Chapter 7

14 1 0
                                    

🌀🌀🌀🌀🌀🌀
*UWAR MIJINAH*
~{Hawan jininah💔}~      
🌀🌀🌀🌀🌀🌀
                NA
   *🤍Fahnaan🤍*

_MARUBUCIYAR: MA'ESHERH(ANNOBA)_
       
©🎆
*AL'UMMA WRITER'S ASSO...* ✍🏻
  _A• W• A•_
_{Al'umma writers, Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane gsky al'umma sai dan Al'umma, Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}._

_
Aunty Hafsah A Garkuwa wannan page din naki ne_ ❤️❤️❤️
 
بسم الله الرحمن الرحيم...

  *_Chapter  7_*

Dan kwalin Jallabiyar dake kai na na cire nayi wurgi Dashi, Na Yi Kacha-kacha da Gashin kaina, nayi tsalle na dira a wuyan inna Rabi, Na kai mata wani wawan naushi a ciki (Irin na Yan wrestling), Ai ban bata daman ihu ko kuka ba Dan mugunta na Gwarata da bango tayi kasa ji kake TIMM....😆,Sai A lokacin ta Samu dabar ihu cikin muryar nan nata kaman An burga tsohon bajaj  "Wayyo ummaru , ka zo ka taimaka min xata kassara ni, Zainab ina kike,suwaiba kuna Ganinta zata kashe muku uwa Baku ce komai ba?'' Har ga Allah maganganunta Sun Sani dariya hakan yasa na shiga darawa kaman wata mahaukaciya,And still ina Mazgar ta, Saida na tabbata nayi mata Raunuka kuma tayi laushi sannan na barta najuya ga Zainab wacce take ta faman daga kafa Alama fitsari takeji kuma kiris take jira Ta Antayo ta....

Na Shiga darawa ina tafi kaman wata zararriya "Wato Ku Masu karfin hali Har kun isa Ku ta6a mana kani , har a gabanta zaku iya daga hannu Ku dakeshi, yanzu Akafara ,Yanzu na Gama da uwar Ku ,Saura ke....." Dakatawa nayi jin zuban wani Abu kaman ruwa,Zainab ce ta tsula fitarin da ya tarun mata a Mara Dan tsananin tashin hankali.

Abdool banda dariya babu Abinda yakeyi nima dariyar nakeyi na cigaba da cewa "mai girma Tunbul yace karku taba wanchan mai bargajajjen hancin," na Nuna Zainab da Dan yatsa

   Wani irin Ajiyan zuciya ta sauke har saida najiyo shi, Dariya na kara sheqewa dashi nace "An gama Ranka Shi Dade..., ke mai katon hanci Naki hukuncin ba na dukabane idan kinyi biyayya ba zamu taba lafiyar ki ba,  Dukawa zakiyi ki lashe Fitsarin nan Tass in ba haka ba Mazgar da uwarki tasha Somanta6i ne akan naki.."

  Ai ban gama Rufe baki ba ta duka ta fara Lashewa tana yatsine fuska Hawaye na tsiyaya daga idanun ta...

Na juya ga Zee da Umar Wanda Firr suke jira su zura a guje

Kwalbar champagne din da na gani saman Fridge dinsu na Raruma na Narka qasa, nace su taka kwalbar har sai kafarsu ya fashe, kuma banason ganin jini , idan ko naga jini, Lashewa zasuyi.....

Ina Gama fadar haka na nufi Hanyar toilet Dan na cire makullin dake nan ina dawo Wa na gansu jini na kwarara daga kafar Umar ita kuma zee hannu tasa tana tana Tare jinin Ga kuma suwaiba da ta gama lashe Fitsari innaa kar har tayi baccin wahala, tausayin su ya kamani na kalle Abdool da shima yayi tagumi ya koma kalar tausayi.
  Nan da nan na yakice tausayin su Wanda ke Neman dunkusar Dani Na shiga darawa kaman wata mahaukaciya Dariyar da nikeyi ne ya farkar da innaRabi ta tashi firgigit Tana ihu dakatar da nawa dariyar nayi na murde fuska kaman bani na gama Dariya yanzu ba?

Na fara magana cikin muryan mai kamada Wanda ba nawa ba(kai Hausa akwai wuya fa😩) ina Nuna Masu key
"Nasan da wannan kuka dogara,Toh kusha kurumin Ku dantsalle yarigada ya dakko mn, in mun fita sai nan da kwanaki uku zamu dawo!, Ku gode ma Allah akwai Fridge mai dauke da kayan marmari da talabijin mai dauke kewa" ina kaiwa nan na dara naja hannun Abdool mukayi waje, na kulle kofar da makulli ta baya. Muna fitowa naga Yan Aiki dan gulma harda mai-Gadi Sunyi cirko-cirko a bakin kofa Kowanne da son jin kwakkwafin sa...

    Tsawa na Daka Masu "kunzo kun manne jikin kofar mutane lafiya?,"

Simi-Simi suka juya zasu wuce nace "a cikin ku Duk Wanda ya bude kofar nan ko bana nan, Sai na yanka shi nabawa Su talbudulmusuyanu Sunyi layya da namanshi," suka Gara tsurewa hanjin cikinsu ya kada
   Direct part din Umma na nufa, Dakin da yake mallaki na na shiga na yi wanka na dauro Alwala na gabatar da Sallan la'asar , Shima Abdool sallar yayi bayan duk mun idar ya dubeni yace "Anty munayfa ce?"

Harga tambayar tasa ta ban dariya nayi murmushi"to da wacece"

Rungume ni yayi cikin farinciki"Wlh na dauka aljannun gaske gareki ne!,I love You So much Anty naaH"

"I love you too my stubborn Kani, yanzu dai jeka kwaso kayanka Yanzunnan mu wuce Zaria tare"

"I thought anan Zaki kwana?" Ya fada yana dubana

"No ina da wani deal da wani lecturer, kuma inada lecturn safe"

Tashi Abdool yayi ya hado kayansa muka bargidan, kaman yanda nazo 20 min motar ta kaini zaria

********

Tun bayan lokacin da na Warce Awaran Umma ta shiga tunanin kalamai na tana tufka da warwara daga karshe ta Sami bakin zaren, Daidai lokacin da yaa Aryaan ke sakkowa daga matakalar bene "Aaryan Wato Yarinyar nan zamanta a part dinnan bai kamata ba, kamata yayi a Gyara wanchan part din su koma itada Hafsah ko ya ka gani"

Aryyan ya Dan Sosa qeya aransa yana fadin _dama ke kika koma chan da nafi Sakewa da matata_ ,  A zahiri kam cewa yayi "Hakane Umma Amma harda ke Zaki koma ko?"

Baki ta riqe tana fadin "In koma ina, ai kasan ban iya nesa dakai ba,bazan iya barinka kai kadai da wata bare ba!,Ai bazai yiwu ba, yanzu dai kaje ka kira masu gyara su fara Aiki kafin Gobe su koma chan din"

"Umma Tun yanzu?"
"Eh ko bazaka bane" Dakinsa ya nufa, sai da yayi wanka ya sauya kaya sannan kai tsaye ya nufi inda yake parka motarsa yaga wayam, mamaki ya kama Sa yasan tunda Driver ya parka motar , Bai sake Aikan kowa ba Amma Dan ya kauda kokwanto ya kira Driver ya tambayeshi  ko ya sake fita da motar ne Amma cewa yayi har makullin motar ma duk ya bashi

Ya kuma tambayan Malam Ali mai Gadi shima cewa yayi babu Wanda ya fita da motar , Wurin Driver ya koma yace ya bashi makullin dayan Motar wacce take ta hafsah ce Sbd bata iya hawa ba yasa Aka jingineshi anan duk yayi kura ....
   Shi ya hau ya Shiga Gari yana Neman motar sa a cewan sa ko barayi ne suka  Shammace su suka Sace motar, har Mangariba bai ga mai kamar motar ba, hakan yasa ya Koma masallaci Dan Gabatar da sallah

  A lokacin da na isa Gida kuwa har A lokacin Hafsah bacci takeyi, Gidan Tsit kaman babu kowa Dakin Umma na shiga Dan Dauko Remote dinTVn Dakin mu da na manta anan jiya...

  Ga mamaki na sai ganinta nayi da wata bakuwa duk sun Saki baki Suna Bacci ga Robar Awara da doya a gaban Su nan na gane Ashe Sleeping pills Akasa cikin Awaran Allah ma yaso ni da ban ci ba da yau bazan Samu damar Garewa da Yan iskan mutanennan ba

   Na dau Remote nayi Waje ina cewa "Yau su yaa Aary zaa chaskale fa🤪"

Ina Shiga daki na tarda har Hafsah ta tashi Sai  faman surutu suke zubawa Nace "Kin tashi?"
Tace "Eh , Wa ya kawo Abdul-Rahman?"

Nace"Nice nan, kiyi sallah muje Dakin Aunty Ramla muyi hira Umma tayi barci"

Tana idar da sallah ta ja hannun Abdool mukayi Sashen Su Ramla, A kitchen muka tarar da ita , Abdool na ganinta ya ruga ya rungumeta yana fadin Matar Uncle dama Gidanku daya da Aunty Maesh?

Shafa kanshi tayi tace "Eh yarona waya kawo ka?"

Mamaki ya kamani Baki bude nake kallon su Dan a iya Sani na Abdool bai ta6a ganin Ramla ba, kasa haquri nayi nace "Aunty dama kinsanshi ne?"

Tace "Eh lokacin da nake NYSC dina school dinsu Aka tura ni, kuma koda dad dina ya hadani da yayanki Sun ta6a zuwa tadi Gurina tare "

Na rufe baki cikin dariya nace
"Kai aunty wai tadi ko kunya?




















TOHFAH

WAI CIKIN INNA RABI, SUWAIBA ZAINAB DA UMAR WA YAFI JINJIKI NE?

INA JIRAN RAAYOYINKU AKAN WANNAN CHAPTERN....

DON'T FORGET TO
VOTE
SHARE
AND
COMMENT❤

Wattpad @Fahnaan🖋️




Thanks for Reading

See you tomorrow💃
Nayi gabas🚶🏻‍♀️🚶🏻‍♀️

19th August

HAWAN JININA (Uwarmijina)Where stories live. Discover now