Chapter 10

15 1 0
                                    

🌀🌀🌀🌀🌀🌀
     *HAWAN JININA*
     ~{UWAR MIJINA}~      
🌀🌀🌀🌀🌀🌀
                NA
   *🤍Fahnaan🤍*

_MARUBUCIYAR: MA'ESHERH(ANNOBA)_
       
©🎆
*AL'UMMA WRITER'S ASSO...* ✍🏻
  _A• W• A•_
_{Al'umma writers, Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane gsky al'umma sai dan Al'umma, Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}._
 
بسم الله الرحمن الرحيم...

    *_Chapter  10_*

Doctor yace "Calm down Ai kinSami Sauqi,Tunda kina iya Tafiya, Saidai ayi Anyother treatment a Gida, Inshaallahu 1:00pm zamu Sallame ku".

Bance komai ba har ya Gama Bayaninsa ya Fita.

   Ganin Duk Sunyi Tsit babu mai magana (Ni kuma na tsani zama Wurinda ba'a magana), yasa na kalle hafsah nace " Ke yau bazaki school bane?"
"Eh, sai gobe"
"Ta6 Ai mu mun je School din Tunda Safe, Har munyi Settling matter da KS dawowan mu  kenan ma, ko janaan"Na fada ina kallon janaan

Umma ta sako baki "Qalya kiri-kiri a Filin Allah, ke da ko Takawa daqyar kikeyi ina kika Sami Qarfin Zuwa wani makaranta?"

Katseta nayi ta hanyar daga mata Hannu nace"Umma ni fa ki daina Sako min baki in ina magana Ehey....Wash". Na dafa kaina jin An rankwasheni ,Na dago Dan ganin wanda Ya rankwaahen, Yaa Aary na gani Tsaye yana Gyara Tie din wuyan Rigarsa (Ashe Kaya Nurse Dinnan ta bashi a Leda yaje chanzawa)

  Zaro ido nayi na kama baki na "Wlh bada ita nake ba!"
  Kwafa yayi ya juya Yana kallon Umma"Mum ya Zaki Ringa Ruba idanu Yarinyar nan tana cha6a miki maganganu San Ranta?, Haba mana, Ni in Shakkar Hukunta ta kike ki barni da ita Duk Randa Ta Miki Rashin Kunya na kamata Saina kusa kashe ta.

  Muryan Abdool Sukaji Cikin Dariya yace "ka kusa kasheta ita kuma ta kasheka gaba daya ba" Gaba daya Juyawa Sukayi Suna Kallonshi Ya wani waske fuskansa Na kan wayan da yake dannanwa kai ka ce bashi yayi magana yanzu ba!...

Shima Waskewa yayi Ya juya ga Nurse dinda ke Mopping yace " Nurse Find her Food"
Nurse ta Russuna"OK sir"
Har zata Fita nace"Hey nurse "
Juyowa tayi tana kallo na "Please Find me Green Tea,Fried egg and potatoes, Pls be fast"

  Nurse ta Amsa da OK ta fita.

  1:30pm Akayi Discharging Dinmu bayan mun dawo ne Umma ta kira Abba take fada mishi Rashin lafiyata,Wai zamowa nayi daga Saman Step stairs😏 (Idan baki San me ya faru ba ki tambaye ni zan fada miki yanda Akayi, bawai kizo kina Zubo mana ehyane ba)😁
      Abba yace"munyi waya dazun ta fada mn Zazza6i ne kawai,kuma ta ji sauqi Sosai.....Amma Halima mai yasa kike takurawa Yarannan ne?,Meyasa kika hana Yarinya Saqat a gidan mijinta ne?, Ke haka Akayi miki ne?..............Nan ya Rufe ta da fada ya kuma ce ta dawo Gida yau yau Dinnan Shima ya dawo yana Abuja Gobe zasu karaso in ba hakaba Ranta Sai yafi nashi 6ace.

    Bata katse Shi ba dan ta san halinshi in yana fada yafi so A saurare shi har sai ya dasa Aya .saida ya Gama Fadanshi ta bashi Haquri  kuma inshaallahu yau Dinnan zata dawo Gida daga nan Sukayi Sallama Ta katse wayan.

   Fitowa tayi ta nufi Part dinmu Wanda Tun jiya Aka Gyara mana Nida  muka koma NaN.

    Hafsah kadai ta gani A falo tana kallo tace"Auta, ina Yar banzan yarinyannan?"
"Ta fita" Hafsah ta bata Amsa a taqaice"
"Toh idan ta dawo ki fada mata ta Yi nasarar Raba tsakanin uwa da Da ta kuma yi nasarar hada Tsakanin Mata da mijiTana Gama fadin haka tayi waje tabar Hafsah da mamakin kalaman Umma (Kodai ta Sami ta6uwa ne?)

   Umma kuwa tana Fita dakin Ramlah tayi Ta kara jaa mata kunne akan kar ta ta6a ba ma Aaryan kanta in ba haka ba to zata rasa Mutuncin ta ne kawai a banza A hofi, ta tashi a tutar babu...

******
Nikam Fitan da nayi ,inda na bada Ajiyan motana nayi Na kar6o daganan na nufi Pz nasiyo Wasu Abubuwa Sannan na karaso Gida.
    Ina shiga na kwala Wa Hafsah kira ta fito daga bedroom da Alama bacci ya fara Daukan Tane  "Hafsah waishin Cikin Attarugu da tattasai wanne ne yafi yaji"
"Mtsww,Dama wannan banzar tambayan Zaki mn kike kwala min wannan Uban kiran?"

"Banzar tambaya ko?,Bakomai"

Ganin kaman raina ya fara baci yasa tace"Duk Sunada yaji Amma inaga kaman Attarugu yafi"

Kallonta nayi da murmushi nace"Thank you So much"

Karasowa tayi tana bude Ledar dake gabana "me kika Siyo mana ne?"

"Attarugu da Tattasai"

Kallona tayi "keko me zakiyi da Attarugu da tattasai?"

"Nothing Fah, Just Pepper juice nake son Hada ma wani  First of All ina Abinci na yunwa Nike ji,"

Tadan harare ni"Baki San Hanyan dinning bane?"

"Wlh na Gaji ne please Dauko min"

Mamaki ya kama ta jin yanda nayi magana in a cool voice, Abinda bata ta6aji ba, A ko da yaushe ina buqatar Abu bana Neman Alfarma, Command nake badawa.
   Gyada Kai tayi Sannan ta mike ta nufi Dinning ta Dauko Abincin ina ci muna hira.

*****

WasheGari Tunda Asuba na Niqa Tarugu da tattasai na, na tace Sannan na cika mishi Ruwa yayi Tsululu.

  Karfe 7:30 naFito cikin Sanda na nufi Part din Su yaa Aary Hannu na Riqe da Empty bottle daKuma Bottle mai kunshe da pepper juice🤪😜

A Dinning naja burki Ganin har An jera kayan kalaci Nadan waiga Ganin babu kowa yasa na bude Katon Jug mai kunshe Da Orange Juice(Wanda na Tabbata na yaa Aary ne,Sbb A kaidan sa kullum kafin ya karya Sai yasha shi sannan zai karya) , na juye A Empty bottle dinda na Riqo,Sannan na Musanyashi da pepper juice,
     Takun Kafa naji Abaya na Kaman Ana doso inda nake, Nayi Saurin Boyewa kasan table,

    Ramlah ce na hango Riqe da Tray din Jugs and cups An wani ci kwalliya !

  ~Samun Wuri~ na fada A raina, dai-dai lokacin da Ta Ajiye kan Table ta juya ta koma kitchen.

    Saida na tabbata ta shige kitchen din Sannan na fito na bude dayan Jug Din, Black Tea ne a ciki, Shima budewa nayi na zuba Pepper dina Amma kadan Nasa a ciki, Gudun kar ya chanza kala a gane,ina Gama Zubawa na tattara bottles dina nayi waje Raina Fess

8:00pm dot
Ya sauko Cikin Shirinshi na zuwa Office,Sanye yake cikin kananan kaya, logoless Riga Indigo Long Sleeve,Da Dogon Wando Jeans Gashin kanshi yasha Gyara Sai Qyalli yake da daukan ido.

Ramlah ta Dan kalle shi ta kanne mashi ido daya"Kayi kyau"

Yaja kumatunta "Na kai ki?,Ai Kinfi ni kyau" ya fada yana kamo hannunta,suka nufi Dinning  Area

Ramlah ta Zuba mishi Orange juice Cikin Transparent Glass Cup, Takai bakinshi,Ya wani wangale baki kaman Mai shirin Hadiye Gida.

    Aikam Ganin Ya wangale baki yasa ta Zuba Mishi dayawa,

  Wani irin Zabura yayi ya Buge kofin ya fadi kasa,Ya Riqe kirjinshi yana Tari,Idanun shi sun chanza launi zuwa kalar jaa, Gabadaya jiyake kaman ba bakinsa ba,Lokaci Guda ya fita hayyaci sa ga ciwon kirjin da ya dirar masa at once, Da zarar ya bude baki zaiyi magana sai wani Azababben zafi ya Dirar mishi A baki, Da hannu yayi ma Ramlah Nuni da Ta zubo mishi ruwan tea ya kora.
   Babu musu ta debo ta zuba a mug, ta miqa mishi tama jera mishi Sannu (cus batasan dalilin Chanzawansa alokaci daya ba haka!).

Yana kaiwa baki ya saki wani irin kara kaman zakiyi kuka, murya na Sukaji Radau ina cewa "............



Masoyan book Dinnan harkullum bazan Gajiya bawurin miqa muku godiyana a gareku, Thank you so much

I love u wujiga² Irin totally😍😍😍

Kumin comments ko naje Strike🤤

Manage pls😍



Fahnaan🖋️

23rd August💃💃

HAWAN JININA (Uwarmijina)Where stories live. Discover now