Chapter 23

15 1 0
                                    

🌀🌀🌀🌀🌀🌀
     *HAWAN JININA*
     ~{UWAR MIJINA}~      
🌀🌀🌀🌀🌀🌀
                NA
   *🤍Fahnaan🤍*

_MARUBUCIYAR: MA'ESHERH(ANNOBA)_
       
©🎆
*AL'UMMA WRITER'S ASSO...* ✍🏻
  _A• W• A•_
_{Al'umma writers, Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane gsky al'umma sai dan Al'umma, Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}._
 
بسم الله الرحمن الرحيم...

    *_Chapter 23_*

"Wash Cikina"

Na fada hawaye bisa kunci na

Ko Kallona baiyi ba Ya ta6e baki tareda daukar wayanshi Yace "In kin Gama kukan ki biyoni" ya dau kudadenshi ya maida Cikin Aljihu yayi hanyar fita,Na biyo bayanshi Ina Tafe kaman wacce Kwai ya fashe ma a ciki!,Ya sallemesu muka bar hotel dn

A mota kuwa Jingina nayi da seat din Motar ina kuka mai ban tausayi, Sai yanzu Memoryn kaina Ya fara Tariyo mn Abinda ya faru Tun bayan Fara shan Icecream dinda nayi,Harda wayan da Sukayi da Hilaal,Kuma na tabbata yaAary bazai ta6a mn karya akan Hakan ba.

Shikenan Tawa ta Qare na zama Matar yaaAary a dalilin Icecream na Rasa daraja ta😭😭,Na shiga uku Rayuwa ta tazo Qarshe Innalillahi wainna ilayhirrajiun Kuka nakeyi da iya karfina har ina shidewa, Amma ko sau daya bai juyo ya kalleni ba Bare nasamu Darajar Rarrashi.

Muna isa PZ ya yada zango a chicken Republic yy mn ordern Abinci,Muna hanyar GRA Hafsah ta kirashi Saida ya Sace kallona kafin ya daga yana murmushi.

Yace "Ya akayi Auta?"

Hafsah tacd"Yaa ka ganta ne?"

Yace"Yanzu haka ma muna tare"

Hafsah Ta sauke Numfashi sannan ta ce"Alhamdulillah To ka Ce ta karaso School Saura 15mins Mu shiga Ajin CHE122 kuma ance Yau Test Zaiyi"

Yace"Tho Gatanan Zuwa"

Tace"To ka hadani da ita mana"

Yace"Call her  line" sannan ya katse wayan.

Kaitsaye ya Juya Akalar motar Zuwa ABU Zaria a Chemistry Department ya Farka mota Harna yunkura zan bude kofar motar,Sai najishi a Garqame na juyo na kalleshi ba tareda nace komai ba

yace"Wipe Ur Tears"

Babu musu na Goge hawayena Amma kaman ina Bude kafar Fitar hawayen ne Suka Dingi fita kaman An bude famfo.

Ya maida Kansa ya jingina da seat yana kallon sama ya dau 2mins kafin ya ce"Idan Kin Tsayar DA Hawayen Sai ki fada mn,A Lokacin Zaki Fita"

Chak Hawayen Fuskata Suka tsaya Dan Zaman da Nayi a motar ji nake kamar a Kurkuku nake

Ya dan lumshe idanu kafin Yace "Dauko hijab ki saka" ,Da sauri na Janyo jakata na dau hijab na saka.

Ya bude min Kofar har zan Fita naji yace"aaie yahaan"(Zonan)

Na dawo na zauna Idanuna Fal da Hawaye yace""Mai wada karta hu chupa ke rekhunga" (Ki mn Alqawari wannan zai zama Sirri a tsakanin mu )

Na kalleshi a hankali cikin in'ina nace"Gum....su..da?"(Sirri kuma)

Yace"Eh aurennan ya zama Sirri! A tsakani na dake karki bari ko su Hafsah su sani"

Na maida kaina kasa ina wasa da yatsun hannuna nace"Mai wada karta hu"(Nayi Alqawari),Na fada Hawaye na Kara zubowa Saman Fuskata.

Ya furzar da wata iska mai zafi ,Sannan in his cool voice yace "Rona band kro"(Stop Crying).

Jiki a sanyaye nasa Gefen hijabina na Goge kwallar da suka zubo mn.

HAWAN JININA (Uwarmijina)Where stories live. Discover now