26

18 1 0
                                    

🌀🌀🌀🌀🌀🌀
     *HAWAN JININA*
     ~{UWAR MIJINA}~      
🌀🌀🌀🌀🌀🌀
                NA
   *🤍Fahnaan🤍*

_MARUBUCIYAR: MA'ESHERH(ANNOBA)_
       
©🎆
*AL'UMMA WRITER'S ASSO...* ✍🏻
  _A• W• A•_
_{Al'umma writers, Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane gsky al'umma sai dan Al'umma, Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}._
 
بسم الله الرحمن الرحيم...

    *_Chapter 26_*

*narasa  bakin da zan godewa masoya wannan littafin sai dai ince Allahu yabar qauna yaqara bani kwarin gwiwar faranta muku ko yaushe 😘*

Hawwa baba

Hawwa'u Adam

Hawwa'u Kwangila

Hawwa ms

Jeedda zubayr

Da dukkan masoyan littafin nan Masu suna Hawwa wannan page din naku neh😘




      *LAOS*

Da suka Gudu fado Dakin suna kyakyatawa.

Yarane Sosai Bazasu Wuce Yan Shekaru Biyu bah,Mace da Namiji Suna matuqar kama da juna Sosai, ko ban fada ba Ya kamata Ace me karatu ya Gane y'an Biyu ne😉.

Macen Na Riqe da Tablets Guda Biyu namijin na Binta yana dariya yana ta bashi AbinShi Amma ita Sai wahalar dashi take,Sai tayi kaman zata bashi ya zo Gab da ita take Zamewa .

Suna Haka wata matashiyar mace ta Fito daga daki tana murza ido Alamar daga bacci ta tashi,

Da gudu Namijin dake bin macen ya Ruga ya Riqo hannun ta ya fara kukan Shagwa6a"Ammi tinka Amiya ko!,Ta Tauka mn new tablet tinda  Uncle hoody ya bamu " ya fada yana Share kwalla.

Wacce Suka kira da Ammi tayi murmushi Sannan ta Shafa kanshi tace "Shine kake kuka?,Kaifa Namiji ne Can't you be a man?, kaifa Soldier ne!, Oya share hawayenka kaje ka Kar6o"

Yaron ya share hawaye ya wani kumburo baki a dole an ce mai soldier, ya nufo inda Macen ke tsaye,Saida taga yazo Gab da ita ta arce ya kuma fashewa da kuka.

Daidai lokacin da Wani Mutum ya Shigo da Sallamarsa, Macen tayi Wuri da Tablets din kan kujera ta Ruga da gudu ta Rungumoshi tana fadin "Daddy Oyoyo, Oyoyo daddy, ka ciyo mn chaklat kor?".

Shima Ameer ya Rugo da gudu ya Rungume shi yana fadin"Daddy Amiya bata iya kayatu ba, Kuma ai kashe ba'aka Siyawa DumpBaby ba"

Ameerah ta 6ata fuska tace"Daddy walla'i Amiy ne bai iya kayatu ba kuma Uncle Hoody yashe jaijo Anjima, ijan yajo ka taibayeshi"

Ammie dai tana zaune sai faman murmushi takeyi ,Yaranta na matuqar Burgeta, A koda yaushe idan Ameerah ta 6aro Zance Sai ka Rantse wata babbace Sa6anin Ameer da Akoda yake kaman bawanta ,Sai yanda tayi dashi koda yake Yarinyar kenan......😉

Daddy ya Ciro Chocolate daga Aljihu ya miqa msu yana cewa"wanene Uncle Hoody kuma?"

Ameerah ta 6are chocolate ta saka a baki sannan tace"wani sabon Tahfeez uncle ne, bakaji Kiya'an shi ba,So sweat!"

Daddy yayi murmushi,Sannan yaja kumatunta yace ”Da bakinki anan kaman so Sweat"

Ya Matsa Inda Ammi ke zaune tana kallonsu sai faman murmushi takeyi yace"Ammin Yara ya dai yau ba magana ne?"

Tace"Eh Bakina da Goro "ta fada tana Harararshi ta Gefen ido.

Ya bude baki da niyyan Yin magana yaji an buga Kararrawan kofar.

HAWAN JININA (Uwarmijina)Where stories live. Discover now