🌀🌀🌀🌀🌀🌀
*HAWAN JININA*
~{UWAR MIJINA}~
🌀🌀🌀🌀🌀🌀
NA
*🤍Fahnaan🤍*_MARUBUCIYAR: MA'ESHERH(ANNOBA)_
©🎆
*AL'UMMA WRITER'S ASSO...* ✍🏻
_A• W• A•_
_{Al'umma writers, Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane gsky al'umma sai dan Al'umma, Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}._
بسم الله الرحمن الرحيم...*Alhamdilillah ban san da bakin da zan godewa masoyana ba,hakika naga ainihin sahihiyar soyayya
zallar so fiye da yadda Munayferh ke son Rashin kunya, ina alfahari daku da godiya gareku tare da addu'ar Allah yabar kauna ya kara zumunci ya sa zumuncin da soyayyar su dore har abada ameen**Hawwa bala dake da Safina Ali wannan page din naku ne*
*_Chapter 18 _*
WasheGari 12:30Pm Nida Hafsah muka Shirya Zamu Gidan Su janaan, Muna zaune a parlour muna jiran Fitowar Abba idan Zai fita ya Rage mana hanya
Saiga Su Yaa Aary da Ramlah Riqe da Hannun Juna Sai faman Murmushi Sukeyi
Sai naga Ta min wani bala'in kyau, Sanye take cikin Supper Atamfah, Blue and Milk dinkin Riga da skirt ,Kuma dinkin yayi matuqar dacewa da ita tayi lullu6i da Milk Veil,Shi kuma yana Sanye Cikin Kananan kaya Riga Sky blue da Blue jeans, Kanshi daure yake cikin Blue band ,Wanda Aka Rubuta AA CUSTEN anan.
Kawar da kaina nayi ina ta6e baki ,Araina nace "Allah ya turo Umma Zakuyi bayani😂"
~Keko banda sa ido ina Ruwan ki dasu?~😂
Kai tsaye dakin Abba suka shiga Hafsah tace"Yau fa Su yaa Gidan su Aunty Ramlah Zasu"
Na ta6e baki" in banda iyayi na Yaa Aary, Ni ban ta6a ganin Mutum ya je Gidan Surukai da qananun kaya ba"
Na fada Daidai lokacin da Suke Fitowa daga dakin, ya wani kalleni yayi wani shu'umin murmushi Sannan ya rada Wa Ramlah wani Abu A kunne,Banji Su ba Amma naga tayi murmushi shikuma ya zaga dakin Su.
Mai kunnen zomo🐰 Ashe ya jini ne Shine ya tafi Dan Chanza kayan
Ramlah ta qaraso inda Muke zaune tana fadada murmushinta "Our Twins Sai ina haka?"
Hafsah tayi dariya tace "Weren't twins ,But Triplet"
Itama dariyan tayi tana waigewaige"yo ni ai Ku Biyu na Gani ina ta ukun?, " haka Suka cigaba da Surutu Cikin tsokana,
Nikuwa Tunda ta Zo na kalleta Sau daya ban Sake kallonta ba,Bare na tankawa hirar tasu ,itama bata damu ba dan A halin yanzu ta fara Fuskantar Halayyana kuma harga Allah tana Tsoron tanka min .
Har lokacin da Abba ya fito, Sai a lokacin Shima yaaArry ya fito cikin dakakkiyar shadda mai kyau mai tsada fara fes👌🏻 wanda ta amshi shi yyi kyau sosai, da key d'in mota a hannunshi.
Abba Ya kalleni yana Yar dariya "My Rigimatu, Kin Fasa Guduwa ne?" Ya fada cikin Sigar tsokana.
"Laah Abba dama ba mafarki nayi ba?,I thought i was dreaming fah, To ya na Ganni A daki na?,Nida nake Bakin Gate how comes" Na fada ina Yarfe hannu
Gabaki dayansu Dariya suka saki "Yananki ne ya dawo dake,Lokacin ma har kinyi barci,Kuma Ko Awarar da kikasa Haleema tayi mki baki ci ba kin wani wahalar min da mata" Abba ya fada yana Jan kumatu na
Nima dariyar na Saki na kawar DA zancen da Cewa "Abbie, Gidan su Janaan zamuje Nida Autar ka, zaka Rage mana hanya kor?"
Abba yace "meyasa zan Rage muku hanya?,Baku da mota ne?"
YOU ARE READING
HAWAN JININA (Uwarmijina)
ActionLabarin Uwarmijin da ta Takura Wa surukarta, daga baya Ta hada danta Aure da Wata Yar Uwarshi saboda wata 6oyayyen kudurinta ,Amma me?, sai Yarinyar ta zamar mata Raina kama..........