Chapter 11

17 1 0
                                    

🌀🌀🌀🌀🌀🌀

     *HAWAN JININA*
     ~{UWAR MIJINA}~      

🌀🌀🌀🌀🌀🌀
                NA
   *🤍Fahnaan🤍*

_MARUBUCIYAR: MA'ESHERH(ANNOBA)_
       
©🎆
*AL'UMMA WRITER'S ASSO...* ✍🏻
  _A• W• A•_
_{Al'umma writers, Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane gsky al'umma sai dan Al'umma, Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}._
 
بسم الله الرحمن الرحيم...

    *_Chapter 11 _*

"Nice Nan na"
Daga Ramlah har Aaryaan din Dagowa Sukayi suna Kallona, cikin tsananin mamaki Ramlah tace
"Kece kikayi me?,Me kika yi masa?"

  "Juye OrangeJuice nayi na musanya da Jajjagen Attarugu" na fada ina Nuna mata Bottle din juice din ina dariyan Mugunta.
  "Yaa Akwai Yaji kor, ko Zaka qara ne?" Na fada ina kara Tsuntsurewa da dariya

     Cikin tashin hankali Ya bude baki zai yi magana MaqogoronShi ta Amsa😄,Da Gudu Ramla ta Tashi ta Dauko Ruwan Sanyi A freezer, Ta Kara mai abaki, nan fa ya shiga Antayawa cikinsa, Saida ta tabbata ya shanye Ruwan tas babu Saura, Sannan ta Cire BakinGorar daga Bakinshi

   Ina Tsaye bakin kofa Duk Abinda Sukeyi, kar nake kallon Su, Sai faman Darawa nakeyi kaman mahaukaciya Sabon Kamu.

   Muryan Yaa Aary naji In his Cool voice yana cewa"Tunda kin Gama Abinda Zakiyi Ki Fitar mana a daki pleasee"

" Ban Gama bah, kasan Dalilin Daya sa na maka hakan?" Bai Amsa ni ba ni kuma oho ban damu ba, na cigaba da cewa.

    "Shinkafar da ka dura min A Asibiti, mai yaji, Shine nima na Rama na dura maka Pepper Juice, Naso Ace dukka ka kwankwada Yanda ka Sani Hadiye shinkafar da ban tauna ba, Mugu kawai😒, ke kuma Aunty Ramlah ki fara shirin Shiga Layin zaurawa, Dan in na Fara Rama dukan da yayi min, kashe shine kawai bazanyi ba babu mai Rabani dashi SAi Allah” Ina Dasa aya na juya Har zan Fita Sai na kuma dawowa Naga yanda Idanunshi Sukayi jaa, da Ace ina kusa dashi na tabbata yau Sai dai wata bani ba.
" Yaa Aary look"
Dagowa yayi yana Kallona,na Sa Yar karamar yatsa na A gefen bakina Tareda kanne masa ido daya "Get Ready for my next Target" Na shiga Tari ina bubbuga kirjina kaman yanda yayi Lokacin da yasha Abin, Sannan na juya na Girgiza Masu Hips dina na fice ina dariya.

    Ina Fita Ramlah ta matso kusa dashi ta Riqo hannayen shi Cikin damuwa tace"honey,Please ko me Yarinyar nan Tayi maka ka Rinqa danne zuciyar ka,Na lura Yarinyar nan tanada Hadari Sosai, Duk yanda Akayi yarinyar nan Aljana ce, in ba hakaba kome akayi mata Sai ta rama?,ni Tsoron ta ma nike,kar wataran Tsautsayi Ya Afkamin na ta6o ta Nima naji A jiki na"

Aaryaan ya Dan Harareta "Matsoraciya, Shekara nawa kika bata?, you're 24 while She's 17, ba Aljana bace tashen balaga ke dawainiya da ita, zanyi maganinta Ai...."

   "Good morning uncle And Aunty" Abdool ya gaidasu yana Jan Chair, Suka Amsa mishi cikin Sakin Fuska

"Uncle, wannene Abinci na a ciki?"
"Duk Wanda ka za6a" inji Aaryaan

Aikam Kwadayi irin na Abdool baikai hannu ko ina ba sai kan Pepper Juice😆

__BooM_

~INTERMISSION~

Yau Friday Yau su Abbie zasu dawo so yau Zamu koma Kaduna dan tarbar baqi, Hakazalika yau zan bude su Suwaiba

    Tafe Muke a Mota Sai faman Surutu mukeyi, Janaan ke Driving Hafsah na kusa da ita ni kuma ina Sit din baya.
  Janaan tace "Aff Babe, kinga na manta nayi Miki ya jiki?, koda yike kinji Sauqi" Duk muka bita da kallon Rashin fahimta.

HAWAN JININA (Uwarmijina)Where stories live. Discover now