chapter 24

13 1 0
                                    

🌀🌀🌀🌀🌀🌀
     *HAWAN JININA*
     ~{UWAR MIJINA}~      
🌀🌀🌀🌀🌀🌀
                NA
   *🤍Fahnaan🤍*

_MARUBUCIYAR: MA'ESHERH(ANNOBA)_
       
©🎆
*AL'UMMA WRITER'S ASSO...* ✍🏻
  _A• W• A•_
_{Al'umma writers, Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane gsky al'umma sai dan Al'umma, Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}._
 
بسم الله الرحمن الرحيم...

    *_Chapter 24_*

Lokacin da Umma ta isa Gidan Aaryaan babu kowa a Gidan Sai Ramlah itama tana kitchen tana Girka Wa OGA AARYAAN Abincin dare.

Umma Tun A falo take kwala kira "Aaryaan! Aaryaan!!, Wai ina Ka Shiga ne?, Bakaji nane?,Eh? Kafito, Tunda ka Guji uwarka Gani nazo ,Kar ma ka fito Gidanka ne kuma na zo ,Bani komawa Ko ina Sai Alhaji ya dawo tunda Abin ya kaiga haka har Da zai Guji Uwarsa oh ni Sa'adiyyah banyi sa'ar Haihuwa ba wlh"

Ramlah dake kitchen taji hayaniyan Umma Gabanta ya yanke ya fadi Shikenan Qarshen Farin-Cikinta yazo,Jiki asanyaye ta fito Falo inda takejin Surutan Umma.

Ta fadada Fuskarta da Murmushi Tanacewa "Sannu da zuwa Umma ya hanya?, Ai Aaryaan din ya Fita Tun DA safe bai Riga ya dawo ba"

Umma ta katse ta"Na tambayeki ne?, iyeh!, Watoh duniya ta miki dadi Har wani Fresh kikayi Ga wani Kiba da kika karayi, lallai an Sami hutun Sati Biyu an murmure An barni sai Qashin wuya da Tayani muni nake Tarawa, to na dawo nima Kibar nakeso nayi Na murmure na more dana Ehe!,..... Ji yanda Fatarki ta Sauya kala ta koma Jaazir kaman Baturiya, ke anya ba Ciki Gareki ba kuwa"

Ramlah ta sunkuyar dakai Cikin Jin nauyin tambayan umman tace"Ni!, Nida Wanda Nike Aure ke dauke da Blood cancer ai babuni Babu Haihuwa har abada Sai  in ta Allah ta kasance na Auri wani, ko kin manta ne Umma?"

Harga Allah Ramlah bata fadi maganar nan da wata manufa ba Magana tayi tsakanin ta da Allah Amma da yike Umman  Al-Masifatu ce Sai ta hayayyakota "Munahika Dama Burinki bai wuce ki ga bayan dana ba kin daura mai Cutar Blood cancer bai isheki ba har Fata kike ya mutu ki Auri wani Ki barni da Asara kenan koh,To ahirr dinki Wallahi sai dukka Ahalin Ku sun mutu kafin dana ya mutu, Munafikan Allah, ni in banda kaddara inani ina hada Dangi da marasa Asali, Wa'enda aba'a San daga wace duniyar Suka zo ba?!, Mugaye dangin mayuh?"

Ramlah Ta danne 6acin Ranta Ta duqa zata dau mata jakarta ta dakatar da ita Tace" Dakata dakata dakata, karki kuskura ki Ta6a min jaka,Me kika Ajiye jikin Jakar?,ko na saki ne?"Umma Tadan tsagaita Tana bubbude kofofin Hanci kaman maishaqar wani Abu kafin daga bisa ni tace "Wai warin me nakeji kaman Abu na Konewa?"

Sai a Yanzu Ramlah ta tunada ta aza Sanwa kan wuta, da Gudu ta koma kitchen din, Umma ta biyo bayanta dan Ganin Kokof😂 ,

Gaba daya Abinda ta Daura ya kone kurmus Sai Kauri ke tashi, Umma ta Riqe baki tace "Me zan Gani ?,Abincin ne ya qone haka?, Lallai Yarinya Kin Samu Sake dayawa ,toh wlh Sai kin Biya Abincin da kika Qona ,ko kuma ki kwashe ki Adana Shi Zaki ci har na tsawan kwanaki Uku, yo ai Wannan ko ni zai mn Kwana Biyar In Gaya miki, Gara Aaryaan din ya dawo Muyi sabon zama Dan Aradu bazata Sa6u ba!" Yanda take zuba kekia ce itace mai nemowa..

Ramlah tace"Haba Umma akan 'Dan Abincin nan kike daga Murya haka?, Ai idan wani ya jiki zaiyi zaton ya wuce haka ne,Alhalin Abincin daga nawane Sai nashi dana Hafsah "

Umma tace "Wai da Aka auro ki Garan me aka kawo Gidan nan?,Inace Cewa akayi a barshi, daganan ya isa ace kin Gane Ba Matsiyaci kika aura ba munada Zuciyar nema kuma Bazamu bari wata bare tazo ta wulaqanta mana Dukiya bah,Duk wannan Uban Abincin da kika dafa kice naku uku ne...Toh Abun yazo qalshe,Daga yau idan ina Gidan nan ni zan dinga Auna Iya Abincin da Zaki Dafa Dan naga Albazarancin ki yayi yawa kinji ni kor"

Ramlah ta Gyada Kai Alamar Gamsuwa Umma ta juya ta fice tana Sababi

Daga Zuwan Umma har ta Fara Shimfida tabarmar Tsiya.😆




Aaryaan kuwa yana barin Gidan ya dau waya dan ya duba TYm Yaga miss calls Daga Asibiti ya tabbata ana nemabshi ne Shiyasa ya Garzaya Shika direct, Dama akwai Aikin da ya baro a chan.

Sai 6:30pm kafin ya  Samu kansa, A lokacin Hafsah ta kirashi tace Jaanaan ta kirata tace a Gidanta Munayferh zata kwana..

Baice komai ba Amma yana mamakin Hali irin na Munayferh wato idan An kwa6o ta tanan zata koma tachan🤧🤧

______________

Abinda yasa na Za6i kwana Gidan jaanaan Saboda nasanta,Bata damu da Sanin damuwan mutum ba idan ba Mutum yayi niyyar fada mata da kanta\ kanshi ba!, bakamar Hafsah ba Da idan tagan ni Cikin damuwa sai Tabi diddigi tasan Dalilin damuwan In ba haka ba itama ta Shiga damuwan kenan Shiyasa na fi Son kwana Gidan jaanaan idan ina cikin Damuwa, Cus ni mutun ce mai zurfin Ciki ba kowa ke sanin Ciki na ba duk yanda muke tareda Kai kuwa, Sai in nayi niyyar Gaya kawai.


Cikin Damuwa janaan tace"Nayfee please Stand up mana!"

Cikin Qufula Nace'' Dan Allah ki qyaleni Wai dole ne?"

Tace"For the last time, idan baki tashi ba Saina kira YaaAary na gaya mishi ya aiko a zo dauke Ki kawai,"

Ban tanka ta ba , kawai saiji nayi tana waya da mutum🥺,  ai ban San lokacin da na doro kan Gadon ba na zuba mata ido ina jiran jin ta bakinta, banji me ya gaya mata ba.
Na daiji tace"Bataci komai ba Amma kaman zazza6i ke Shirin kwantarda ita,Tunda kana kusa kawai  ka taho mata da magani" sannan ta datse wayan.

Na bita da Harara ta ta6e baki sannan ta miqe ta yi Alwala ta Gabatar da sallahn isha'i.

Ina zaune Har ta idar da sallan.a lokacin wayanta ya hau ruri tasa hannu ta dauka banji me ya gaya mata ba ta dai miqa mn wayan, hannu na rawa  na Kar6a Na kara a kunne...

Muryan shi naji Cikin Yar dariya yace"ina jiranki  ki fito ko na shigo in dauko ki da kaina"

Babu Shiri na cire wayan A kunne na ina Zare ido.

Jaanaan dake kallona ta danne dariyanta Tace".....Gara ma ki tashi Dan bazan Bari ya shigo mn cikin Gida ba"

Na harareta ina turo baki kaman zanyi kuka na dau wayata Sannan hijab na fito 

na iskeshi jingine da mota Yana waya Saida ya gama wayan kafin ya Kalleni yace na Shiga mota, Bai kaiga bashi amsa ba wayan dake hannuna ta dau ruri Jeeboi ne .

Da sauri da dauka ina murmushi Mai Kara qawata Fuskata,Sannan nasaka Wayan a handsFree, Shi dai ido ya zuba mn Ganin Irin murmushin da nayi kafin na daga waya.

Daga chan 6angaren Jeeboi yace"Haba Babe, me ya kawo gaba babu fada?, Tun dazu nake ta faman kiranki Amma Bakiyi picking ba Why naa"

Nayi Dan murmushi Nace"Sorry Sweat Heart bana kusa ne"

Yace"Okay Dama Tun dazun da na mutumin nan ya ritsa mu hankali na ya kasa kwanciya, please me ke tsakanin Ku dashi?, naga Akwai sanayya A tsakanin Ku ne"

Nace" laah babu wata sanayya A tsakanin mu fa, Yayan wata Qawata ne Yanada mental Disorder shiyasa Yayi maka haka dazun ,but Am sorry on his behalf "

Jeeboi yace"Babe mutumin fa baiyi kamada Mahaukatan nan ba, Naga kaman Shima sonki yakeyi kuma Kishinki yasa shi yin hakan ko dai Kuna soyayya ne ban Sani ba!,Tell me pls, you know..."

Na katseshi da cewa"Haba Swthrt Am not cheating on you,even if I were to cheat it can be with yaaAary that mad mad With mental disord......."

Ban Karasa ba naji saukan mari saman Fuskata Wanda yayi sanadiyyan daukewan ganina na Wasu Yan seconds.











*Hakika babu babban jin Dadi sama da Allah ya hadaka da masoya,inama ace wannan soyayyar da kuke nunamin ta kasance har Abada ina kaunarku masoya na danaWannan  littafin Allah ya bar Qaunar nan har Abada*

wattpad @Fahnaan

Nayi Gabas🚶🏻‍♀️

6th September

HAWAN JININA (Uwarmijina)Where stories live. Discover now