Chapter 14

11 2 0
                                    

🌀🌀🌀🌀🌀🌀
     *HAWAN JININA*
     ~{UWAR MIJINA}~      
🌀🌀🌀🌀🌀🌀
                NA
   *🤍Fahnaan🤍*

_MARUBUCIYAR: MA'ESHERH(ANNOBA)_
       
©🎆
*AL'UMMA WRITER'S ASSO...* ✍🏻
  _A• W• A•_
_{Al'umma writers, Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane gsky al'umma sai dan Al'umma, Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}._
 
بسم الله الرحمن الرحيم...

    *_chapter 14 _*

"Kamar dai yanda kuka Sani sunana Rahma Rihan, mu Asalin Yan Pakistan ne,a cikin Garin Sindhi, cikin Garin Karachi ,mahaifiyata Asalin Yar India ,Mahaifina Shine Sarkin Garin Sindhi,

Garin Sindhi Garin musulmai ne Amma yanda Aladar masarautar mu yake sai ki rantse ba musulmai bane, kwata kwata basu yarda da qaddara ba, Sunada wani murdadden Aqeedah Idan Sarki ya hau mulki to dole sai ya kasance Yanada Da Namiji, idan kuma bai haifi da Namiji ba Yanada 'ya mace, tohkoro Yana mutuwa Zaa kori Yar daga Garin kuma bazaa bata kosisi cikin Dukiyar da mahaifinta ya bari bah.

To nima na kasance cikin wannan chakwakiyar, ni kadai mahaifa na suka Haifa,Na taso ne cikin Gata da Sangarta Gabaki daya Garin Tsoron ta6a ni suke saboda Halina bana barin bashi duk Wanda ya mn Ramawa nake, Kuma Ga tsokana da Rashin tsoro, Infact fadin irin Halina 6ata bakine , Halayena Sak yake da irin halin ki Munayferh Amma banbancin Shine ni a lokacin inaji da sarautar mahaifina Kekuma da Sarautar kanki kike taqama " Munayferh tayi murmushi batare da tace komai ba Dan ta zaqu taji Karshen labarin

Kakus ta cigaba da cewa"Ina chan ina Tara Fitina a Gari iyayena na Neman yanda zasuyi su haifi da Namiji Dan karda Rayuwata ta tagayyara, Lokacin inada Shekaru 14 a duniya Allah yayi Wa mahaifiyata Rasuwa, Mutuwar nan ya gigitani matuqa, bayan komai ya kafa ne mahaifina ya kara Auran wata matar,Wacce ta Dora karar tsana ta Dora mn Ganin yanda mahaifina ke Ririta ni kaman kwai, A lokacin ko harara tamin,sai na hada ta fada da mahaifina, kunsan dai bana barin bashi .

Bayan Shekaru BiyudaRasuwan mahaifiyata, Na hadu da Wani Saurayi Dan Nigeria Mai suna Yazeed yace yana son Aure ni, Amma Halina ne bayaso ,A lokacin ina 16yrs ,Nima ina sonshi A lokacin Amma yanda ya Nuna baya son Halina Shiyasa nake Nuna nima bana yi dashi, Tun magana na Tsakanin nidashi harya kaiga An fada ma maimartaba.

Ranar kam nasha Nasiha,Daga karshe yace  in turoshi su Gana, kuma zaisa ayi bincike a kanshi,Dama Wai Abinda yake jira  kenan ya bada Amanata ga wani kafin ya mutu Yan Garin Su kore ni.

Duk iya binciken da sukayi Akansa basu Sami wani Aibu ba ,Daganan Akasa Ranar biki Akayi biki A lokacin ne mahaifina ya tattaro dukka kadarorinshi ya ba ma yazeed ya kara a Jari (dama dn kasuwa ne) dan kula dani,Zaman mu da yazeed abace Gwanin ban sha'awa Bayan Shekara daya na Haifi dana Namiji A lokacin kuma mahaifina ya Rasa Ransa, Wayyo Ranar nayi kuka na rasa Gata Babu mai Ririta ni kaman Mahaifina Ga mijin da na Aura mikili Mara son Dogon magana  bare ya Ririta ni illa kawai ya zuba min ido in-ina kuka Infact Halin su daya da Aaryaan " Munayferh ta jaa Dogon tsaki"Mtswwww,Na ma fasaji,Ki Riqe Abinki,Tunda Mai'Irin Halin yaa Aary kika Aura ,labarin bazaiyi Armashi ba"

Kakus tayi murmushi tace"Aikam Shine armashin labarin, Tunda mukayi Aure ya taka mn burki Baya bani damar tsokana balle in taro match, Kafin Shekara ta zagayo na zama mutumiyar kirki,A lokacin ne kuma na haifi dana Namiji,Ranar suna Yaro yaci Sunan Aabir ,A lokacin ne kuma Ya Soma Sauya halayensa ganin na fara nutsuwa,Zokiga gata da tarairaya, kai har ya so yafi Wanda  mahaifana suka Nuna min Ashe dama chan Miskilancin Akan Halaye na ne.

Aabaan yanada Shekaru uku na kara haifan namiji, ya ci Sunan Junayd , daga nan ban sake haihuwa ba a lokacin naso haihuwar mace Saboda in Sa Mata Sunan Mahaifiyata *Munayferh*  Amma allah baiyi ba

HAWAN JININA (Uwarmijina)Where stories live. Discover now