🌀🌀🌀🌀🌀🌀
*HAWAN JININA*
~{UWAR MIJINA}~
🌀🌀🌀🌀🌀🌀
NA
*🤍Fahnaan🤍*_MARUBUCIYAR: MA'ESHERH(ANNOBA)_
©🎆
*AL'UMMA WRITER'S ASSO...* ✍🏻
_A• W• A•_
_{Al'umma writers, Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane gsky al'umma sai dan Al'umma, Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}._
بسم الله الرحمن الرحيم...
*Fatima da nana Juwairiyyah (Fahnaan) Wannan Page din namu ne🤪*_Chapter 17_*
Kawar da kaina nayi ina Ta6e baki, "Nifa babu Abinda ke damuna Yunwa kawai nakeji"
Tun kan na Rufe baki Kakus tace"Amarya A samo mata Abinda zata ci"
Mikewa Ramlah tayi har ta kai bakin kofa Sannan nace"Kice Wa Umma ta Baki Awarar da na sata Soya mn dazun"
Ramlah ta gyada Kai ta fita,Kakus tace inje in Rama Salloilin da Ake bina kafin Ramlah ta dawoBabu Musu na shiga Bayi na dauro Alwala Sannan na Gabatar da sallolin da Ake bina na Azahar,la'asar, magrib da Esha'i, har lokacin da na idar Ramlah bata dawo ba, A lokacin Har kakus tayi barci, Gyara mata kwanciya nayi naja mata bargo Sannan na fito Parlor.
Ramlah kuwa tana Fita ta nufi dakin Umma tana dar'dar a ranta Dan harga Allah tana mugun Tsoron matan nan,
Sallama tayi Umma ta Amsa kaman An mata dole, tana Tsaye Bakin Gado tana jera kaya cikin Cupboard,
Tana Ganin Ramlah tace "Yawwa karasa Jera min kayan nan,Ina zuwa" ta fada tana Ajiye Yar Rigar dake hannunta tare da Ficewa daga Dakin.Saida Ramlah ta Gama jera kayan a Cupboard sannan Umma ta shigo,ko karasa Shigowa batayi ba ta fara sababi Wai Ta Jera mata kaya in a wrong Place, waya mutu waya tashi, ita dai Ramlah Haquri ta bata Sannan ta Zube kayan ta kara Re-Arraging dinsu cikin Drawer, Tana Gamawa Umma tace Ta Share Mata dakin sannan ta Shimfida Mata GadoSai A lokacin Ramlah ta Sami damar magana"Umma Aikoni fa Akayi"
"Oh Dan An Aiko ki ni ban isa na aike ki ba kenan, ko?, To shike nan Tunda Aiken nawa ne baki so ki fice mn daga Daki ,dama ai ban ce dole kiyi ba"
Ramlah ta Girgiza kai"Haba Umma, wlh ko Fiye da haka kika Sani Aiki zanyi,Albarkacin dan ki danake Aure,ai ke tamkar Uwa ce a garenu, idan banyi Aikin da kika Sani ba yana nufin idan uwata ta Sani Aiki bazan yi ba kenan,Ai kinfi karfin Haka a gareni , Please and Please take it Easy,Ba cewa nayi bazanyi ba kawai inaso inyi delevering message dinda Aka Aikoni ne Sannan na cigaba da naki aikin, Please Umma Ki yi Haquri Idan nayi kuskure a maganganuna ,Please Ummah dama Kakus ce ta Aiko ni tace in Amso Awarar da kika Soyawa Munayferh, Ta tashi "Umma ta mere baki tace "Munafika ni zakiyi Wa dadin baki?,Eh ? Uwar taki wani daraja take dashi A idonki har kike Hadani da ita?,Ba anan kika Gama Cin mata mutunci ba a bainar jama'a harda cewa ta daina kirarki diyarta,ko kin dauka mun manta ne?, To Aradu ban manta ba ina iya tariyo maki Ranar da kwanar watar ,Wato Ashe nima bani da daraja A idonki kenan, Yo ai ba Abin mamaki bane Fitsararriya kaman ki tayi wa uwarta ma bare uwar mijin ta ,in banda Finkarfin da Aka mn Allah Bazan ta6a yarda dana ya Auri Fitsararriya irin ki ba wacce batajin Shakkar wulaqanta Uwarta,Aini Tunda ya Auroki nake Tashi Sallar dare Ina Addu'ar Allah ya tsareni Hada zuri'a da mara tarbiyya irinki"
Ta kalle Ramlah wacce tayi mata Kuri tana kallonta cikin Zafi da kunar Rai tace"Ki gaya ma kakus din nayi baquwa na bata Awarar"Ramlah ta gyada kai Sannan ta fice a dakin ,Tana fita Ta Rushe da Kuka bai man tausayi, batayi sa'ar iyaye ba Gashi kuma Tayi Aure Dan Ta huta Takaicin iyayen nata Ta hadu da Bakin cikin Uwar-Miji.Ina Zaune a falo ni kadai kamar mayya na kunna TV ina kallo naji Shigowar Abba da sauri na Ruga na Rungumeshi "Oyoyo Abbie na,Oyoyo Abba na"
Abba ya sumbaci Goshin na yana Rabani da jikinsa "Oyoyo Angel din Abba,Ina Auta nane?"Ban Amsa shi ba,Na Amshi Jakar dake Rataye a kafadan sa na Rataya a nawa kafadar Sannan na Turo baki nace"Shine Tun da ka fita baka dawo ba sai yanzu?"
Zai bani Amsa Ramlah ta shigo Falon tana Matse ido, fitowarta kenan daga dakin Ummah
Ta Gaida Abba ya Amsa yana kallonta "Amarya meyasami idon naki,Naga ya chanza kala?"
Nayi charab nace"Inaga kuka tayi Kila Ummace ta Zane ta kokuma ta Zageta Nasan baza'a Rasa cikin Dayan Biyu ba, kasan yanda Matar taka ta Tsaneta.....Uhmm, ni ba wannan ba ina Awarar da Nace ki kar6o min"
Abba yayi murmushi yace"Badai Duka ba dai "Sannan ya kalli Ramlah yace " Amarya Me ya Sami idon naki"
"Wani Abu ne ya fada min ,but Am Fine Right Now"
Yace "Allah ya kara Sauqi" ta Amsa da Ameen na bita da kallon Kurillah,Harga Allah ni ban yarda da Zancen ta ba Amma tunda Abba ya yarda Aje A hakan Bani Zan cutuba💁🏼♀️
Na Shagwa6e fuska nace "Aunty Ramlah Ina Awaran?"
Tace "Aff Na manta,Tace ta ba Wa baquwa"
Wani irin Zabura danayi na cire Bag din Abban da na Rataya A wuya na nace "What?,Me take nufi?,In kwana da yunwa kenan?,Wlh bazan Yarda ba” na fada ina Zaman Yan bori a kasa,na Fara birgima ina kukaDaga Abba har Ramlah Kallona sukeyi babu mai Rarrashina har saida nayi mai Isa na Ganin duk sun zuba min ido babu Wanda ya tankani ba karamin hasalani yayi ba
Na miqe ina Turo baki "dama na Sani,Ba sona Akeyi a Gidan nan ba , Saboda banida Iyaye kusa, Da ace daya daga cikin yayanku ne Na tabbata bazaku ta6a barinsu da Yunwa ba,Ni wlh bazan sake kwana a Gidan nan ba,Kuma idan na Fita bazaku sake Ganina ba" kuka nakeyi Bil haqqi da iya Gaskiya na na nufi Hanyar dakin mu
Kayana na shiga Sakawa cikin Dan karamin Trolley na kayana ina matsar kwalla,Saida na Gama saka kayan cikin Akwati sannan na tuna da Diary na ,Amma ban Wani yi Dogon bincike a kan inda yake ba.
Ina Saukowa parlour na Iske Abba da Ramlah,Harda Umma wacce Hayaniyan da nkyi ya Fito da ita
Wuce su nayi nabi Hanyar waje ina karajin Haushin Rashin Tankanin da Sukayi,kuma fa da zasu kulani da sunsha masifa😄
Ina Fita Gate na buga dakin mai Gadi yafi sau Ashirin Amma yaqi Kulani,Dan Abbie ya Riga ya kirashi yace kar ya bude mn Gate din.
Da na gaji da dukan kofar sai na Sami wuri na zauna ina Kuka tamkar marainiya, yaune Ranar farko da naji Son Ganin iyayena kusa dani, Haka kuma yaune Ranar farko da naji Qaunar iyayen nawa a raina, Na tabbata da suna Nan Babu mai hanani Abinci a gidann ~kin tambaya an hanaki ne?~🙄
Da wannan tunanin ne Baccin wahala Yayi Awon gabadani
Jin Ana Bugun bayana Ahankali yasana Ware idanuna A hankali,
Yaa Aarry na Gani Fuskar nan babu yabo babu fallasa"Ke Tashi ki shiga ciki"
Ina Ganin sa kuka ya Kwace min, na fada jikinsa ina kuka bai ban tausayi "Yaa Please Help me Find my Parents, Am missing them😭"
Jikinsa yayi Sanyi,Tausayi na ya kamashi, Yasa hannayenshi dukka biyun ya zagaye bayana,Wani irin Sanyi ya Ratsa ni jikina har Wani kyarma yakeyi
Saida yaga na daina kuka ina sauke Ajiyan zuciya Sannan ya Rabani da jikinsa,Yaga idanuna A lumshe Alamar Bacci ya Sace ni.
Chak ya dauke ni yayi ciki dani.
Tun Fitana daga Parlon Abba ya kira Mai Gadi a waya yace kar ya barni in Fita,yana Gama wayan ya juya ga Umma ya Rufeta da Fada Wai me yasa Zata Bawa baquwa,Sai kace babu Wani Abincin A Gidan? ,kuma ya ce taje ta kara Yin wani Awaran yanzun nan...
Yo Allah yaso Ba Duka ta juye ma baquwa ba sai ta Dauko Raguwan Ta kawo,A lokacin ne kuma Aaryaan ya Shigo Parlourn Yazo daukar matarsa🤪
Sai Abba yace ya duba ni A waje ko na fita ne.......
Manage🤪
~NOTE~
Alway observe Social Distance between you and Ur phone B4 Reading My posts😂
Don't Forget kusaka Takunkumin Rufe Bakida hanci kafin Ku karanta Littafin Ga
Acigaba da Wanke hannu
Nayi Gabas💁🏼♀️🚶🏻♀️
30th Aug
YOU ARE READING
HAWAN JININA (Uwarmijina)
ActionLabarin Uwarmijin da ta Takura Wa surukarta, daga baya Ta hada danta Aure da Wata Yar Uwarshi saboda wata 6oyayyen kudurinta ,Amma me?, sai Yarinyar ta zamar mata Raina kama..........