo fa har Goma ta wuce"

Abba yayi dariya yace"Oh Wai Aaryaan?, Ai Kirani dazun yace Wai ankirashi Aikin Gaggawa,yanzu haka yana Zaria, yace Zaiyi sati Biyu Amma nace yayi zamanshi achan,Ai hakan ma mungode"

Umma ta dafe kirji tace"What!,Alhaji kana nufin ,Aaryaan ya koma Zaria da Ramlah kenan?"

Abba yace"Uhm?,Ko da matsala ne?"

Umma ta Dan Saita Natsuwan tana ta6e baki tace "Babu komai kawai mamaki Tafiyar nasu ya bani....,Sannu DA zuwa,An dawo lfy?"

Yace"Lfy ina yaran da Kakus?"

Tace"Duk Sunyi barci,Muje kayi wanka Sannan kazo kayi Dinner".......

A Ranar dai Umma batayi barci ba Kwana tayi tana kuka, Tasan Yau babu makawa Sai Aaryaan ya Kashe Arna🤨

_____
A can Barnawa kuwa Saida Aaryaan ya Saukema Ramlah Abinda ya tara Shekara da Shekaru sannan ya kyaleta, Har dare Suna manne da juna Sai A yau ne ya Tabbatar DA yayi Aure.


Wasa wasa Yau har Sati daya,Babu labarin Su Aaryaan ko a waya Umma ta daina SamunShi, Shiyasa ta kira kawarta HajiyaAsiya wacce take zaune a nan Zaria tace ta Aika a duba Gidan su na Zaria ko Suna nan,Amma Amsar dayace Baizo ba.

Ni kuwa Raina Fes,Addua ma nake karAllah ya Dawo mana da Mugu, Halayya na Nada na dawo dasu,Kaman Sa kananun kaya,Fitan dare da zuwa Bukukkuwanda baa Gayyace mu ba,Kuma na Kara Sa ma Yan Aikin Gidan ido,Sosai na takurawa kowa, babu mai kwa6a ta yanzunnan kakus DA Abba zasu hayayyaqo mar.

Su InnaRabi Kuwa Tunda Abin ya Faru ban Sake hada koda hanya dasu ba,Ko daga nesa Suka Ganni boyewa sukeyi,Amma fa Akwai Shirin da sukeyi Akaina Dan Haryanzu basu yarda Aljanun Gaske Gareni ba!

(Lemme laugh Small🤣).

Yau muke Shirye-Shiryen mu na koma School Gobe, don dama Hutun Christmas da NewYear ne ya tsayar damu,

YaaJunayd ya Kaimu ShopRite munyi Siyayya Sosai,Amma ni ban dauki komai ba illa Chocolates,Biscuits, Chewing Gums,LollyPops Etc.🤨

Su jaanaan kuwa Sune Siyan kayan kwalliya, kayan Sawa ne,Su Sarquna ne,Waya mutu waya tashi.

A Nan ShopRite din nayi Saurayi danWanka Wai shi Jeebril(Jeeboi), Janaan ce ta bashi number na ,Dan ni ko kula shi banyi ba,Gaba daya ya tafi da Tunani na, koda yake maybe Dan ban baa ta6a Gaya mn Ana sona bane.



Aikam nasha Tsokana wajensu Hafsah sai cewa take Wai naqi Yayanta Ga  wani yanason yayi Sama dani ya kwashi Raguwarsa


Ni Ban fahimci inda Zantukan nata Suka nufa ba,Duk dauka na Wani sabon Salon Tsokanan nata ne hakan.

Gaba daya na manta da na Rubuta a diary na kuma Nasan zata karanta Tunda a hannunta na gani,

Har muka isa Gida basu daina Tsokanar ba nima ban tanka musu ba ,Danne danne kawai nakeyi a waya na.

***

Ramlah na kitchen tana Soya dankali Aaryaan ya Shigo, ya Rungume ta tabaya yana Shaqar kamshin jikinta.

Yace"Priceless, Ki hada mana Loads dinmu,Zamu koma Zaria Anjima Inshaallahu, zamuyi Resuming Work Tomorrow "

Ramlah tayi murmushi Tace "Angama Ranka Shi Dade,Amma fa ya kamata ka bawa Yarinyar nan Motar ta ka Gyara naka, ina Tsoron hukuncin da zata dauka akan hakan, kasan bata barin bashi"

Aaryaan yace "Waya gaya miki hakan?,Idan Bata Barin Bashi meyasa har yanzu bata Rama dukan da nayi mata ba?, Meyasa bata Rama Wa Kaninta Yajin da mukasa ya sambada ba?,Meyasa bata Rama Uhmm"

Ramlah tace "Meyasa bata Rama me ba?"







No Dogon Turanci

A SAMBADO COMMENTS kawai

A cigaba da Wanke hannu.

Nayi Gabas🚶🏻‍♀️


31st Aug

HAWAN JININA (Uwarmijina)Where stories live. Discover now