27

13 2 0
                                    

🌀🌀🌀🌀🌀🌀
     *HAWAN JININA*
     ~{UWAR MIJINA}~      
🌀🌀🌀🌀🌀🌀
                NA
   *🤍Fahnaan🤍*

_MARUBUCIYAR: MA'ESHERH(ANNOBA)_
       
©🎆
*AL'UMMA WRITER'S ASSO...* ✍🏻
  _A• W• A•_
_{Al'umma writers, Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane gsky al'umma sai dan Al'umma, Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}._
 
بسم الله الرحمن الرحيم...

    *_Chapter 27_*

_*Masha Allahu Hakika jiya naga Ruwan masoya ta koina naji dadi sosai da sosai Ku zage kara himma wajen karatu da comment nikuma zan zaqe wajen Faranta muku Akoda yaushe Allah ya bar Qauna ta har Abada💖*

Godiya ta musamman Ga Alisha Wacce ta Samu nasarar Lashe Tambayan Jiya, ta fadi Sunan Baqo wato SALEEM tsohon saurayin Ramlah💖💖

______________________

Ramlah Jin muryan Aaryaan yasa ta fito da fara'ar ta, saidai Tana isowa falo taja ta tsaya Chak Dan Gaba daya ta manta Umma na Gidan.

Kallon kallo aka shigayi tsakanin Ramlah da Aaryaan.

"Keh,Me Nake Gani haka?" Umma ta fada cikin Tsawa.

Ramlah tayi hanzarin janye Idanta daga Kallonshi ta maida kallonta Ga Umma wacce take Binta da Kallon tsana,Da hanzari ta Kawar da kai Gefe jiki na Rawa ta koma daki,

Aaryaan ya Sauke Ajiyan Zuciya ya karasa inda Umma ke zaune ya zauna Qasa Gefen kafarta,Sannan ya gaidata,Ta amsa mai ciki-Ciki,Ya Kwantar da kansa Bisa Cinyarta Cikin Shagwa6a yake fadin"Haba Umma,Dama kinzo shine ko ki fada mana zakizo?"

Umma ta Ture kansa da ya aza bisa Cinyarta tace"Tunda MaraAsalin chan ta Mallake mn kai, ta saka Gujeni yanzu ai  bana Gabanka,Aaryaan Wai yaushe ka zama haka ne?, har ni zan kira ka kaqi daga min waya Saboda Kar na Rabaka da Rabin Ranka kor, Tho ni da kake Gudu na Dawo Gidan nan da zama Har sai Alhaji ya dawo ,In ka ga dama ka dauketa Ku bar Qasar ne ni kuma bazan Gajiyaba Duk inda kuka Je ,Ku sa a ranku kaman ina Gurin ne Dan Babu makawa sai nazo,Kuma wallahi Tallahi idan ina Gidan nan ko kallon Arziki kayi Wa Yarinyar nan Saina Tsine maka!"

Aaryaan ya dago da Sauri yana duban Umma baki sake, Yana mamakin Rashin Imani irin na Umma,Ya tabbata da Hafsah Ce tayi Aure akae mata haka Sai inda Qarfinta ya qare,tho meyasa zatayiwa Yar wata Akan dalilin da Baitakakarayakaryaba?,Nan danan Tausayin Ramlah ya kamashi Haqiqah tana Haqurin zama da ita maruqah, Tunawa yayi da Munayferh (Amaryarsa😉),ya tabbata Bazata ta6a yarda da Cin mutumci irin na Umma ba,Saidai ayita ta qare..

Muryan Umma yaji ta cigaba da cewa"Ka Kureni da idanu, ko kana tantama ne?,....kai!,Ka kasa kunnenka kajini dakyau idan naji  labari koda wasa ka Sake Shiga koda dakinta ne tho ban yafe maka ba...."

Aaryaan bazai iya Jure jin irin kalaman dake Fita daga bakin mahaifiyarsa ba, Shiyasa ya miqe Zubur ya nufi hanyar Fita ba tareda yace mata qala ba.

"Au fita ma zakayi, Dan na isarmaka da Saqon mutuwa ko?" Ta fada cikin karaji,Juyowa yayi ya tako har inda Take idanunnan Sun kada Sunyi Jaa Saboda 6acin rai ya bude baki zaiyi magana, Sai kuma ya fasa ya Dafe kansa dake Sara mshi.

Daidai lokacin Hafsah ta Sauko cikin Shirin Zuwa makaranta, Ganin Umma na kumburewa Ga Kuma Aaryan Riqeda kai yasa ta Gane Umma ta kuma halinta kenan, Da gudu ta karasa inda Aaryaan yake Riqeda kai jikinsa na karkarwa yana tangal² ta Riqoshi zata Zaunar dashi Gudun karya fadi, tamanta idan yana Fushi Baa tunkarar shi,Ta manta idan Yana Baya Ji baya Gani ,

Tana Riqeshi taji Saukar Mari, Yasa kafa yayi ball da ita yana haki ,Tayi Gefe tana Ihu(Daga Taimako?🙄)

Sannan ya tako har inda Umma take Ayau da ba mahaifiyarsa bane a Gabanshi Yau Sai inda Karfinsa ya qare

HAWAN JININA (Uwarmijina)Where stories live. Discover now