chapter 5

13 1 0
                                    

🌀🌀🌀🌀🌀🌀
*UWAR MIJINAH*
~{Hawan jininah💔}~      
🌀🌀🌀🌀🌀🌀
                NA
   *🤍Fahnaan🤍*

_MARUBUCIYAR: MA'ESHERH(ANNOBA)_
       
©🎆
*AL'UMMA WRITER'S ASSO...* ✍🏻
  _A• W• A•_
_{Al'umma writers, Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane gsky al'umma sai dan Al'umma, Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}._
 
بسم الله الرحمن الرحيم...

  
     *Chapter 5*

Hilal Ya kalle jaanaan dake Faman latse waya yace "Wannan fa?, kawar Ku ce?"
Nace "Jaanaan ce fah, baka Santa ba?"

"Eh ,daga yar inace??"
" itama yar kd ce Anguwan mu daya "

"OK, banta6a ganin taba, But she's so cute...,Pretty Damsel"

Nadan Sace kallon jaanaan wacce gabaki daya hankalin ta na kan waya bata ma San munayi ba na ta6e baki "Ba laifi, amma fa nafita kyau"

Ya bude baki zaiyi magana yaji Aryaan nacewa "in ka gama, you can meet me outside" Yana gama fadin haka yayi waje. Hilaal yayi min sallama yabi bayan sa.

     Muma muna gama siyayyar mu muka shiga mota na sauke Jaanaan a Off.K mu kuma muka taho gida.
    Muna isowa na danna horn har sau Uku Gate-man bai zo ya bude mn Gate ba haushi da takaici suka ishe ni, Na kashe mota na Dora kaina a kan stirring din motana, hafsah ta bude murfin mota ta fita Ta kwankwasa , Gate-Man da fitowarshi kenan daga toilet rike da buta, ya leqo Ta Mini-Space Yana ganin mu da gudu ya wurgar da butar ya wangale mana Gate, Hafsah ta shiga tana Gaida shi cikin Girmamawa.

    Nikam na cika nayi fam , kiris nake jira in fashe!, A fusace naja motar Na shiga dashi, Har zan parka a parking inda na saba parkawa, Sai naga Tent dinda Yaa Aary ke parking motarshi wayam, Sai na fasa parkawa na nufi inda yake parkawa na Parka
  Ina fitowa naga Gateman tsaye yana jiran fitowana(Allah sarki bawan Allah🤤)

  Ya durkusa gabana ya hada hannaye waje daya yana fadin "Am very sorry Madam Wlh nadan zaga ne, Ban gama tsarki ba naji hor......." Bai karasa ba Na Daure fuska tare mishi hannu"Enough man!,hang it, duk wannan matsalar kace,Na Riga nayi maka warning Ka jira Hukuncin ka,Tsohon banza kawae mtsw" na sa6a jakana a kafada  gaba abina . Direwa ya karayi a gabana Yana hada hannaye alaman roqo "Pls madan ki ban ko wane irin punishment na yarda zan iya jure Wa , Amma banda wanda kika za6a min, inada ulser bazan iya jure yunwa ba har na tsawan kwanaki Uku ,Please Madam ki sausauta min"
  Shuru nayi ina jinsa Saida ya dasa aya sannan na kalleshi nace "Ka gama?, Nace ka gama?, OK stand up"
  Kaman jira yake ya mike tsaye yana matsar hawaye.
    Kallon Agogon Hannu Na nayi 2:47pm. Takaici ya kara turmuke ni yasa na wuce time din cin lunch dina , bansan lokacin da Nasa kasa na shure shi ba nan da nan ya fadi Kansa ya bugu da karfen Tent , Nayi gaba abina. Bai dandara ba ya biyoni da gudu yasha gabana "Madam please help!"
     Cikin Zafin rai da kunar zuciya na  daga hannu zan wanke tsohon da mari ba tareda na duba girman dattakon sa ba idona ya rufe banaji bana gani,jinayi an Riqe hannu na ta baya, Kamshin turaren sa ne ya tabbatar min da ko waye, na zaro ido Zuciya ta na dukan Uku Uku, Na tattaro dukka karfina Na fincike hannu na nayi ciki a guje .
    
    Aryaan ya kalle  Gate-man Wanda gabaki daya ya fice hayyacin sai sharar kwalla yake yi yace " Malam Ali, me ya hada ka da wannan yarinyar"

   Malam Ali mai-Gadi yaja majina tare da share gumin Dake karyo masa ya kwashe mishi kaf Abinda ya faru ya kara da cewa "Tun ranar da Tazo nan gidan ta gaya min Dokokin ta na farko kar tayi Horn Sau Biyu ban bude mota ba, idan kuma na qi hukun cina shine bazan ci Abincin Gidannan ba har na tsawon kwanaki Biyu kuma ba fita bare na siyo a wani gun in kuma na fita korana zatayi.

Doka na Biyu kuma idan zatayi aike ni zata aika kuma zata bani Time in na ketare Hukunci na shine bazan Yi Amfani da ruwan Gidan nan ba har na tsawon sati daya inzanyi sallah kam saidai nayi tayammun, in na nema ko akayi ruwan sama na Tara to korana zatayi"

  Aryaan ya kwashe da dariya ,cikin dariya ya dafa kafadan Malam Ali maigadi yace "Great hustler VS yar barazana , I wanna ce the end of this play Faah😂"
   Gateman ya kasa kunne don jin Horn din DA ake Faman dannawa  , ai da gudu ya zura ya wangale gate Motar Aaryan ta danno kai driver yayi parking ya fito da ledoji guda Uku ya mika Wa Aryaan tareda makullin motan.

    Ina Shiga na Shige Toilet nayo wanka na sauka kayana zuwa wata baqar jallabiya mai adon Stones na dauro Alwqla na gabatar da sallan Azahar Sannan na fito falo Dan nabawa ciki na hakkinshi.
    
   A takiyar falo na tadda su, duk sun yi tsuru sun kurawa tsarabar da Yaa Aryaan ya shigo dashi ido, jiki na har kyarma yake naje kusa da Umma na zauna nima na kurawa ledojin ido.
     Zaro ido nayi Ganin an fiddo Wani katon ledan Vanilla cream Puff pastry , bansan lokacin da na hadiye wani yawu  ba(Kwadayi ya motsa😜)
   Ya kara fiddo da Awara da doya mai  kwai   daga dayan ledan ledar karshe kuma  beef shawarma duk suna cikin takeaway daban daban ne.

   Ya mika ma Umma takeaway mai kunshe da Awara da doya mai kwai, Umma ta amsa cikin fara'a tana sanya mishi albarka,sannan Ya bama Hafsah dayan take away din mai kunshe da beef Shawarma ta  amsa tana godiya Ragowar takeaway din mai kunshe da puff pastry kuma ya mika ma Ramlah cikin murmushi ta karma tana godia.
    Ganin Angama rabo babu nawa yasa na zaro ido A shagwa6e nace "Yaya Gani fah"
Yace "Uhm?,sai akayi ya?"

Muryan Umma yaji cikin hayaniya tana cewa " Aradun Allah bata sa6uwa bindiga a ruwa, Inye Aryaanu!, Har kayi girman da Zaki Siyo mq matarka Abincin Yan birni ka hada uwarka da Awara da doya?, Anya kasan darajar uwa kuwa? Kasan Allah?, wlh bazanci Awara ba ,ka kwashe tarkacenka kada mata ta cinye" ta fada tana ture Robar takeaway din.

    Aaryan ya rike kansa dake Sara mai cikin taikaici yace "Sorry mum, indai akan puff vanilla ne gashi amma Dan Allah ki fara cin awarar kinsan yana da matukar mahummanci a jikin danAdam ko?,

    Umma tayi murmushin jin dadi tace " Allah yayi maka Albarka Aaryaanu yanda kayi min biyayya ka fifita ni akan matarka Allah ya baka waenda zasuyi maka fiye da hakan ma"
  Charab na Amshe da cewa "Kema kinsan dai wagga Adduar Iyakarta fatar baki ne kawae ,inba munafurci ba , kin hanasu xrsryjiyeasjkknh😜 kinzo kina Adduar Allah ya bashi da?, wane Dan kenan? Shege ko Dan titi?"

Ina gama fadin haka na sunkuce Robar awarar dake Gabanta na  kwasa a guje  ,Shima biyo ni Yayi yana son kwace awarar Umma!, amma kash kafin ya iso har na shige na sa key, a fusace ya juya zai koma yayi kicibis da Hafsah yace ta kar6o masa awarar Umma karta bari ta dana ko guda a ciki. Ya koma parlour Inda ya tarar da Umma tayi jugum tana Tunanin Furuci na na dazun
   Ashe duk abinda takeyi ina sane da ita?, ita ta dauka ni konko ce babu abida na Sani, Lallai zatayi magani na.
   ***
Koda Hafsah ta kwankwasa kofar ban bude ba Saida na leqa ta Dan karamin Glass dindake tsakiyar kofar .
Ina budewa waya na dake kan dressing mirror ya hau ruri , da sauri na dauka jin Ringing tone dinda na sa ma Abba na ne na kara a kunne ina Dan turo baki cikin  Shagwa6a nace"Abiey na sai yau ka tuna dani ko?, Tom nayi fushi"




NO DOGON TURANCI

SEE YOU TOMORROW😉

SHARE
AND
COMMENT😒


COMMENTERS I LOVE YOU WUJIGA WUJIGA IRIN EHN😉

GROUPS DINDA SUKA GA NA DAINA MUSU POSTING TAM SUYI BLAMING KANSU...... RASHIN COMMENT NE YA JAWO HAKAN



A CIGABA DA WANKE HANNU😄😄

Hope kuna sa nose mask kuma kuna bada Social Distance tsakaninku da wayoyin Ku  kafin Ku karanta littafina ko?😌

Nayi gabas🚶🏻‍♀️



Fahnaan🖋️




Friday 14th August🤍

HAWAN JININA (Uwarmijina)Where stories live. Discover now