🌀🌀🌀🌀🌀🌀
*HAWAN JININA*
~{UWAR MIJINA}~
🌀🌀🌀🌀🌀🌀
NA
*🤍Fahnaan🤍*_MARUBUCIYAR: MA'ESHERH(ANNOBA)_
*kai kai kai gaskiya na fuskanci mutane ma sunfi son Munayferh Akaina , zan fa koma 'yar adawarta dan na fuskanci hmmmm bari dai kawai nayi shuru,Comments Dinku Na saani Farinciki I ❤️ u All*
~Sarah, Zainab Ali,Mum Ameerah, Hafsah Tukur and Da duk Fahnaan Novel member Wannan page din naku ne😘😘~
©🎆
*AL'UMMA WRITER'S ASSO...* ✍🏻
_A• W• A•_
_{Al'umma writers, Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane gsky al'umma sai dan Al'umma, Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}._
بسم الله الرحمن الرحيم...*_Chapter 9_*
"Da ya kiraki Sai Akayi ya" Malam manseer(HOD) ya fada cikin zaquwa.
"Shine Yace na bashi kaina,in kuma na qi,Zai Cire Sunana a course din gaba daya ko Sai dai ta maimaiawA har 400L, kuma Wlh da gaske yake ko yau Da na duba class list babu Sunana Aciki...." Ina kaiwa nan kuka yafi qarfina (kaman da Gaske🙄)
Ba Malam mansir ba harda Jaanaan zaro ido Sukayi suna Jan Salati
"Innalillahi wainna ilayhirrajiun,Sorry Munayferh, bi'izinillahi sai an bi maki haqqinki,Wannan Cin zarafin yayi yawa,da ba don Allah ya tsare ba Ai da ya Lalata Miki Rayuwa, yanzu Shekarunki nawa ne?""Seventeen" na bashi Amsa a taqaice
"OMG,This is child molestation, he molest a child kuma yana neman Yi mata barazana Ga karatun ta!, wannan wani irin Rashin imani ne?, Don't worry Dear Inshallahu zan kai maganar sama Dan wannan case din ba qarama bane,Sai an bi miki hakkinki,Take care of Ur self"
Dadi ya lullu6e ni,Ban iya cewa komai ba,Sai jaanaan da Taketa yi masa godiya,
Zamu tafi najiyo muryanshi yana tambayana "Munayferh Har Yanzu Dad dinku Shuru?, ko kunsami wane bayani dangane dasu ne?"Ban Amsa mishi ba Dan na tsani Ayi min maganan iyayena, ba Dan zai taimake ni ba da na yarfa mishi magana.
Ganin bazan bashi Amsa ba yasa ya shige office dinshi yana mana Allah kiyaye
Kallo na janaan tayi cikeda mamaki tace "Nayfee, wane lokaci KS ya kira ki office din sa ko dama jiya bayan mun Rabu kin Dawo School Dinnan ne, ?"
Ta fada lokacin da take tada motaNace "Aa,ko daya Sharri nayi masa "
"Raunukan Face dinki fa?,kuma kince ba accident kikayi ba"
Kawarda zancen nayi da cewa"Muje Office Din kS,"
Babu musu ta juya Akalan Motar Zuwa Science Complex inda Office din KS yake
Fitowa nayi daga mota daqyar ina Dingisawa na Shiga office din babu ko Sallama ,Ganinshi nayi da wata Student Suna Dan kus-kus🤤,
A Razane Duk Suka dawo hayyacinsu, Student din ta dau Jakarta da mayafin ta ta fice tana Sunkuyar dakai ,Sai da na Kare mata kallo kafin ta fice Dan inna ganta A hanya Gobe Zangane ta ...
Muryar KS naji cikin Hayagaga yana fadin"Ke wace irin mahaukaciya Ce,Ya Zaki shigo Mana babu Sallama ko..."Hannu na daga mishi"Hey man Kar kamin borin kunya anan, Ba wannan ya kawoni ba, Class list dinda kasa Aka cire Sunana ka tabbata yanda Ka cire Sunan nawa haka Za'a cire Sunanka A jerin ABUlecturers, na fada maka hakan ne Dan Tun wuri ka fara Neman Aikin yi ko dako ne Dan zaifi Rufa maka Asiri" Ban tsaya jin ta bakin sa ba na fice Nasan na Barshi da Takaici da Tunani kalakala......
Ina Fitowa na Sami Janaan Tana jirana a mota ta tambayeni "Me kika gaya masa?"
"I cant Talk anymore, Bakina na ciwo", na fada ina lumshe ido Daidai lokacin da Ya'ya'n cikina Suka Nemi Nasu haqqin.
YOU ARE READING
HAWAN JININA (Uwarmijina)
ActionLabarin Uwarmijin da ta Takura Wa surukarta, daga baya Ta hada danta Aure da Wata Yar Uwarshi saboda wata 6oyayyen kudurinta ,Amma me?, sai Yarinyar ta zamar mata Raina kama..........