28

17 1 0
                                    

🌀🌀🌀🌀🌀🌀
     *HAWAN JININA*
     ~{UWAR MIJINA}~      
🌀🌀🌀🌀🌀🌀
                NA
   *🤍Fahnaan🤍*

_MARUBUCIYAR: MA'ESHERH(ANNOBA)_
       
©🎆
*AL'UMMA WRITER'S ASSO...* ✍🏻
  _A• W• A•_
_{Al'umma writers, Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane gsky al'umma sai dan Al'umma, Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}._
 
بسم الله الرحمن الرحيم...

    *_Chapter 28_*

Na Rufo kofar ina dariya Sannan na fara Dube-Duben makulli

Jinayi ya Banko kofar ya Shigo,Fuskar nan dauke da murmushin mugunta, Wanda ya saba yimn.

Chak na tsayarda dariyan da nakeyi,Tsoro ya kamani,Jikina ya fara Rawa baki na Rawa nace"Ki...pya, Chama"(So....rry Pl...ease)

"Sorry for what?,Nifa zuwa nayi na tambayi kayan" ya fada yana dago Fuskata dake Sunkuye,Alamar na kalleshi,Ni kuwa Tun jiya da Abin ya faru na kasa kallon Cikin Qwayar idonsa ,Saboda ko na kwatanta hakan Sai naji Gabana na fadi.

Gabana ya qara faduwa cikin Rashin Sanin Madafa na fara Hawaye, Sakin Fuskata yayi Sannan yace" kukan Fa?"

"Main bhookha hoon"(Yunwa nake ji). na fada ina matse ido

Da yatsa ya mn nuni DA Kitchen sannan yace"jao aur khaana banao"(kije kiyi Girki)

"Ai duk kayan Abincin Sun lallace"

Maganar ta bashi dariya, kayan da kwata² basu wuce Sati Uku da Siyowa ba yace"Kodai Girkin ne baki iya ba?, taya za'ayi foodstuffs dinda basu wuce 3wks ba su lallace"

Na kwa6e fuska nace"Wallahi Dagaske nake Duk sun lallace harda Qasa-qasa a kansu ma"

Dariya ya sakeyi kafin yace "Kin yarda muje a duba idan Basu lallace ba ,Zaki bi duk Abinda na Umurce ki kiyi koda Ranki baya so,Amma idan Sun lallace da Gaske Na yarda ki juyani Kaman bawanki"

Tsoro ya kamani ,Tunawa nayi da Yanda naga Kayan Abincin ~(Yasin sun lallace~) Raina ya qara bani Tabbacin hakan.

Gyada kai nayi Alamar "Eh" a raina ina Kitsa yanda zan juya yaaAary idan hakan ya kasance Gaskiya ne,Saina maidashi Abin tausayi😆.

Ya tasani Gaba muka nufi kitchen, Kayan suna nan yanda suke babu Wanda ya lallace a cikinsu,Sunyi kura ne kawai.

Ya kakka6e Kurar da hannunshi Sannan kalleni yana Murmushin mugunta yace"Finally I'm the winner "

Narai-Narai nayi da idanu Hawaye na shirin Zuba nace"Nifa ban dau Maka al'qawari ba"

"Tun baki San Kudiri na ba Zaki fara min kuka,Aap kya Ummeed kar Rahe hain? ~what are you expecting?~ ,Ni yau Girkin Amarya nake son ci" ya fada yana Shafa mn Dattin Kurar hannunsa bisa Fuskata.

Sunkayar da kai nayi Hawayen da nake dannewa suka zubo Saman kunci na ,Tabbas da na San manufar sa kenan Da banyi Saurin Amincewa ba, jiki a sanyaye murya a sarqaqe nace "Bazan iya Girki ba,hannu na ya Gurde dazun"Murmushi kawai yayi ya fice zuwa Store ya debo dankalin turawa da Kwai ya Zube a gaba na Sannan yace na idan hannun nawa ya Dawo Daidai na Gyara Kitchen dn Na hada masa break yana tare da baqo ,ya fice Abinsa,

Yana Fira na bi bayan sa da Harara na kwashe potatoes na Wanke, na fara Tunanin Next abinyi.

Wuqa na Dauko na fere dankalin,Wanda gaba daya Rabin nayi asarar su ne,Sannan na dauraye FryingPan na zuba mangyada Na Dauko lighter zan kunna Gas,Toh anan fa akeyin ta Dan nida Hafsah Tsoron Gas mukeyi,Fitowa nayi na nufi falo Naga bayanan

HAWAN JININA (Uwarmijina)Where stories live. Discover now