chapter 6

12 1 0
                                    

.🌀🌀🌀🌀🌀🌀
*UWAR MIJINAH*
~{Hawan jininah💔}~      
🌀🌀🌀🌀🌀🌀
                NA
   *🤍Fahnaan🤍*

_MARUBUCIYAR: MA'ESHERH(ANNOBA)_
       
©🎆
*AL'UMMA WRITER'S ASSO...* ✍🏻
  _A• W• A•_
_{Al'umma writers, Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane gsky al'umma sai dan Al'umma, Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}._
 
بسم الله الرحمن الرحيم...

      *_Chapter 6_*

Daga chan 6angaren Abie yace "Sorry Princess din Abie, kinsan yanayin Network din Garin,Ko na kira Abanza"

Nace "Ba wani nan ,Ka manta damu ne kawae,ni ina Hajiya ta?, Nayi kewar ta"

Abie yace "Jiya Akayi mata Aikin kafa ,tana bacci in ta tashi zan hada ki da ita inshaAllah"

Nadan Shagwa6e fuska nace"Abie na yaushe zaku dawo I Really miss u"

"InshaAllah zuwa next tomorrow zamu dawo ina Auta naa?"

Da kalle Hafsah da ta wani zuba min idanu na kauda zancen da cewa

"Abie Kayi Wa Umma fada Tana Shiga haqqin Su Yaa Arry da yawa.........nan na kwashe masa duk Yanda akayi tsakanin Ranar da Aka kawo Ramlah har zuwa yau dinnan na kara da cewa " in da so Samu ne ma kayi mata fada ta bar mana Gidan mu huta da takuran ta, ta takura mana ta takura Wa Yar mutane" jin yayi Shuru bai ce komai ba yasa na cire wayar daga kunne na naga bai katse ba

nace "Abie kana jina ?"

Yace "Ina jinki princess cigaba"

Nace"Ai na gama"

Yace "Toh ya kike so ayi ne?"

Nace" kawai kace ta koma Gida mu kuma ka Aurar damu mu bar musu Gidan Su ko hafsah? "Na fada tsakani na da Allah ina me duban Hafsah

Abie yayi Yar dariya irin tasu ta manya yace " Yaro kenan, yanzu innace zan Aurar daku kuna da Wanda kuke so ne?"

Nace"Aa kai zaka za6an mana yanda ka za6a Wa yaa Arry"

Yace"Munayferh,You're too young, You're just 17yrs fah"
Turo baki cikin shagwa6a
Nace "Nidai wlh Amin Aure ko In Gudu" ban tsaya jin Abinda zaice ba na katse wayar.

   Hafsah ta kalleni cikin dariya Tace"ke yanzu ko Aure Akayi miki ba zama zakiyi ba, Dan na tabbata kina sati zaa koro ki"

"Muguwa,Aniyyarki ya biki" na kalle takeaway din dake gabanta nace nifa bazanci Awara ba, Na tura mata Robar awara na jawo nata dake kumshe da beef Shawarma , ita kam A dadinta,  nan ta fara tsakurar awara ni kuma na hambadi Shawarman ta🌮

       Inajin wayana na ruri naqi dagawa, Dan duk a zato na Abie ne, Sai da nga alamun kaman bazaa daina kira ba na dauka ina Saka loman Shawarma cikin bakina Muryan kanina Abul-Rahman naji cikin Kuka yana cewa"Aunty Please kizo Su Yaa Umar da Anty Zainab sun dau key din Dakin Dad😭" iya Abinda naji kenan wayar ta katse.

  Tashin Hankali!, ai bansan lokacin da na hankade Robar gabana ba na Mike ina haki, Da mamaki na Sai naga Hafsah ta 6ingire tana bacci ban tsaya nazari akan Dalilin baccinta lokaci guda ba na gyara mata kwanciya nja mata bargo na dau Robar awara nakai kitchen Nasa shi cikin oven.

Ina dawowa na bude drawer na dau makullin mota na nafice, har nayi nisa da driving na tuna banida isasshen Fuel din da zai kaini Kaduna . kai tsaye motor park dinda ke sabonGari na nufa na parka na dau taxi ya dawo dani .
  Ina Shiga cikin Saa babu kowa A falor , key din motar yaa Arry nagani a saman Center Table, da Sauri n dauka nayi waje

   Inda driver ya parka motar dazun na nufa, na hau na tada Gateman ya wangale min Gate, ina isa Daidai gate din na dakata tareda zuge glass din Motar na kalle Malam Ali mai gadi nace"Saura in an tambayeka ka koro Masu bayani" ban tsaya jin Abinda yake cewa ba nayi gaba Abina.

  Daga Zaria zuwa kd tafiyar 45-50mins ne a motar gida ,1hr  a motar haya, Amma Dan tsananin Gudun da nake Sheqawa 20mins na isa Kaduna (kunsan gudun Firari ba na wasa baneh)

    Ina isa bai gadi ya Fara kirari "AngoAngo Ango kasha kamshi" duk daukan shi yaya ne fah.

  Sai da nayi parking na Zuge Glass din motar, yana tozali da Fuskata, Yan hanjin cikinShi suka kada ji kake kululululu.....😆

Na galla Masa wani Mugun hararar da yasashi ja da baya batare da ya shirya ba,

Kai tsaye Part din Su inna Rabi(kishiyar Umma) na nufa , a falo na tarar da Abdul Raku6e gefe guda yana kuka kaman maraya... Allah sarki Dan kani na, Yana gani na ya Rugo da gudu ya rungumeni "Anty pls karki bari Su bude Dakin please Aunty"

Ganin kaman ba cikin hayyacinshi yake ba yasa na zaunar dashi da nufi Fridge na Dauko mishi ruwan Sanyi Dan ya kora ko yaji dan Sanyi a ransa, Amma sai yaqi amsa sai nuna min Part din Dad dina yake.

    Riqo hannunshi nayi muka nufi part din, Ga mamaki na Sai ganin Su nayi tsaye a bakin kofa Suna kiciniyan bude kofar.
   Ta baya na jawo Wuyar rigar yaa Umar Wanda ke faman zura key a mabudin kofar.
     Gaba dayansu Waro ido Sukayi a razane Dan ko a mafarki basuyi zaton ganina a wannan lokacin ba.

Cikin zafin nama na fizge makullin A hannunshi, Aikam kaman raba ruhinsa nayi da gangarjikinsa, haka ya wani zabura yana Zazzare min ido kaman maye sabon kamu(Wayasani ma ko sabon mayen ne?😏)
Na kalle Abdool Cikin Murya mai Nuna tsananin 6acin rai nace " Twin cikin Su, waya ta6a ka?"
Da hannu ya Nuna Suwaiba da Zainab
Suwaiba wacce itace kanmu daya a cikin Su tace "Eh an dake shi din me zakiyi?,Rama mishi zakiyi ne ko me?" Bata ida Rufe baki ba taji Saukar tafi a kuncinta, nan na shiga lafkarta harsaida na tabbata tayi laushi.
   Juyawan da zanyi naga wayam duk sun Ware, Nima bin bayansu nayi Dan na tabbata suna Dakin uwar su
   Aikam anan na taddasu Sunyi tsuru-tsuru suna Gayama innar tasu Zuwana.

Kulle kofar nayi da makullin dake jikin kofar, na jefar da makullin ta window...

    Salati inna rabi ta saki "Innalillahi munaifa, wannan wane irin Sakarci ne?, kin kulle mu kin jefar da makulli ta taga ta ina zamu fita?

    Ban tanka ta ba na Jawo wuyan Rigar Zainab  na gwarata da bango nace " Uban waya Baku izinin daukan makullin part din mu?,Me kuka Ajiye anan ?,Eh tambayanki nake me kuka ajiye anan?? Shine Dan Abdool ya hanaku shiga harda dukan Shiko?,Wannan wane irin Rashin imani ne?"  hawaye ya gangaro bisa kunci na Dan tausayin yanda naga Qanina cikin kwanakin da basu wuce 3ba duk ya rame ya tsukare kaman bashi ba

Muryar inna naji cikin hayaniya tana cewa "Dan mun dakeshi bamu isa dashi bane?, faruq oya jawomin Dan banza nayi maganin shi yanzunnan

Sakin wuyan Rigar Zainab nayi na hankadeta tayi gefe na kamo hannun Abdool nazo gaban inna na ce  " Ba sai an kawo miki shiba! Gashi na kawo mk shi da kaina!, duk Wanda ya isa ya ta6ashi na gani"

Ai ban gama Rufe baki ba naji tassss An tsinka mishi mari ta baya,  muryar yaa Umar naji yana cewa "An dakeshi din ko Zaki zama mishi ne?"

Kallon inna nayi sai faman murmushi take yi, tausayinta ya kamani, Da na tuna irin hukuncin da zanyi mata.
   Nan da nan na fara jaa da baya hannu na riqe da kai, na wangale baki na saki ihu..........





See you tomorrow💃

Fahnaan🖋️

18th August

HAWAN JININA (Uwarmijina)Where stories live. Discover now