Chapter 16

10 2 0
                                    

🌀🌀🌀🌀🌀🌀
     *HAWAN JININA*
     ~{UWAR MIJINA}~      
🌀🌀🌀🌀🌀🌀
                NA
   *🤍Fahnaan🤍*

_MARUBUCIYAR: MA'ESHERH(ANNOBA)_
       
©🎆
*AL'UMMA WRITER'S ASSO...* ✍🏻
  _A• W• A•_
_{Al'umma writers, Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane gsky al'umma sai dan Al'umma, Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}._
 
بسم الله الرحمن الرحيم...

    *_Chapter 16 _*

Na wurga Saitin inna Rabi wacce take Aikin kama kunne ba,

Dama chan Allah yayini da iya saiti Saiga shi a Gefen Fuskarta, Sakin kunnenta tayi ta dafa nan tana ihu,

Zaro mata ido nayi na aza Hannu Saman lips dina Alamar tayi mn shuru Saigata Ta kama baki ta Riqe tana makyarkyata, Harga Allah Hakan da tayi ba karamin dariya ta bani ba,Saboda haka na Tuntsure da Dariya ina Riqe kai Saboda Sarawan da yake min.

Na tako har inda InnaRabi ke Tsugunne dafe da kunci, nace "ke Yar tsohuwa, kar kiga mun kyaleki ki dauka Mun yafe miki ne!,A yau dai zakici Albarkacin mijin da kike Aure yana qaunar Gudiyarmu Amma zamuyi maki kashedi Na Qalshe ,Koda Harara ko kallon kurillah kuka Sakeyi Wa Qaninmu Sai mun maida Ku Makafi,Zamu kakule idanunku muba 'ya'yan Sarkin Ruwan ido su Shanye Ruwan idon naku,Kin Gane?"

Ta Girgiza min Kai Alamar Eh

Na gyada kai tare da nufan inda Su yaa Umar suke yashe na lalubeshi na Ciro key na bude kofa na fita.Na fito Riqe da Hannun Abdool,Saida na bar part din InnaRabi Na shigo Tsakar Gida ,jiri ya kwashe ni na fadi Saboda ba karamin Bugu nasha ba Ga Ruwan da nasha da safe har yanzu ban koma normal ba Gaba daya  jikina ya Amsa Dukan yaa Umar,

KumaDuk Abinda Aikata Musu Cikin Dauriya nakeyi,Cus banaso Suga Gazawata Ahakan hakan

Abdool ya hau Girgizani yana kiran Suna na, cikin Karfin Hali,cus Shima ya jihata kuma har yanzu jini bai daina Zuba Daga Goshin Sa ba.Inajishi Amma ko Dan yatsana na kasa dagawa sai wani duhu² nake Gani, Ana Haka Saiga Aaryaan da Junayd sun dawo daga masallaci.

Zasu wuce parts dinsu Suka Ga'Alamar mutane yashe a kasa ,har Rige² suke Wurin Ganin ko su waye ,

  Suna Ganin mu duk suka Waro idanu Cikin Mamakin Abinda ya Same mu

   Junayd Yayo kaina yana jijjigani Yana kiran Sunana, Aaryaan kam kama hannun Abdool yayi Yana kallon yanda Goshinshi ya fashe, ba tare da Ya ce komai ba, Sannan ya juya Idonshi akan mu

Gani yayi Junayd ya daukeni Chak ya Sa6a ni a kafada, Ba karamin 6ata Ran Aaryaan yayi ba,kuma Ya rasa dalilin 6acin Ran nasa

Saida ya bari Junayd ya fara tafiya Sannan yasa kafa ya Shureshi ya Fadi ta baya ,  yasa kafa ya hankade shi Gefe , sannan ya 6anbareni daga Jikin Junayd yana Hararar sa,

Tashi junayd yayi yana kakka6e jikinshi Baisan Dalilin Hankadeshin da Aaryaan yayi ba,yaja Hannun Abdool da yake kallonsu baki Sake,Suka bi bayan Aaryaan.

A General falo ya Shimfidani a kan Three Seater Sannan ya tashi ya Dauko Ruwan Sanyi a fridge ya yayyafa mn jin Digar Ruwan Sanyin da naji a Fuskata yasa nadan Bude idanu a hankali na waresu Akansa , Gaba daya jikina ya mn nauyi ko hannu bana iya dagawa ,Sai a yanzu Nakejin Zafin Dukan da Yaa Umar ya mn

Dishi ² nake Ganin mutum Shiyasa na
Kara Rumtse idanu  Na ware su Akansa ,Yana zaune kusa dani ya wani kura mn ido kaman Yau ya fara Gani na , Duk da bana jin dadin jiki na Saida na harareshi na sannan Turo baki

   Hannunshi aza kan lips dna yana yawo dashi , na Gane Abinda Yake nufi Shiyasa, Na yunkura zan tashi a tsorace Amma sai naji bazan iya ba,

bazan iya Daga koda hannuna ne duk ilahirin Jikina Ciwo yake mn Zumburo baki nayi Hawaye suka zuba saman kunci na.

Tsaki yaja tareda kauda kai gefe "Ke nifa kar ki mn kukan Munafurci anan dan Saida akace ki bari Amaki Allura Dazun kikaqi, yo Gashi ae kin qara karo makanki wata Alluran , Allah kadai yasan Uban wa kika tsokano yayi miki wannan Ubn dukar, ga Shatin Hannu Kwance Rudu rudu a Fuskar ki, to yanzu Kukan me kikeyi?...." Tsagaitawa yayi DA fadar da yake mn jin Junayd na Tambayan Abdool Meyasamemu.

Abdool ya Kwashe komai ya fada Masu, Junayd ya karasa Daura mishi Bandage a kansa yana Murmushi Ai Nasan Daughter bazata bari A daketa a banza ba Duk giman mutum Sai ta Rama

Aaryaan ya nade hannunshi a baya yana kaiwa da komowa Ranshi a Jagule

ya jaa Tsaki dai-dai lokacin da Umma ta fito daga Kitchen Riqeda Coolern Awara ,Wanda nace ta mn Dazu.

    Ganin Aaryaan yana kai komo Ga Junayd Yana yiwa Abdool Dressing yasa ta fasa hayewa saman ta tako  har inda  muke Tana Tambayan lafiya? Junayd ya bude baki zai bata Amsa Aaryaan ya harareshi yace"Basu da lafiya ne"

Umma ta Riqe ha6a "yo Basuda lafiya, Ta Shafe Ku ne?, KUN WANI tasa su a gaba Sai kace Wasu likitoci, Ku ko zuciya Baku dashi, Yarinya duk Rabi ta Raina Ku harta ni uwarku bata Bari ba Sannan, wani Abu ya samesu Ku kinkimo kayan Aiki kuna Basu kulawa,Yarinyar da Ko yanzu ta tashi bataqi Tazage....."

Hannunda Aaryaan ya daga mata shi ya sa ta dakata da maganar da takeyi Ta kafeshi da idanu tana jiran taji  ta bakinsa,

Saida ya kawarda kai Gefe ya Furzar da iska daga bakinshi ya ce"Haba mum, ya kamata Ace koma me Yarinyar nan tayi miki ki Tausaya mata mana, She need our help Right now, kinsan Yarinta ke damunta Bata Gama mallakar Hankalinta ba shiyasa take Irin wannan Abun , ya kamata ki mata Uzuri Akan hakan mana!" Ya karashe magana yana Kallon inda nake kwance.

Umma ta hasala iya Hasala, Dukawa tayi ta Ajiye Coolern dake Riqe a hannunta,Sannan ta tako har inda yake tsaye ta Tsaya Saitinshi Suka fuskanci juna ta fara magana cikin Kakkausar lafazi "Aryaan ni kake Fadawa magana Akan Yar Yarinyar nan?, Wacce ta maida maka uwa kamar baiwa?,Har kana Gaya min Ai Yarinya ce?, Aikam Yarinya ce fa Tunda Yau Aka haifeta ai, to ka Bude kunnuwan ka kajini dakyau, Idan kasake daga hannu Ka A kan Yarinyar nan Da Sunan zaka taimaka mata  Allah ya isa Tsakani na dakai Ban yafe ba , kuma Sai na tsine maka Kabi duniya", sannan ta juya Ga Junayd dake Gyarawa Abdool daurin Bandage a Goshi. " kaikuma banason na bude Na bude idanu na sake Ganinka anan duk ka fice min Anan,Kai kuma Aaryan ka dauki Coolern nan ka kai mn daki, ta kwana gidan sauqi Dama Inada baquwan da zanyi Anjima"

Ko kallonta Aaryaan baiyi ba ya Ra6a ta Gefen ta ya wuce,

Ramlah dake Sama tana kallon su ,taja Gauron Numfashi tana  mamakin Hali Irin naUmma Ita babu Wanda ta bari, Hatta y'a 'Yan Dan uwan mijinta!

Dakin Kakus ta shiga ta sanar mata Ga Munayferh nan an kawo ta Rai a hannun Allah.

   Fitowa kakus tayi tana  Ambaton Sunan Allah
Hafsah jin sallallamin da Kakus take kwadawa yasa ta fito da Sauri Dan tana Tambayan me ya faru , Ganin Kakus Rungume da Munayferh tana Kuka yasa Ta karasa jiki A sanyaye ,kakus na Ganinta ta Share Guntun Kwallan ta tace" Yawwa hafsah DanAllah ki kira mana Dr ,Yi sauri Dan Allah kar ta mutuuu" ta karashe magana tana Rushewa da Kuka

  Koda Dr yazo Allura uku yayi mata na pain Relieve da alluran bacci Sannan na Sauke zazza6i, Dan Hafsah ta sanar dashi Yanayin Jikin nata a lokacin da ta kirashi

   Sai bayan Esha'i na Farka A lokacin Har an kaini daki na Kakus da Ramlah ne kawai a dakin,

Ina bude ido Suka hau min Sannu ya jiki?,Ina ke miki ciwo.........






Allah Sarki Munayferh Har kin ban Tausayi😂


Manage Please🤧





Jum@ mubarak❤️❤️

Wattpad @fahnaan

28th August

HAWAN JININA (Uwarmijina)Where stories live. Discover now