53

60 2 0
                                    

Koda Mama Zenabu suka je suka ga Hafsa ne ta rasu har an mata wanka ma, se ta zauna tayi shiru ta bude fuskan ta tana ta jero mata addu'a, hawaye se zuba yake daga fuskan ta
"Na yafe Miki Hafsa, na yafe Miki duniya da lahira, Allah ya sada ki da mala'ikun rahama Ameen.
Tana karshewa ta fashe da kuka me tsuma rai, yaushe ta rasa mijin ta, wata biyar ne fa a tsakanin su, innalillahi.
Suna zaune can su Sulaiman suka shigo shida su yaya Lawan, makara suka kawo aka saka ta a ciki, bayan an rufe fuskar nata, wucewa dakin shakatawar Yarima akayi da ita, mutane suka dinga suma, Jamila kam tunda taga fuskar Hafsa a likkafani ta suma.
Can akazo aka kama makaran aka fita da ita waje, Yarima na hango yana tafiya kamar wani mara hankali, shidai gashi nan dai za'a ce amma baya cikin hayyacin sa.
Daman akwai makabarta a cikin masarautar dan haka can aka nufa.
Yana tsaye yana ganin sanda aka zura ta a cikin kabarin nata da daidai ita aka haƙa shi, se a lokacin ya yadda da komai, sannan ya kasa motsi kwata kwata, yana gani aka zuba tukwane aka shafe da kasa kana aka tsaya aka dinga jero mata addu'o'i.
Shidai kawai mamaki yake, wai yau Hafsa, Hafsan shi ce kwance a cikin ramin nan har an zuba mata ƙasa bisa kanta?
Allah Sarki, da kam be yadda ba, amma yanzu ya yadda
  Hafsa ta rasu,
      Ya karɓi hakan
             Sede baya tunanin rayuwa shima.
Bayan kamar minti arba'in aka gama addu'a kowa ya fara watsewa, aka barsa da su Sulaiman da su yaya lawan, zama yayi ya dora kan sa akan kabarin ya fara hawaye yana zubo mata addu'o'i, yafi awa yana abu guda, gashi mangariba har ta iso, ganin baze tashi bane Suleiman ya riqo hannun sa Lawan ya riqo dayan, suka kama fita dashi daga makabartar dan su Mai Martaba tunda aka gama addu'ar farko suka yi gaba.

Suna shiga cikin masarauta suka ji ana shirin shiga sallan mangariba, alola suka yi suka je suka bi jam'i
Bayan da aka gama Sulaiman ya wuce da Yarima sashen sa dan sashen sa da jama'a, sannan Bilkisu ta koma sashen sarauniya babba, tare da jariran da Hafsa ta haifa, a can Bilkisu tace a bata su zata shayar da su tunda itama shayarwa take, sarauniya babba ce ta hana tace mata baza ta iya shayar da har yara uku ba, tayi tayi sarauniya ta bata ita kuma ta hana, se ta hakura a karshe kawai tabar maganar.

__________________

Bayan bakwai da kowa ya watse, Mai Martaba ya kira Mama Zenabu, yace mata ya rada wa yaran da Hafsa ta haifa suna Jafar da Aminatoú wato sunan kanın sa waziri da kuma mahaifiyar sa sarauniya babba, Waziri daɗi kamar ya kashe shi, nan kuma ya mata explaining din situation din da ake ciki, akan baze yiwu a bata yaran ta tafi dasu ba saboda hatsarin da rayuwar su ze iya shiga duba da sune yaran Yarima me jiran gado, sede in zata dawo zama a Masarauta ta kula dasu.
Koda jin haka se Mama ta ɗan yi jim, ita dai tana so a bata su, toh amma ina zata kaisu? İta daman tun kafin Hafsa ta rasu take so ta koma Borno, toh yanzun ma hakan take, baze yiwu ta kai yaran nan gida daya dasu Kulu ba, sannan Bornon ma bata san taje ta ɗora musu dawainiya, sannan ai baze yiwu ta dauki yara har biyu da Jamila ta uku suje gidan auren yar uwar ta su zaune musu ba, duk da tasan bata da matsala da hakan sede be kamata ba. Can dai ta nitsa kana ta kalli me martaba tare da sunkuyar da kanta ƙasa tace masa
"Allah ya baka nasara gobe gobe daman nake san barin ƙasar Bauchi zan koma ƙasa ta ta haihuwa Borno, idan naje zanyi shawara da yar uwata da kuma mijin ta, duk yadda muka yanke za'a ji daga gare mu, daga nan zuwa da shekara ɗaya İnshallah".
Koda jin haka sai Mai Martaba ya aminta da abinda tace masa sannan ya yaba da hankalin ta kana yace toh Shikenan bari yasa a aika gidan su a kwaso mata kayanta in yaso gobe se ya shirya mata tafiyar Tata, tunda dai surikin nata da Yakamata ya mata hakan har yanzu baya a cikin hayyacin sa, shidai kawai rayuwa yake yi hakanan.

Ai kuwa da sassafe Mama Zenabu da Jamila suka je suka yiwa sarauniya babba da Fulani sallama, tana kallon jikannun ta dakyar ta sake su, Yarima ma yazo sunyi sallama shida Sulaiman sede ta lura kamar baya cikin hankalin sa, well, bata ga laifin sa ba, ita kanta da take uwarta karfin hali take yi.
Suna fitowa suka ga me martaba ya shirya musu goma ta arziki a cike da kekunan doki har uku, suna cikin na hudun, har bayi seda ya zaba musu wanda zasu raka su.
Nan da nan kuwa suka kama hanya sai Borno.

______________

1 YEAR LATER
MASARAUTAR KANEM BORNO

Suwaiba ne da Jamila a zaune a ɗakin shakatawar Mama Maryamu, hira suke ɗan taɓa wa kaɗan kaɗan dan dukkanin su ba masu san magana bane musamman Suwaiba, ita sam magana bata dame ta ba, wai fa zaman jiran su Mama Maryamu suke akan su fito su kama hanyan zuwa masarautar Bauchi, tun dazu suka ce musu suna fitowa amma sunji shiru, shine suka zauna suke hiran yaran Hafsa da zasu je su gani anjima In Sha Allah
Jamila ce tace
"Kin san wani abu Yaya Suwaiba? Wlh kina matukar kama da Yaya Hafsa, wlh dazu da asuba da nagan ki seda na tsorata, kawai dai yaya Hafsa ta fiki jiki kaɗan ne"
Jamila ta karashe idan ta da hawaye, tunda ta rasa Hafsa take cikin kunci amma samun Suwaiba da tayi ya matukar ɗebe mata kewar Hafsa, suna matuqar kama da junan su, harda itanma Dukkanin su ukun kamannin mamannin su suka dauko
Suwaiba ce tace
"Tunanin me kike Jamila"
Firgigit Jamila tayi kana ta fuskance Suwaiban, tana shirin bata amsa suka jiyo muryar yaya Abubakar yana ce musu suyi waje.
Keken doki ɗaya suka shiga suka zauna, can sega su Mama Zainabu sun fito, kap a cikin shekarun nan da suka yi tare mutane sun kasa dena kallon su in sunzo wucewa tare saboda tsananin kamar da suke, musamman ma yanzu da Mama Zenabu take rayuwar jindadi sulalla sun zauna mata, bata aikin fari bare ja, fatar ta ta saje da na Mama Maryamun.
Nufo keken dokin da su Jamila suke ciki suka yi, shiga suka yi daman gun zaman mutum takwas ne, Mai girma Galadima kuwa dayan keken dokin ya shiga shida Talban Borno da kuma Shettiman Borno, dayan keken dokin su Abubakar da su Ibrahim ne a ciki.
Tafiyar awanni goma sha biyu suka yi suka shigo masarautar Bauchi, wani numfashin baƙin ciki Jamila da Mama Zenabu suka shaqa, direct masarauta suka wuce, aka yi musu tarba me matuqar girmamawa, aka basu sashe sukutum suyi sharing, Galadima kuma sashen da aka ba su Talba yake.
Can da dare kamar karfe goma su Mama Zenabu suka shirya suje sashen sarauniya babba dan su miqa gaisuwa da kuma godiyan irin karamcin da aka musu, on the other hand tana so taga jikannun ta, taga yaya suke, tana so taga yanda suka ƙara girma, dan rayuwar da tayi a kasar Borno dakyar ta saba da rashin Hafsa, rashi na har abada, sede Jamila da Suwaiba suna ɗebe mata kewa musamman in taga suwaiba se taga kamar Hafsan ta ce, kamannin ta daya da Hafsan ta, halayyar su ne ya bambanta.
Koda suka shiga sashen sarauniya babba suka miqa gaisuwa, daga idon ta sarauniya babba tayi tana kallon Suwaiba, zuciyarta a take ta tsinke, maida hankalin ta kan su Mama Maryamu tayi, su Jamila kuwa jiyo sautin yara suka yi, nan da nan suka yi cikin dakin kuwa, hango yara ƙanana suka yi sai tafiya suke, suyi ɗaɗɗaya su fadi, haka dai suke tayi, shafa'atu dake kula dasu sai murmushi take, ganin suwaiban da tayi seda taja da baya, se daga baya ta fahimci ba Hafsan bace, gaida su tayi tayi waje, karasawa dakin Suwaiba tayi Jamila biye da ita, Areef da Areefa na ganin ta suka yi wajen ta suka ruqunqume ta, Jamila se dariya take musu, tana san ta dauki Areef yaqi zuwa gun ta, basu san da shigowan mutum ba, kawai ganin sa suka yi a kansu yasha mur fuskar nan kamar hadari, juyowan da zeyi yayi arba da ita, nan da nan ƙafar sa ta kama rawa

ALƘALAMİN FADREES 🖋️ 🖋️ Ƴar Mutan Yobe.

YARİMAN HAFSA Where stories live. Discover now