chapter 15

9 1 0
                                    

🌀🌀🌀🌀🌀🌀
     *HAWAN JININA*
     ~{UWAR MIJINA}~      
🌀🌀🌀🌀🌀🌀
                NA
   *🤍Fahnaan🤍*

_MARUBUCIYAR: MA'ESHERH(ANNOBA)_
       
©🎆
*AL'UMMA WRITER'S ASSO...* ✍🏻
  _A• W• A•_
_{Al'umma writers, Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane gsky al'umma sai dan Al'umma, Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}._
 
بسم الله الرحمن الرحيم...

    *_Chapter 15 _*
Ya Nuna ni da yatsa bakinshi har Rawa yakeyi, Sai ya Sauke hannunshi ya kasa Cewa komai, haka ya fice Rai 6ace.

Nikuwa kara Rushewa da kuka nayi
"Please Deedeema Stop Comparing me with Him,Wlh Mai nafrat karta,Aapp bhar" (Dan Allah kakus ki daina hada ni dashi, Wlh na tsaneshi mugune)

Murmushi kakus tayi tana jawoni jikin ta

Cikin Sigar Rarrashi ta fara magana"Badi ladki mafi maf Chama"(yi haquri³ jikalle) Sai ta ka kalli Ramlah, Yanda taga mood dinta ne yasa ta Sauya yare cikin Rarrashi tana bubbuga bayana"Haba Uwata  ,Daga Wasa?,Ai babu mai hadaki Aure da Aaryaan, Aaryaan din banza Aaryaan din hofi?,Ai bai kai matsayin da zai mallaki tsaleliyar Budurwa irin ki,Ai ke din ba Ajinshi bane, kinfi karfinshi duniya da lahira, Inba Ramlah ba ai babu mai iya Auren shi, da karamin kanshi anan Tun na haihuwa"ta karasa tana kallon Ramlah, Ramlah tayi murmushi tana Ajiye jug din kunun da ta kawo

Kara shigewa jikinta nayi ina kuka mai hadeda da dariya "Wayyo Kakus dina Allah ya bar minke, aini soja nake Son na Aura,Wanda zai Rama mn dukan da Yaa Aarry ya mn"

Gaba daya Dariya sukayi ,Hafsah ta matso ta dungure mn kai "kuma inshaallahu babu mai Auren ki Inba yaa Aary ba", kakus ta Jefeta da pillow ta kauce Tana dariya.

Ledar da Aaryaan   kawo mn na jawo gabana ina yatsine fuska, Red Apples da Strawberries ne Cike a Ledar , Gashi Ni banason Strawberry Abdool ne meso Sai A yanzu na tuna da Wani Abdool kallon Hafsah nayi ina tambayanta "Ina Abdool ne?"
"Na ganshi da ball dazu ya fita" ta bani Amsa

Zumbur na mike Ina kallon Agogo "karfe goma yake fita ball ya dawo shabiyu, Amma yanzu to three, Inaga babu lafiya,Bari inje in duba  shi" Babu Wanda ya tanka mn da kallo suke bina har na Fice

Kai tsaye Falon Umma na nufa na duba koina babu kowa Sannan na fito na nufi part din InnaRabi Tun kan na iso part din na fara jiyo ihun Abdool yana Tashi, da gudu na karasa a falo na Ga duk sun zagayeshi Suna jibgarsa harda Hegiyar Uwar tasu.
   Saida na Saita natsuwa na sannan na shiga Tafi kaman Wata zararriya.
    Jin Ana tafi a bayan su yasa duk suka juyo Suna Kallona
   Umar ya kwashe da Dariya kaman wani mahaukaci Yana Nuna ni "Nasan zakizo, tabbas zakizo Gashi kinzo ,Suwaiba Jeki kulle mana kofa ki bani makulli" Babu musu Suwaiba ta kulle kofa ta bashi makullin

   Suwaiba tace"Wato ke har kin isa ki mana karyan Aljanu ki Sanbade mu, Sannan ki dauka kin daki banza kenan?, Inaa yau mai kwatan Sai Allah. Duk Suka kwashe da Dariya harda Uwar tasu😆

Wani Shaka da Umar ya ma wuya na ,ya hada ni da bango Ya falla mn mari "Yau idan mun fara Mazgar ki babu mai kwatarki harta Wannan tsohon me daure mki Kugu kina Abinda ya Kikaga dama, kin dauka tsoronki Akeji ne?, ko Dan kinga mun zuba miki ido, kin dake mu Wawaye marasa Hankali Wa inda bamu San me mukeyi ba ko" ya kara tunturewa da dariya yana kara Yarfa min tafi..

 
  kirjin Munayferh fa ya shiga lugude inda takeji kamar ta arta bata san tanadin da sukai mata ba tasan ma makaman yakin su sunfi nata dan haka ta yunkura da niyyar Artawa, Amma Riqon da Umar yayi mata bana wasa

Hannu na sa akan nasa ina kokarin cire nashi daga wuyan Riga na ya riqe hannun da karfi riqo bana wasa ba hakan yasani sakin qara don jinda nayi yana barazanar ballan wurgi yayi da ni gefen kujera inda saida kaina ya dan bugu kafin ya dauke ni da wani wawan marin dayasa ni ganin star wata qarar na saki yasa yayi saurin aza hannunshi a saman bakin shi alamar nayi mishi shuru

kasa shirun nayyi inda nan ya shiga mazgata su Zainab da inna Rabi na gefe suna dariyar mugunta saida ya gama canzamin hallitar fata abinka da fara fara duk jikin sai yayi ja yayi rudu rudu kafin ya kyaleni ya zauna yana maida numfashi

cikin daurewar fuska ya kalleni idona kyar babu Alamun Hawaye na kureshi da idanu Sai maida Numfashi nake
Yace"Dan ubanki,wannan dukan da kikasha na Raina mana hankalin da kikayi ne Saura Na Mazgar da mukasha A hannunki"(ko kunya, Ansha mazga a hannun yarinya😆)

Shuru nayi ina kallonshii da alama Munayferh akwai zuciya

Suwaiba ce ta taso cikin daga murya "dan uwarki ba magana akeyi miki ba ta karasa maganar cikin daka tsawa

Na tattaro kuzari na cikin karfin hali na Sheke da Dariya

Gaba daya Sakin baki sukayi Suna Kallona Alamomin Tsoro Sun baiyyana a Fuskokinsu dama ni haka nakeso

Na mike da kyar ina kallon Abdool Wanda jini ke zuba daga Doshin sa

Na kara tuntsurewa da dariya , na ware hannayena Cikin Murya irin Gardayen mazan nan na soma magana"Hahaha, Ku cigaba da Mazgar, Ya naga kun tsaya?,Gata Ku mazgeta har Sai ta daina Numfashi, ya na ga kunyi cirko²,Ku Daka mana!"

Na karasa magana cikin Daka tsawa babu mai magana cikinsu Sai makyarkyata sukeyi Ganin yanda muryata ta Sauya at once

Cikin zafin nama na Rarumo kwalar Rigar Umar na hadashi da Show Glass nan da nan ya Fashe, kanshi ya fara Fitar da jini , nan ya zube yana kurma ihu kamar bashi ya gama Ciccika baki yanzu ba

Ai tuni Zee da Suwaiba suka nemi bayan kujera suna Neman wurin 6uya ,takowa nayi har bayan Cushion dinda suka boye na chakumo wuyar Rigunan su na hada su da bangon dakin,Suma banda ihu babu Abinda Sukeyi Ganin babu jini a fuskokinsu

Yasa na jasu na kara Garesu da Show glass Wanda tuni ya wargaje
Jini ya fara Ambaliya a goshinsu, daman tunda naga sun Fitar da jini a goshin Qanina na rantse a zuciyata idan ban Fitar musu da jini ba bazan yafe Wa kaina ba

  Gabaki dayansu ihu sukeyi, InnaRabi kam Ra6ewa Tayi Chan Gefe tana zaro idanu, yau banida lokacin ta Shiyasa ko kallonta banyi ba, Abdool kam tunda Yaga na fara shaqo Umar ya shiga rama mn dariyar muguntar da suka mn

Kai tsaye Wurin TV na nufa na ciro Igiyar charger na Shiga Fyada Masu ta ko ina suna ihu, babu mai jinsu (kundai San irin kofar Gidan mu)
Cikin Fitar hayyaci nake Dukan su, duk inda na Samu a jikinsu Duka nake ,Gaba daya na koma tamkar mahaukaciyar gaske
Saida nayi Masu Lilis na Tabbatar babu mai iya kwakwwarar motsi,Duk Sunyi laushi Sai fidda Numfashi suke a wahalce, barin ma Umar Sa Sannan na juya Ga uwar su Nace tayi kneeling, Babu musu Sai gata tayi harda hands up😆Nace ta kama kunni tamana Up and down 'ya'yana sun Dade basuga Rawar Tsohuwa ba Jiki na Rawa ta kama kunne ta shiga up and down😆

Najuya ga su Umar waenda Gabaki daya Sun fita hayyacinsu har zanyi magana Sai naga ko nayi ba jina zasuyi ba Saboda yanda Suka jigatu matuqa

Kallona na maida kan Abdool naga yanda Goshinshi ke Fidda jini na Rintse ido Raina na kuna, Bansan lokacin da na dau Glass Wanda ya fashe ba...


Wait what......😳

Kardai Ace Yarinyar nan ta Sami ta6in hankali!




Just Comment and off Ur data OK?😆

Nayi Gabas🚶🏻‍♀️

Wattpad @Fahnaan

27th August

HAWAN JININA (Uwarmijina)Where stories live. Discover now